Shafi Na Biyar

3 1 0
                                    

Duk da Mama tana son ta auri Alhaji Saleh har cikin ran ta, amma yanayin yadda aka 'daura mata aure da shi ya tsaya mata a rai matuqa, haka nan tana ji tana gani aka 'daura mata auren da bata yi tsammanin yin shi a wannan lokacin ba.

Jikin ta a sanyaye ta koma Garin Zaria bayan Maman Husna ta lallashe ta ita da Kawu, Kawu har gidan Maman Husna ya sama Mama bayan yaji irin hukuncin da Yaya Madu ya yanke, kasancewar ba hurumin su bane ya sa suka ce ma Mama ba sa so su sa baki a ciki dan gudun fitinar Yaya Madu, ban  samu ha'duwa da Mama ba sabida bata qaraso gidan Anty Bilki duba ni ba se dai kawai ta ba Kawu saqon da ta saba kawo muna in ta kawo muna ziyara.

**Mama na shigowa gidan da sallama Matan Yaya Madu suka tsare ta da ido, yanayin zaman da suka yi a tsakar gidan ze tabbatar da cewa akwai wani damuwan bayan wanda ta dawo da shi, ganin hakan ya sa ta qaqalo murmushi ta shimfida a fuskar tare da yin sallama a takaice sannan ta samu guri a gefen su ta zauna, bayan sun gama gaisawa se Babbar Matar shi ta sanar da Mama cewa Yaya Madu yace da ta shigo gida yana son ganin ta, hakan ko akayi ta tashi ta miqe ta nufi sashen sa. A zaune ta same shi yana cin abinci yana kallo, fuskar nan ta sa babu walwala kwatakwata, sallama ta yi ta zauna a qasa a 'dan nesa da shi sannan tace

"Ina Wuni Yaya, na same ku lafia"

"Lafia lau" yace sannan ya waiwayo gare ta bayan ya rage qarar TV ya dube ta, gyaran murya yayi yace

"Da fatan saqo na ya riske ki Zainab"

"Eh toh, saqon auren da kayi mun ya iso amma ban san ko akwai wani ba"

"Ita Sa'a bata gaya maki abunda na ce ba?"

"Ta ce mun kana son gani na idan na shigo gida"

"Shikenan?"

"Eh shikenan abunda ta gaya mun"

"Ina Amina?"

"Tana gidan Yaya Fateey ba da ita naje Kaduna ba"

Numfasawa yayi ka'dan se yace

"Saqon shine Mijin ki ze zo ya tafi da ke nan da ke nan da kwana biyu, sadakin ki ya na hannu na, duk sanda buqatar baki ya tashi zan baki"

'Dago kai Mama tayi ta kalle shi sannan ta sake sauke kan ta, be ma lura da kallon da tayi mai ba ya cigaba da cewa

"Ina son ki bar Amina anan wuri na, za'a kula da ita ba damuwa"

Gaban ta fa'di yayi da  taji abunda ya furta, hankalin ta in yayi dubu ya tashi, ta ina zata fara barin wannan jaririyar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba a cikin yaran Yaya Madu masu yawan gaske gashi duk sun manyanta, a wurin wa zata bar ta, kulawan da bata samu bane da take nan za'a mata bayan bata nan, Yaya Ahmadun da ko makaranta ya kasa saka ta, ko kuma Matan sa da ko a jikin su duk abunda ake mata, yanzu ta gane dalilin sanyin jikin na matan shi, tunani suke wa za'a 'daura ma 'dawainiya a cikin su, a gaskia ba zata iya barin Maama a gidan nan ba.

Qara gyara zama tayi tace

"Yaya nace wai shi Alhaji Saleh ne yace kar in taho da Maama gidan sa?"

"Kaman ya? Haka nace miki? Haka na ga dai ya kamata ko zaki mun musu ne? Ya zaa yi ki 'dauki 'yar wani ki je mai da ita gida, an gaya maki kowa ke son haka? Haba Zainab dan Allah ki dinga dogon nazari mana, ga ki a fuska kaman me hankali amma duk abunda aka gaya maki se kinyi musu, ban ta'ba gaya maki abu ba ki fa'di naki ra'ayin ba, yanzu dai na gama magana, Yarinya Amina bazata biki gidan miji ba, ki chanja wannan tunanin in ma kina da shi, na gama magana zaki iya wucewa"

A fusace yake ta magana ya ma qi bari ta sake magana, juya fuskar shi yayi bayan ya gama koro jawabai sabida kar ma ta ga fuskar sake wani magana, tashi tayi ta nufi hanyar fita jikin ta duk a mace, a bakin qofa ta ci karo da Hajiya Fateey riqe da Maama a hannun ta, gaisawa suka yi sannan Maama ta saki hannun Hajiya Fateey tayi gurin Mama, ganin haka ya sa Hajiya Fateey ta yi dariya ta ce

