Shafi Na Shida

4 2 0
                                    

Babu Biki babu gayyata haka Mama ta tare a gidan Alhaji Saleh bayan ta kashe ku'di sosai tunda daga wurin gyaran gida, kayan 'daki da kuma suturar da zata sa, rai babu da'di haka ta tare a gidan mijin kasancewar rigimar da ya shiga tsakanin ta da Yaya Madu akan Maama, ranar da zata wuce gidan mijin ta ta ha'da ma Maama kayan ta tace da ita zata je, haka aka dinga kai ruwa rana, har Alhaji Saleh se da ya sa baki amma Mama tace ita dai a bar mata 'Yar ta, hakan ne yasa Yaya Madu yace ko a mafarki kar tayi tunanin sake kiran sa da Yayan ta, kuma kar ta kuskura tace zata dawo gida da sunan yaji ko kuma an sake ta, a hakan ma cewa tayi taji ta gani kuma ta amince, sannan yace ko da wasa kar ta danganta shi da lamarin ta ko na yaran ta, se da wani 'dan uwan Maman su ya shiga maganan sannan Yaya Madu ya janye kalaman sa na kar ta sake cewa shi Yayan ta ne amma fa ya ce shara'din da ya gindaya mata yana nan.

Haka lokaci ya cigaba da tafiya, a kwana a tashi Mama tayi wata shida a gidan Alhaji Saleh, abubuwa da yawa sun chanja, Alhaji Saleh ya fito da asalin halin sa na tsatsauran ra'ayi, yau da'di gobe akasin haka, sannan kullum gani yake yi kaman shi yayi mata alfarma, ita kuwa Mama wani irin son shi ta kamu da wanda kwatakwata bata ganin laifin sa, a da kafin Mama tayi aure se ta kawo muna ziyara kusan so uku a wata amma tunda tayi aure so biyu ta ta'ba zuwa ta duba mu, ta karkata hankalin ta gaba 'daya kan Alhaji Saleh, yaran sa da kuma hidimar gidan sa, Yaya Aminu ko tunda Mama tayi aure so biyu ya dawo hutu daga makaranta kuma duk lokacin da yazo gidan wani 'dan uwan Baban mu yake zama, irin abunda ya fuskan ta a zaman gidan ne ya sa baya sha'awar dawowa hutu, sannan a gidan Mama baya samun sakewa sabida duk sanda ze je gidan se ya tarar da ita tana ta aikin gidan ta, ko kuma tana wurin mijin ta.

Maama ta zama abun tausayi sabida Mama ta chanja sosai, mu kan mu da muke Kaduna kewar Mahaifiyar mu muke yi sosai, gashi ni inda nake zama yafi na su tashin hankali duka, tun Anty Bilki na tsangwama na har ya kai ga ta fara saka hannun ta a jiki na da sunan duka, ina shan duka sosai a wurin ta sabida duk qanqatar abu in nayi tashi take yi ta zane mun jiki na, ita kuma Jamila baiwa ta koma a gidan su Husnah, kullum cikin aiki take, ba za'a iya banbance ta ba da me aiki ba, kullum cikin aiki take ba ji ba gani, yaran gida kam se dai su kwanta su huta, ba ta fuskantan komai irin nawa amma tana jibgan aiki sosai a gidan, ni kam azaba nake sha a hannun Anty Bilki.

*****Dawowar Mama Kaduna ba qaramin farin ciki ya saka muna ba sabida a ganin mu duk wani sauqi zamu same shi yanzu tunda tana kusa da mu, abunda bamu sani ba shine ba za'a taba ayyana abunda ze faru ba a rai har se in ya faru 'din.
Ranar da suka tattaro komai na su suka dawo Kaduna munyi matuqar farin ciki sosai, Mama har gida ta samu kowacce mu ni da Jamila tayi muna albishirin dawowa kusa damu, hakan be yi ma Anty Bilki da'di ba, rashin jinda'din nata har a fuska ya bayyana sabida ta kasa 'boye shi, amma ni ba na Anty Bilki ya dame ni ba sabida nasan manufar ta, Kawu da ya nuna ma Mama cewa zama a Zaria se ya fi mata kwanciyar hankali shi ya 'daure ma Mama da mu kan mu kai, amma ba wanda ya kawo komai a ran shi dan a cewar Mama shine qila Kawu ba ya son ta tuna da Baba ne da yadda suka yi zaman aure kafin mutuwar sa.

