GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143P17
Shiru Hafsa tayi, ba tayi magana ba.
Khalil ya ce "Yau Allah ya haɗani da gamona ni Ibrahim, Baby magana nake Please answer me" yayi Maganar yana kuma marairaicewa.
Kwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka "Ni ka ƙyaleni ko in yi kuka Subhanallah, ba ƙaramin narka zuciyar Khalil Hafsa tayi ba, saboda a rayuwarsa yana son shagwaɓaɓɓiyar mace.
"Kar ki yi kuka Please" yayi Maganar yana kwaiwayonta.
"Ni ba haka nake magana ba"
"To ya kike yi?" Yayi Maganar yana kallon in da take.
"Kaga muyi sauri, kar Mama taga na daɗe ta hanani zuwa na gobe in Allah ya kaimu".
"Allah ya sa ta hanaki zuwa" ya faɗa yana kunna motar.
"Allah ya sa ta hanani zuwa ko?" Ta maimaita tana leƙa fuskarsa.
"Eh mana, gaba ɗaya ma ni kishi ne ya ke damuna, duk an gama ganinki, ga mayafinma ba wani babba ba"
Kallon kanta tayi da mayafin, ta sake jan mayafin tana rufe jikinta.
"Me zaki rufe bayan an gama ganin komai?"
"Me aka gani?".
"Kyakywar surarki mana, shiyasa duk naji haushi ai" haɗe rai tayi, tana sake gyara zamanta.
Haka Khalil ya yi ta janta da hira, ga mamakin Khalil ashe Hafsa na magana sosai, duk a hirar tasu ma, idan ba ta ga dama ba, shiru take taƙi tanka masa, amma yau ta ɗan sake da shi.
Har ƙofar gida ya kaita, sannan ya kalleta ya ce "Babyna, yau zan kwana cikin farinciki, duk da ban samu amsar tambayar da nayi miki ba, amma naji daɗin kulani da kika yi, Ina sonki Hafsa" Hafsa ta ɗaga ido ta kalli Khalil, haka nan taji tana tausayinsa, tabbas ya nuna mata so, ko ga wannan sintirin da yake yi a kanta."Sai da safe, ka samu kaje gida ka huta, Allah ya kiyaye hanya".
"Ameen my love" ya furta a hankali, ta buɗe motar ta fita ta nufi gida, har ta shige gida, yana tsaye yana kallonta, sannan ya ja mota ya bar wurin.
Sai ƙarfe goma Sa'annan Khalil ya isa gida, Mummy ce ta rage ba ta kwanta ba, taji ana knocking ƙofar Falon taje ta buɗe, mamaki ne ya cikata da ta ga Khalil.
"Kai, saukar yaushe?"."Yanzu Mummy".
"A wannan daren? Baka samu Flight ɗin yamma ba ne?".
Ya shiga cikin falon yana faɗin, a mota fa na dawo.
"What, mota kuma? Amma baka da hankali, da wani abu ya faru fa, yadda gari babu tsaro?".
"Ai ba abinda ya faru Mummy, baki bacci ba ashe?".
"Eh ban kwanta ba tukuna, bari in taso masu aikin can, su girka maka wani abun ka samu ka ci".
"No bana jin yunwa, a ƙoshe nake, na shigo ne ma kawai dan kusan na dawo, naga motar Daddy a waje yana gari ne?".
"Eh yana nan kusan sati guda kenan yana gari".
"Masha Allah, shikenan sai da safe"
"To Allah ya kaimu lafiya" ya fice daga falon ya nufi sashinsa.
Mama ta lura da yadda Hafsa ke murmushi lokaci lokaci, amma ba taji ta ce mata komai ba.
"Nace Khalil ya biki wurin bikin ne?".

ESTÁS LEYENDO
GABA DA GABANTA
De TodoGABA DA GABANTA (Aljani ya taka wuta)😂 don't miss it, akwai cakwakiya