"Iyyee dan kin ga Maman ki ko? Yaro kenan, wa ze raba uwa da 'danta ai se Allah se kuma mara tausayi"

Murmushi kawai Mama tayi tace

"Bari mu shiga cikin gida"

"Toh nima bari in gaisa da Yaya Madu"

Da sauri Mama ta ja hannun Maama suka wuce 'dakin kwanan su, suna shiga ta riqe Maama gam a jikin ta ta fara kuka me tsuma zuciya, kuka take yi sosai harda shashsheqa, maganar Maama ne ya dawo da Mama daga duniyar kukan da ta shiga, cewa tayi

"Mama kin matse ni"

Sakin Maama tayi tace

"Yi haquri yarinya ta, Allah ya raya mun ku, ya kare ku da kariyar sa, Allah ya riqa mun ku a ko da yaushe"

Shigowan Hajiya Fateey ne ya sa Mama ta tsagaita kukan ta, samun wuri suka yi suka zauna kowacce da abunda take kitsawa a zuciyan ta, ganin shirun nasu yayi yawa ne ya sa Hajiya Fateey tace

"Naji duk abunda ya faru Maman Nana, ba abunda zan ce maki sai dai in ce kiyi haquri, kuma Allah ya baki ikon cin jarabawan ki, yara kuma da ba sa hannun ki suma kiyi haquri ki dinga masu addua, kin ga kula da su ze 'dan yi miki wahala tunda ba aiki kike yi ba kuma babu wata sana'a me qarfi da ki ke yi"

Mama dai bata ce komai ba har ta gama maganar ta ta gaji tayi shiru sabida a sanin ta inda Hajiya Fateey ce aka yi ma yadda aka mata ba zata jure ba ko ka'dan, kuma a yadda ta san ta da son yaran ta bazata yarda a rabu su haka ba, cigaba da magana Hajiya Fateey tayi

"Yanzu me ne ne shirin ki Zainab?"

Se a yanzu Mama tace

"Banda wani shiri, kayan 'daki ne kawai nake ji yanzu, Amma zuwa anjima zan nema Alhaji Saleh ya zo se in ga yadda za'a yi, abun ya zo a qurarren lokaci"

"Eh hakane, to Amma dai kin san ba auren fari bane ko? Auren bazawara ai ba ya buqatan wani shiri, Allah ya bada zaman lafia, ni zan wuce, duk yadda ake ciki se muyi waya"

"Toh se anjima" kawai Mama tace sannan ta bi Yaya Fateey da kallo har ta fice daga 'dakin, laluba wayar ta tayi ta kira Alhaji Saleh a waya, bayan sun gaisa ta ce mai tana son ganin sa in ba ze damu ba, nan ya sanar mata da ana idar da Sallahn magriba ze zo.

Tashi tayi ta 'dauro alwala ta gabatar da Sallahn magriba ita ma ta zauna tana lazumi tana tsumayin zuwan sa, bayan wasu 'yan mintuna ya kira ta ya shaida mata ya qaraso, har cikin gida ta shigo da shi ta shimfi'da mai tabarma suka zauna wani gefe a harabar gidan, bayan sun gaisa se ta tambaye shi a ina zata zauna, ce mata yayi

"Da yake abun ya zo a qurarren lokaci kuma gaskia banyi wani tanadi me yawa na auren nan ba, na yanke shawarar ha'da ki zama da Uwar gida na a gidan da muke zaune yanzu, akwai 'daki 'daya da ba a gyare ba shine kawai za'a gyara, matsalan dai shine yanzu banda ku'di sosai a hannu na da har ze ishe ni inyi gyaran, ban san ko zaki iya roqan alfarma ba a wurin Yaya da ya 'dan qara muna lokacin tarewar "

Ce mai tayi
"Kar ka damu hakan ba ze gagara ba, a cikin ku'di na da ake juyawa mun a wurin 'dan uwan su Baban Nana zan sa a bani wani abu se in ba ka ayi gyaran"

Murmushi ya saki yace

"Nagode sosai kuma In Sha Allah ina samu zan baki abun ki"

"Kar ka damu ba se ka biya ba, kyauta na baka"

"To to to Madallah, Nagode sosai Allah ya bamu zaman lafia"

"Ameen alfarmar manzon Allah, ina so ka 'dan yi mun uzuri zan shiga gida yanzu, Gobe za'a turo ku'din da yardar Allah"

"To ba damuwa, Nagode sosai se da safe"

Hello everyone, ayi haquri da jina shiru dan Allah, abubuwa ne suka 'dan mun yawa, Amma fa Ina da qorafi, bana jindadin rashin comment din ku gaskia, Anya ba zan daina littafin nan ba kuwa? Na ga kaman baya qayatar da ku

Daga masoyiyar Chuchujay
Aisha Ameerah♥️

Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING)Onde as histórias ganham vida. Descobre agora