Shafi Na Hudu

5 4 0
                                    

"Gaskia Nana bazan qara baki haquri ba, kuma in har nayi waya da Mama se na fa'da mata abunda kike yi tun jiya, haba dan Allah tun jiya ake ba mutum haquri ya qi haqura, se kace wata shai'dan, ni bana son haka wallahi, mtswww ni kin ga tafiya ta, mun wuce, saduwan alheri" Jamila ta jero maganganun nan rai a 'bace, saurin saukowa daga kan gadon nayi na ce

"Wai Jamila kin san me Anty Bilki ta mun bayan fitar ki?"

A zafafe Jamila tace "me ta miki kuwa banda lallashin ki da naga tana yi, kina dai gani matar nan bata san da zuwan mu ba, jiya da muka zo kin ga yadda tayi, amma yau da mijin ta ya mata magana kin ga ai ta sauko har lallashin mu take yi, wallahi gara ki shirya yin abunda ya dace ni dai na gaya maki" sannan ta ja kayan ta fuuu ta wuce rai a 'bace, gyaran muryar da Anty Bilki tayi ne ya sa hankali na ya qara dawowa jiki na, kallon ta nake yi irin kallon tsana, amma sakamakon irin nata kallon da ya dama nawa ya sa na saukar da kai na, kallo ne take mun wanda ya ke fassara ma'ana da yawa, se da ta qare mun kallo sosai sannan ta sauke labulen da ta 'daga bayan fitar Jamilan daga 'dakin ta wuce ita ma.

Ina ji ina gani haka aka raba ni da 'Yar uwa ta wadda ita ce nasan zan kalla in ji da'di tunda nayi nisa da mahaifiya ta.

****Wasa Wasa haka tafiya tayi tafiya, kwanaki suka zama satuttuka, satuttuka suka koma watanni, a haka gangara tayi gangara har muka kai shekara uku a garin Kaduna amma fa a daddafe.
A 'bangaren Jamila ba ta samun 'kalubalai kaman nawa sabida Maman su Husna ba mace bace me takura, ita in baka shiga harkar ta ba ba zata shiga naka ba, aure suke yi da Kawu amma kaman ba aure ba sabida tunda ya qara aure ta ce su rabu, da ya qi rabuwa da ita se tace a raba gida kawai sannan kowa yayi harkar shi kawai, ba ta buqatan shi zaman yaranta zata yi, ni kam 'KALUBALAI NA (littafin chuchujay) shine makirci da muguntan Anty Bilki, zata yi abu amma ta nuna ma duniya komai lafia lau, ko da na fa'da gani zaa yi kaman sharri nake yi mata.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum rayuwar babu da'di, makarantan da muke kafin rasuwar Baban mu nan muka qara komawa kasancewar dama makarantan na shi ne, yanzu kuma ya shiga cikin gado, Yaran Kawu duk a makarantan suke suma sabida shi Mama ta ba jagorancin makarantan, shi yake tafiyar da komai na makarantan kuma Mama na jin da'din hakan.

***A 'bangaren Mama ita ma nata rayuwar cike ya ke da matsi, takura da hantara sabida Yayan ta be qyale ta, kuma wulakancin yau daban na gobe daban, Mama tayi tayi ya bata nata gadon na Mahaifan su amma yaqi shiyasa ta hanashi riqe muna gadon na Baban mu, hakan ya sa kullum yake jin haushin ta, bata jin sanyi a wurin shi ko ka'dan, abunda ya sa ya kasa korar ta a gidan ma sabida gidan gado ne, in dai har Mama ta ji 'dan sanyi to se dai in ta je gidan Yayar ta Hajiya Fateey ko kuma qanwar ta Anty Bara'atu, Hajiya Fateey tana da kirki, kyauta da kuma fara'a amma fa yaran ta ka'dai take 'dauka 'ya'ya, bata damu da damuwar a wani hali muke ba, sa'banin Anty Bara'atu da take jan mu a jiki, ita dai ba me yawan fara'a bace amma muna son ta sabida tana nuna muna kulawa duk da ita ma tana matuqar son yaran ta sannan bata son laifin su, ganin yadda Mama ke wahala ne ya sa 'yan uwan nata mata suka bata shawarar in ta samu miji tayi aure kawai, duk da Mama bata so yin aure ba ta so ta riqe mu kawai amma in ta duba wuyar da Yayan ta ke bata ba me qarewa bane se ta yanke shawarar yin auren kawai, duk da maneman nata duk babu wanda halayen sa yayi kusa da na Baban mu, kowanne da irin halin da yake zuwan mata da shi, me sauqin cikin nasu ta yanke shawarar aura kawai me suna Alhaji Saleh, Alhaji Saleh na da mata 'daya da yara hu'du, mazaunin Zaria ne shima sannan yana aiki a Katsina inda nan ne Mahaifar sa.

Bayan Mama tayi shawara da 'yan uwan ta kuma sun bata goyon bayan auren Alhaji Saleh se ta gabatar da shi wurin Yaya wanda shine ma'daurin auren su tun bayan rasuwar iyayen su, Bayan Mama ta gabatar da shi se Yayan ta ya buqaci  da ya zo yana neman shi.

A wata asabar Alhaji Saleh yaje wurin Yayan Mama, ranar kuma Mama ta zo Kaduna kawo muna ziyara kaman yadda ta saba, tana gidan Maman Husna inda aka kai Jamila Alhaji Saleh ya kira ta domin jin yaushe take ganin ta shirya ayi auren sabida idan Yayan ta ya tambaye shi bakin su ya zama 'daya dan kar ya takura ta, wata biyu Mama tace a saka sabida tana tunanin ze ishe ta tayi duk wani shirye shiryen ta, suna zaune suna hira ita da Maman Husna Alhaji Saleh ya sake kiran ta jikin shi a sanyaye, abunda ya sanar da ita yayi matuqar tada mata da hankali, kasa cewa komai tayi kawai ta aje wayan ta dafe kan ta, ganin yanayin ta ya sa Maman Husna ta tambaye ta ko lafia, a nan Mama ta shaida mata ai daga zuwan Alhaji Saleh ko dogon bayani ba suyi ba Yayan ta ya kira wasu mutane uku a waje wa'inda su ma a bakin qofar gida ya taddasu da su zo su zama shaidan 'daurin aure, sannan ya buqaci sadakin Mama daga wurin Alhaji Saleh, duk da mamaki shima ya cika shi amma ba yanda ze yi haka yayi ma Yayan Mama transfer aka 'daura aure sannan ya ba Alhaji Saleh kwana biyu ya zo ya 'dauki Matar shi, salati Maman Husna ta dinga yi, Mama ko kuka kawai take yi, bata ta'ba tunanin Yayan ta ze nuna mata irin wannan qiyayyar ba sabida gadon ta da ta buqaci a bata da kuma gadon yaran ta da ta hanashi.

Hello lovelies, ayi haquri da jina shiru da akayi, kar ku manta kuyi comments please, daga masoyiyar Chuchujay  Aisha. Ameerah ♥️

Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING)Where stories live. Discover now