Shafi Na Uku

5 6 1
                                    

Kiran sallahn farko Jamila ta bu'de idon ta, na lura da ita ma baccin ba da'di ya ke mata ba sakamakon rashin cin abincin da ba muyi ba, ita kenan da har ta samu ta 'dan yi baccin, tun bayan awa 'daya da kwanciya na farka sabida tsabar yunwar da ke ci na, rabo na da abinci tun karin safe, shima tea na sha ka'dan, fargaba da kuma rashin son zuwa Kaduna ya sa ban bi takan abinci ba da muke Zaria, amma a yanzu kam ido na ya raina fata sabida ba qaramar yunwa nake ji ba. Ganin zaman ba ze mun ba ne ya sa na miqe na yi hanyar fita inda ze sada ni da bayi don 'daura alwala, a falo na samu Kawu yana azkar, ganin fitowa na ne yasa ya 'dan tsagaita, ni kuma ganin ya tsaya ya sa na duqa har qasa na gaida shi cike da girmamawa, amsa mun yayi sannan ya 'daura da

"In kun idar da Sallah ku same ni ke da Jamila, ina son magana da ku"

"To" nace ma shi sannan na shige bayin, ina fitowa na koma 'daki na tada da sallah, ita ma Jamila bayin ta wuce tayo alwala ta zo ta tada nata Sallahn a kusa dani. Bayan mun idar mu ka gaisa sannan na shaida mata saqon Kawu, a tare muka wuce falon, ba mu tadda shi a can 'din ba se kawai muka samu wurin a qasa muka zauna muna jiran shi.

A hakan muna zaune ba me ce ma 'dan uwa shi komai, da ka fahimce mu kasan akwai abunda muke saqawa a zuciyar mu, mun da'de a hakan har Kawu ya dawo ya same mu, gaida shi mukayi ya amsa sannan ya shige 'dakin Anty Bilki, tare suka fito a wannan karon shi da ita, tana sanye da dogon Hijabi har qasa amma fuskar nan ta ta a ha'de kaman wadda aka aiko ma saqon mutuwa, gaida ta mukayi cike da girmamawa, Amma a mamakin mu se ta amsa da fara'ar ta sa' banin yadda fuskar tata ta bayyana bayan fitowar ta a 'daki, wuri suka samu ita da Kawun suka zauna baki 'dayan su sannan Kawun yayi gyaran murya ya fara magana

"Jamila da Nana na kira ku ne ba dan komai ba se dan in shaida muku shawarar da na yanke a zama na da ku"

Wani da'di ne ya ziyarce ni tare da addua a zuciya ta na Allah ya sa yace Zaria ze maida mu wurin Mama ba ze iya riqe mu ba, se kawai naji yace

"Zan raba ku"

Kallon juna muka yi ni da Jamila sannan muka maida kan mu qasa muna sauraren shi da ya cigaba da cewa

" Jamila zata koma wurin Uwargida na da zama, ke kuma Nana Khadija kina nan wurin Maman Abba"

Bazan iya misalta irin tashin hankalin da na shiga ba sakamakon jin wannan mummunan shawarar se dai babu daman yin musu, haka muka ce mai mun fahimta sannan ya muna izini da zamu iya komawa 'daki, amma ita Jamila ta ha'do kayan ta tun yanzu ta fito da su, in ze wuce aiki ze aje ta. Jikin mu a sanyaye muka shiga 'daki Jamila ta fara ware kayan ta gefe 'daya, sa'banin ni da na haye kan gado na saki kuka me cin rai, kallo na ta tsaya yi ba tare da tace mun komai ba, se da nayi kuka me isa na sannan ta mun magana, amma abunda ya fito a bakin ta ban so shi ba kwatakwata, cewa tayi

"Wai ke Nana me aka maki ki ke kuka? Tun jiya kike kuka ai ya kamata ace zuwa yanzu kin yi haquri, gara mu rungumi qaddarar mu tun yanzu, tun rasuwan Baba abubuwa da yawa suka chanja, ni dai shawarar da zan baki shine kiyi haquri ki 'dau dangana in ba haka ba ke zaki wahala"

Jin maganan da ta fa'da ne ya sa na sassauta daga kuka da nake yi na kalle ta tare da cewa

"Ina kukan rabuwa da Baba duk da nasan ba zan iya chanja hakan ba, ina kukan rabuwa da Mama, Yaya Aminu da Maama amma su ma nasan dan ba su da yadda zasu yi ne, amma ke ai gaki nan a tare da ni, ai zamu iya yin wani abu a kai, mu ce ma Kawu ya bar mu tare kawai..."

Kafin na qarasa abunda zan fa'da Anty Bilki ta shigo cikin 'dakin, kallon mu tayi a tsanake sannan ta qaqalo murmushi wanda duk wanda ya kalla ya san be kai zuciya ba, cewa tayi

"Haba ke kuwa Nana, ai haquri ake yi, kuyi haquri kun ji, ai kowa da irin qaddarar sa"

Sannan ta maida duban ta kan Jamila tace

"Kawun ku ya riga ya shirya Jamila, ze je aiki yau da wuri, yace baya so 7 ta buga yana cikin gidan nan sabida suna da manyan baqi, jawo kayan ki ki fito da su in ya so in kin je can se kiyi wanka"

"To Anty" Jamila tace sannan ta ja 'daya daga cikin akwatin ta tayi waje, bin ta da kallo Anty Bilki tayi har ta fita sannan ta waiwayo kai na ta daka mun tsawa

"Ke!! Tashi daga kwanciyan nan da kika yi, kin yi wani shame shame akan gado se kace da ku'din uban ki aka siyo shi"

A hanzarce ta qaraso inda nake tare da mur'de mun kunne na, fizgo ni ta qara yi ta jijjiga ni tace

"Ki bu'de kunnen ki da kyau ki ji, ba'a mun iya shege a gida, nayi niyyan in ci uban ku ke da Yayar ta ki, amma se na lura kaman ta fiki hankali, kuma Allah ya so ta ba ita aka bar mun ba, ina godia da Allah ya sa ke aka bar mun me mugun taurin kan, zan saita ki, zan gyara maki zama, watan hankalin ki ya tsaya, zaki 'dan'dani azaba sosai a hannu na "

Tana gama fa'din haka ta qara wulla ni kan gadon, dai dai shigowar Jamila kenan, wani irin matsanancin kuka na fashe da shi, amma abunda ya ban mamaki ya gigita mun tunani shi ne abunda Anty tayi da Jamila ta shigo, bu'dan bakin ta se tace

"Haba Nana, wai kukan nan naqi ba ze qare ba, kiyi haquri Nana ta, Jamila zo ki lallashi 'Yar uwar ki"

Sannan ta fi ce waje ta bar mu, tsayawa nayi da kukan cak, dama haka ake makirci ban sani ba? To ribar me Anty Bilki zata ci?

Ayi haquri da ji na shiru dan Allah, abubuwa ne suka 'dan yi mun yawa, da fatan duk kuna lafia? To  ya kuka ji wannan shafin? Ayi comment dan Allah

Daga masoyiyar Chuchujay  Aisha Ameerah ♥️

Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING)Where stories live. Discover now