GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P11
Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda take gabatar da sana'ar ta ta cikin nutsuwa, ba hayaniya ko ƙazanta komai nata a nutse, amma mamaki ne ya biyo bayan tunanin da yake yi, me wannan budurwa take haka a titi? Yafi dacewa ace tana gidan Aure, ko kuma tana makaranta, amma kalleta a titi tana suya.
Yaron da ya aika ne ya kawo masa ruwan, ya barwa yaron sauran canjin, ya cigaba da kallon in da Hafsa take, sai dai yadda take gudanar da lamarin nata ne, da gani ka san za ta yi izza, saboda sai shan ƙamshi take, tare da haɗe rai dan kar ma wani ya kawo wargi. A hankali Khalil ya yi you tune, ya koma hannun da Hafsat ke zaune tana gudanar da sana'ar ta. Parking ya yi a gefenta, ya fito daga motar, ya ƙaraso in da take suyar awarar ya kalleta ya ce "Sannu dai" ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa ƙasa ƙasa da 'Yawwa".Ya miƙo mata dubu biyu ya ce "Zuba mini abin nan na 2k" wani irin kallo Hafsa ta yiwa Khalil, irin kallon ka raina mini hankali ma, ba ta ce masa uffan ba, ta cigaba da sallamar yaran da ke gabanta.
Khalil gani ya yi ba ta da niyyar sake ko ɗaga kai ta kalleshi, ya kuma matsawa ya ce "Magana fa nake yi, ki sa mini na 2k""Ka bari idan ka san sunan abin da nake sayarwa, sai ka dawo in sayar maka" ta bashi amsa.
Khalil ya ce "To, ikon Allah am serious ki karɓa ki bani".
"Malam nace ka bari ka san sunan abin da nake sayarwar sai ka siya".
Yaron da ke tsaye zai sayi awara ya ce wa Khalil, "Sunan abinda take sayarwa Awara".
Khalil ya ce "Ok na gode sosai, ki bani awara ta dubu biyu".
Ba tare da kalleshi ba ta ce "Ni awarata ba ta kai ta dubu biyu ba, ta ɗari biyar kawai za ka iya samu".
"To bani ta ɗari biyar ɗin, sai ki riƙe canjin"
Hafsat ta ɗago idanunta ta harari Khalil ta ce "Malam ba fa bara nake ba, sana'a nake yi".
"Ai nima bance bara kike ba, kyauta ce kawai na baki, ta ɗari biyar ɗin ki rabawa yara sadaka, sai ki riƙe canjin".
Ba ta kuma tankawa Khalil ba, ta cigaba da iza wutarta, ya tsaya ya zuba mata ido, ta gama soya awarar dake cikin mai, ta zuba masa a leda ta miƙa masa .
Khalil ya ce "Ai ba ni zaki bawa ba, sadaka zaki bayar".
Hafsa ta ce "Ai kai ma kana da hannu, zai fi kyau ace kai ka raba musu da kanka" Nan Khalil ya shiga jinjina halin yarinyar, ana mata abin Arziƙi amma ba ta gani, sai jin kai da tsabar taƙama.
Ya sa hannu ya karɓi ledar awarar, ya miƙa mata dubu biyun, ta kalli hannunsa da yake riƙe da dubu biyun, ta ɗauke kanta ta cigaba da sabgar gabanta.
"Ikon Allah, yau Allah ya haɗani da gamona, to ga dubu ɗaya tun da ba zaki karɓi dubu biyu ba".
Nan ma ɗauke kai ta yi, ta ƙi kallon in da Khalil ya ke.
"Idan ba zaki karɓa ba zan tafi da awarar ba tare da na biya ba".
"Ka daɗe baka tafi ba" ta furta a hankali.
Khalil ya durƙusa ya sa mata dubu ɗayan, a gefenta sannan ya juya ya fara tafiya.
Ko ɗago kanta ba tayi ba, balle ta dubeshi, fifita wutar ta kawai take yi.
Yayi gaba ya bawa wasu almajirai awarar, ya kuma waiwayawa yana kallon Hafsa, cike da mamakin wannan tsatstsauran ra'ayi nata.Amina kuwa tana shiga gida, ta tarar da Baba ya dawo daga ƙauye, wurinsa ta nufa cikin fara'a, shima ya tareta da murmushi yana faɗin "Alhamdilillah".
"Baba an kai ni Makaranta, na zama 'yar Makaranta".
"Alhamdilillah, Allah yayi miki Albarka ya cika miki burinki 'ya ta".

YOU ARE READING
GABA DA GABANTA
RandomGABA DA GABANTA (Aljani ya taka wuta)😂 don't miss it, akwai cakwakiya