A kwana a tashi Mama ta shafe shekara 'daya ita da Mijin ta, Matar sa da kuma 'ya'yan sa a Kaduna, ba mu cika zuwa kai mata ziyara ba sabida makaranta amma ita tana yawan zuwa wurin mu.
Wata rana se Mama ta tashi da rashin lafia me tsanani wanda hankalin kowa ya tashi, Kawu ya kwashe mu ya kai mu har asibiti muka duba ta, a nan ne kuma ya mata alqawarin kawo mu hutu wurin ta da zarar an sallame ta, hakan ko akayi sabida a ranar da aka sallame ta muka ha'da kayan mu bisa umarnin Kawu sannan ya kai mu gidan Mama.
Tayi matuqar farin ciki da ganin mu ita da Maama, ya bayyana sosai a fuskar su domin se nan da nan suke yi da mu kamar wasu baqi na alfarma.

Sashin Mama da abokiyar zaman ta duk wurin 'daya ne, kowacce da 'dakin ta se kuma na yara, a gefen na su kuma shi ma akwai na mijin su, gidan be da wani girma, falon su guda 'daya ne dukkan su, se 'dakunna su, se kitchen 'daya bayi kuma guda biyu, 'daya a cikin 'dakin mijin su 'dayan kuma shi suke shiga dukan su. Ko da muka zo mijin Mama yayi tafiya amma ta ce muna washe gari ze dawo, tunda muka shigo gidan ake bin mu da wani irin kallo, yarinyar gidan wadda ake kira da Ummi, qannen ta biyu mata Rahama da Ruqayya, se kuma namiji guda 'daya Daddy, wani irin kallo ne me wuyan fassara, amma kuma me cike da ma'ana da yawa. Maman su kuma irin makiran matan nan ne sabida halin ta be ma 'boyuwa, tana son shiga jikin Mama sosai tare da yi mata shishigi da son jin sirrin Mama, a bakin ta muka ji cewa Mama juna biyu take da shi sabida kwatakwata bakin matar baya rufewa tsabar surutu, ga Iyayi da kau'di.

Kasancewar ranar da muka zo Mama ce da girki ya sa mu ka shiga kitchen tare da ita muka taya ta, bayan ta gama girkin ta zuba ma Maman Ummi, ta zuba nata ita da Maama sabida Maama bata son cin abinci hakan ya sa suke ci tare sabida ta tilasta ta dole taci, ta zuba ma Daddy na shi daban sannan ta samu babban tray ta zuba muna tare da su Ummi, a falo aka aje abincin sannan ta kira su Ummi, bayan ta tabbatar kowa ya zauna se ta wuce da nata 'daki ita da Maama.

Mun saka hannu kowa na cin abinci amma Rahama da Ruqayya se tattara abinci suke yi gaban su, Yayarsu kuma na kallon su amma bata ce masu komai ba, ita kuwa loma kawai take yi kaman abincin ze gudu, a fuskar Jamila akwai damuwa amma bata ce komai ba, da naga abun ba me qarewa bane se na ce ma su

"Wai meye haka kuka yi?"

Kallon banza dukan su suka watsa mun suka cigaba da abunda suke yi, qara cewa nayi

"Dan Allah ku daina tattara abincin gaban ku ku bari mu ci tare gaba 'daya"

Daddy da ke kan kujera yana cin abinci ne ya ce

"Wai ku Rahama ba da ku ake magana ba, Yaya Ummi ki masu magana"

Se a sannan Ummi tace

"In ce masu uban me? Ita ma tayi yadda suke yi mana, mtswww kuma sannan mu da gidan mu"

Dai dai lokacin da Maman su ta fito daga 'daki kenan, daka ma Ummi tsawa tayi tace

"Ke Ummi!!"

Hankalin mu duka komawa yayi kan ta muna jiran abunda zata fa'da........

Daga masoyiyar Chuchujay 
Aisha Ameerah♥️

Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING)Where stories live. Discover now