_20-23_
*K'ANDE*
Ink'iya:-Nita Dabance!!!
*NA NANA DISO*
Baba baba sai ta fashe da k'uka..." Kar kice min mutuwa yayi tana kuka tana jijjiga 'yar uwar k'ande data hango mutum akwance baba ya zaka tafi kabarni wayoo nan i tama ta suma....
" goggo ce ta dauk'e k'ande ta k'aita dak'i da gudu sadiya ta bita nan aka shirya baba sai gidan sa na gaske kowa a kauyen sai da yaji mutuwar alhaji yakubu, su ya abbas sai zirga zirga sukeyi har aka dawo daga kai mahaifin su, kowa agidan sai kuka yakeyi..
" goggo tana shigowa ta k'wara wa k'ande ruwa...
" wayyo Allah na shiga uku k'atana yak'are tasaka ihu wayyo Allah babana Allah yajikanka yayi maka rahama!
" zaki rufemana baki ko sai ranki ya baci..
" k'ande cikin kuka tace ai bacin rai ta fara haduwa dashi har...
" iya habu ta taso tace haba k'ande menene haka kuka banaki bani ba addu'a zakiyi masa...
" wane sabon kukan ne yazubo mata nayi shiru kikace? Kinfine sanin dacen mutuwa kuma ace masoyin kane yatafi...
" toh kiyi hakuri dai...
" babu wanda takara kulawa tunda ta kwantar da k'anta acinyar ta!
" mutane sai gaisuwa ake shigowa..
" goggo da idon ta ya kumbura ta kalle farida tace kidaina kuka domin babu abunda zaiyi miki sama da kisa kanki amatsala..
" farida tace bana tunanin zan samu miji kamar baba, mai tausayina mai sona ga sanin damuwa ta...
" haba farida Allah shi yakarbe abunsa kuma yafemu sonsa...
" Tohm goggo...
Yau sadakar bakwai angama addu'a su goggo sunata karbar gaisuwa!
" babu yadda ba'ayi da k'ande tayi wanka ba Amma tak'i in banda wari babu abunda takeyi...
" k'ande bazakiyi wankan baniba? So kikeyi kijawo mana magana!
" sadiya tace ai goggo bakije warin datakeyi na! Duk ta cika mana dak'i...
" farida tace ai nema tazo nakusa amai saboda warin hammatar ta...
" kuka tasaka tayi gefe tare da tausayin kanta taje sannan tace wari innayi kaina ne kuma jikina ne!
" iya habu da sauran yan gaisuwa sukace tsafta dai tana daga cikin imani..
" haba dame zanji? ba zanyi ba ai jikina ne!
" hajiya asabe tace Ai k'ande ta dabance...
" yaya Abbas ne ya shigo ke k'ande kizo inji adam?
" me zanyi masa?
" gaisuwa zai yimiki tun daga birni yazo yimiki gaisuwa!" lokacin da yatafi birni ai bai gayamin ba kuma gaisuwa bazan fito ba nayafe! Yayi masa Addu'a daga nan...
" anya kinada hankali?
" ai kasan haukan gadonsa akeyi...
" iya habu tace tashi k'ande kije mana!
" wallhi bani zuwa yayiwa su baba datti gaisuwar...
" to kai Abbas jik'ace bata fitowa...
K'ande ce ta zauna kusa da goggo tana fadin tabata gurasa...
" anya k'ande kinji warin dakikeyi subhanallahi wannan wari haka!
YOU ARE READING
K'ANDE
Romancek'ande Yarinya ce karama fitinanniya Kuma matsokaniya, bata shakkar kowa akauye, kullum burrin ta taje birni tayi karatu! zuwanta birni ya chanja ta? karatun datakeso ta soma? Amma Kuma kalubale da matsalar rayuwa Sai tunkarota suke! mahaukacin da t...