Chapter 2

5 0 0
                                    

💋_ALAQAR MU💋_
~Our destiny ~

©️®️ _Hafsatouamjad_

Chapters 02

✍️Ya kwashi ak'allah 30minutes azaune all this time Kallon ta yake bayaso ko kiftawa yayi , ahankali ta fara k'okarin bude idanuwanta da suka canza launi zuwa jaaa sun yi wani mugun kumbura ,hakan ze tabbatar maka da ba karamin kuka tayi ba , seda ta gama bude idanuwan nata akan celine din Asibitin ahankali ta waiga side dinta na hagu tana kara Lumshe idanunta , abunda ya faru ne ya fara dawo Mata cikin kwakwalwarta wani razanannen ihu ta saki daya janyo hankalin nurses din dake yawo a reception dakin suka nufo Da gudu ,Ganin Noorain akanta yasa nurses din suka bashi hakuri ya fita , Babu yanda ya iya dole ya fito adakin yana rike kanshi dake barazanar Cirewa .
Girgiza kanta take tana riko hannun nurse dinnan cikeda azaba da fargaba tace "Ka barni na tuba da zafi ,Dan Allah kayi hakuri karkayi ".
Abunda take ta fada kenan duk ta rikitasu ,lokaci daya tausayinta ya kama zuciyoyin su ,yarinya Karama da ita
Da sauri suka kira babbar likatan ta shigo , allurar bacci ta Mata ganin taki dawowa hayyacin ta .
Sauke numfashi sukayi atare lokacin da baccin ya fara dibarta ,ahankali ta Lumshe idanunta hawaye na gangaro Mata a side din idanunta .

Doctor tana fitowa ta kalleshi tace "Munyi Mata allurar bacci ,ya kamata ka fadawa iyayenta halin da ake ciki saboda kula da ita dole se mace ".
Fitowa yayi daga asibitin zuciyansa duk babu dadi , koda ya koma gida be nufi part din Mommah ba ,seda yaje yakarayin wanka ya shirya sannan ya fito ganin lokacin xuwa office dinshi yayi .

