chapter 1

34 1 0
                                    

💋_ALAQAR MU!💋_
~Our Destiny!~

©️®️~Hafsatouamjad~

Chapter 1

~DANDANO~!

✍️Tafe yake da ɗan gudun sa akan shimfiɗaɗɗiyar kwaltar da ya ƙawata street ɗin gabaɗaya, gidaje ne a jejjere wanda kusan ginin su duk iri ɗaya ne, yayin da wasu irin haɗaɗɗun flowers suka yiwa ƙofar kowane gidan ƙawanya.

Shar kwaltar take babu gilmawar motoci haka kuma ungwan yake tsit kowa na rufe cikin gidan shi kasancewar duhun asuba bai gama yayewa garin yayi haske baki ɗaya ba.

Farin saurayi ne wanda yake late 38 ɗin sa, kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci arziki da nasaba sun zaunar masa duba da irin yadda fatar jikin sa take sheƙi, fararen murɗaɗɗun muscles ɗin sa dake bayyane kasancewar shigar armless pajamas ɗin dake jikin sa ne zai sake tabbatar maka da shi ɗin ba irin ƙananun masu arziƙin nan bane ba, haka kuma jikin sa ke a murɗe kasancewar sa ma'abocin motsa jiki a kullum.

Ɗan dakatawa yayi da gudun da yake yana stretching hannayen sa cikin kwarewa, a takaice dai jogging ya fito kamar yadda ya saba a kullum.

Cigaba yayi da gudun nasa wanda za'a iya alaƙanta hakan da sauri, so yake ya koma gida ganin dai garin ya fara haske.

Shigowar sa street ɗin su ya nufi hanƴar gidan su zuciyar sa cike da kwaɗayin early morning coffee ɗin da mahaifiyar sa ta saba haɗa masa.

Tafiya ya soma cikin takun sa mai ɗaukar hankali hannayen sa zube cikin aljihun wandon sa yayin da yake ɗan kaɗa kansa sakamakon head-phone ɗin dake manne da kunnen sa yana sauraran ƙira'ar Sheikh Abdul Rahman Mas'ood, kansa sadde a ƙasa as usual yazo wucewa ta ƙofar gidan dake kusa da nasu, a kullum yana ƙoƙarin avoiding kallon gidan ba dan komai ba sai dan dalilin da ya bar wa zuciyar sa shi kaɗai.

Bai idda ƙarasa zuwa ƙofar gidan su ba idanun sa suka sauƙa kan wani abu da yaja hankalin sa, sam shi ba mutum ne mai shiga sabgar da ba tasa ba, but haka kurum ya tsinci kansa da dosar inda yake ganin abin wanda dai yafi kama da mutum.

Saurin ja yayi ya tsaya expression ɗin fuskar sa na canzawa zuwa mamaki, he can't believe abin da idanun sa ke gane masa.

At first yayi tunanin wucewa kawai yayi tafiyar sa sai dai kuma ba zai taɓa yin hakan ba kasancewar sa mutum mai tausayi da kuma sanin yakamata.

Jujjuyawa yayi yaga street ɗin shal babu kowa kafin yayi saurin ƙarasawa inda yarinƴar da he has no idea koh wacece ke yashe.

Durƙusawa yayi kan guiwowin sa yana ƙare mata kallo, doguwar rigar abaya ce a jikin ta wanda bai gama rufe mata fararen ƙafafuwan ta da jini ya ɓata ba, fuskar ta kuwa rufe take da doguwar gashin kanta hakan ya sanƴa bai gane koh wacece ba.

Ganin ta cikin halin nan ba ƙaramin tsorata shi yayi ba, abu ɗaya ke bashi mamaki yadda akayi aka yasar da ita anan ba tare da sanin kowa ba.

A hankali ya kai hannu ya yaye gashin da ya rufe mata fuskar yayin da idanun sa suka yi arba da kyakkyawar fuskar ta.

Wani irin mugun shock ya shiga ganin zuciyar sa na beating so very fast sakamakon wacce yake gani kwance wacce sam babu alamun numfashi tattare da ita.

Wawwaigawa yayi sai dai babu kowa anan wurin in banda kukan tsuntsaye da ya cika wurin, sake maido duban sa yayi kanta kafin ya kalli ƙofar gidan da aka jefar da ita inda nan ne gidan su yarinƴar.

Baiyi wata-wata ba ya miƙe da saurin sa ya faɗa gidan su wanda ke makwabtaka da gidan su yarinƴar, koh mai gadi dake yi masa gaisuwa bai amsa ba sai ma haɗaɗɗiyar part ɗin sa da ya nufa tare da zaro makulli ɗaya cikin keys ɗin dake jere a wurin ya fito, danna control ɗin makullin yayi take mota ɗaya ta bada ƙara haɗi da jan light inda baiyi wata-wata ba ya nufi motar ya shige, mai gadin ganin ya doso gate da gudu ya sanƴa shi saurin zuwa ya danna wani abu kamar switch take gate ɗin ta buɗe da kanta ya fice daga gidan.

ALAQAR MUWhere stories live. Discover now