Seda ya fara tsayawa A kofar gidan su yai parking ya dade yana kallon gate din gidan sun yana nazari,Dole ya sanarwa da iyayenta sabida yasan komai rintsi zasu sani ,bashi da wani option dole ya fito daga Motor ya nufa kofar gate din cike da nutsuwa da kamalar shi .Knocking yayi a kofar tasu me gadin ya leko yana tambayar waye ,ganin Noorain Ne yasa me gadin ya fadada faraarshi yana cewa "Ranka shi dade ka shigo mana "
Babu musu ya shiga ya tsaya daga jikin kofar yace "Inason ganin Ammah Asmah ne "
"Toh Toh bara afada musu "
"Asmau mauuuu Ina kike "
Me gadin yake Dan raira wakar shi har ya shiga cikin dakin ,landline din dake jikin katangar dakin nashi ya latsa sannan ya kara a kunne
Babu jimawa ya fito ya kalli Noorain yace "Ance ka shiga "
Godiya ya mishi yai cikin gidan gaban shi na faduwa ,harya manta Rabonshi da gidan .
Koda ya shiga parlour babu kowa tsit yake se Tv da take a kunne amman ko sounds babu , ga kuma sanyin da parlour ya dauka da kamshin Air freshner ,daya daga cikin kujerun parlour yayi ma kanshi maxauni ,ko minti biyu beyi ba Ammah ta fito sanye da babban hijjabin ta har kasa ,Ganin Noorain ne yasa ta fadada faraarta tana zama akan kujeran dake Dan nesa dashi tace "Noorain kaine yau agidan "?
Saukkowa yayi a kujeran yana gaisheta cikeda ladabi , amsawa tayi fuskanta awashe tana tambayar ya Maman shi dasu Mamah da Lafiya ya amsa sannan yayi shiru , sosai yake nazari bega wani alaman daze nuna mishi Ammah na cikin damuwa ba ,hankalin shi ya rabu gida biyu ,kallon shi Ammah tayi ganin kamar akwai alamun magana abakin shi tace .
"Ina sauraron ka Noorain "
Ammah ta katse masa Tunanin sa ,gyara zaman shi yayi sosai kanshi akasa yace "Dazu da safe na fito jogging naga mutum kwance akofar gidan nan ,naso na wuce amman ganin kamar mutumin yana cikin mawuyacin hali ne yasa dole na dawo abunda ya ban mamaki mace ce kuma Asmah ..."
Dagowa Ammah tayi da sauri tana kallon shi ,Murmushi tayi mishi tace "Aa Noorain Badai Asmah ba ,jiya ta tafi gidan kanwata dake kaduna zata Mata sati daya ta dawo gaskiya inajin kamace "
Ammah ta fada da confidence duk da hankalinta ya fara tshi ,duk wani abu da ze shafi Asmah yana damunta .
Sauke numfashi yayi yana nazari kafin yace "Ammah ba kama bace Asmah ce yanzu haka na kaita asibiti ,Zaki iya shiryawa muje ki ganta ".
Innalilahi wainnaillahi rajiun Ammah ta fada azuciyar ta , Da sauri ta tashi tace mishi tana zuwa daki ta koma ta daukko Wayarta da takalmi ta fito tana ce mishi su tafi , a compound suka hadu da Ansar da ya fito da shirin sa na zuwa aiki ,ganin Ammah a rude yasa ya karaso inda suke yana mamakin ganin Noorain tare da Ammah da sanyin safiyan nan .
"Ammah Lafiya kuwa "?
"Just follow me ".
Abunda ta iya fada kenan tabi bayan Noorain da ya kusa fita gate din ,Motor shi ya shiga yabi bayansu,duk yanda Ammah taso kada ta tada hankalin ta abun ya faskara gumi ne kawai yake zubo Mata Noorain yana lure da yanda hankalin ta ya tashi ,duk seyaji ta bashi tausayi .
Tafiyar 20minutes ne ya karaso dasu babban asibitin ,parking yayi ya fito itama Ammah ta fito ,Ansar ma da yayi parking Motor shi ya biyo su abaya .
Tun daga reception Ammah ta fara jin muryan Asmah tana kuka ,wani mugun faduwan gaba ne ya ziyar ce ta ,batabi takan Noorain ba tayi gaba da sauri tana bin direction din da takejin kukan , cikin dakin Ammah ta shiga hankalin ta a tashe abunda bata taba tunani ba da sauri tace "Asmah na "
Zabura Asmah tayi ta juyo tana kallon Ammah da gudu ta saukko akan gadon tayo kanta tama manta da ciwon dake jikinta burinta be wuce ta karasa wurinta ba , bude Mata hannu Ammah tayi ta fada jikin ta tana sakin wani Marayan kuka ,muryan ta ya dashe idanunta ko iya budesu batayi da kyau .
Tsyawa Ansar yayi cak yana kallon Asmah ,Yaushe ta dawo daga kadunan? Me takeyi a Asibiti kuma ?
Fita nurses din sukayi a dakin suka barsu su kadai , Ammah gaba daya ta kasa magana kukan Asmah yana ratsa Mata jinin jikinta , gashinta daya barbazu a fuskanta take ta matsar Mata dashi tana pating bayanta ,
"Ammah yaushe little ta dawo "?
Daga mishi Hannu Ammah tayi ,alamun yayi shiru .
A gefen gadon ya zauna yana zurawa Asma idanu har Yanzu kuka take .
Sallamar likitan ne yasa suka dago ,Asmah na ganin likitan ta kara kankame Ammah tana cewa "Ammah mu tafi gida am scared "
Seda takai kunnenta saitin bakin ta taji abunda take fada
Buga bayanta tayi tace "Oaky Yanzu zamu tafi don't cry ".

ALAQAR MUWhere stories live. Discover now