part 4

146 6 0
                                    

Tun daga nesa na hango hajara a bakin kofar ajinmu tana zaune,da Sauri na na karasa wurin ta na rike ta.nace mata hajara ya jikin?ai  banyi zaton zaki zo makaranta yau ba.tace Ai naji sauki sosai amma sai da nasha allurori.nai  dariya nace Ai nima kinsan banson allura.muna rike da juna  muka shiga aji muka zauna.ana fita break muka samu wuri muka zauna.nayi ajiyan zuciya nace mata kawalli daman akwai abunda yake damuna nake son in gaya miki.naso Nazo har gida muyi magana amma sai naga baki da lafiya,ko nazo  ba baza ki bani hankalin ki ba.hajara ta juyo ta kalle ni tace kawalli Fada min inji ke kuwa me yasa ki cikin damuwa haka.na gyara zama nace mata wallahi mallam Nasir ne ban gane mada ba kwana biyu.tace name fa.idan fa muka hadu sai ya rinka  kallo na ido cikin ido har sai na sunkuyar da kaina  kasa don kunya,kuma ran juma'a ya kira ni office dinsa wai in bashi adireshin gidanmu. Nikam na rasa mai zai yi da adireshin gidanmu na Fada yayin da nake sauke wata ajiyar zuciya.hajara tai dariya tace dadina dake  lubna saurin damuwa.toh yanzu don ya tambaye ki adireshin gidanku shine wani abun damuwa.nace mata Ai ko abun damuwa ne tunda bansan ko laifi nayi masa  ba yake so ya kai karata.hafsa tace haba dai ai  kinsan Indai mallam Nasir ne kikayi masa laifi ba sai ya kai karar  ki ba,a gurin zai hukunta ki.ki kwantar da hankalin  ki kawai.nace mata toh babu damuwa Allah dai yasa ba wani abun bane.tace ameen.muka tashi muka koma aji domin daukan darasin gaba.
   Lokaci  sai gaba yake domin yau sauran sati biyu mu fara zama jarabawar mu ta fita sakandare.na dukufa gurin karatu da kuma nafilfilai na tsakan dare domin Neman nasara gurin sarki Allah.wani abun dana kula shine mallam Nasir ya Faye samun ido cikin yan kwanakin  nan.bai dai mun magana ba Amman dai yana shigowa ajin mu zai saka mun ido ko kuma idan mun hadu a hanya.hajara dai in taga  haka sai tayi ta min dariya.INA isa gida na tararda Yaya Maryam ta iso daga makaranta na ruga na rungume ta.tace lubna kenan har yanzu dai baza ki girma ba gashi  dai har kin kusa tafiya  jami'a.nace haba  Yaya Maryam Ai ko na tafi jami'a idan na ganki sai na rungume ki.muka SA dariya duka daidai lokacin yaya imran ya shigo,yana shigowa ya tsuguna ya gaida hajja.suka gaisa da Yaya Maryam.ya juyo yace ke kuma lubna nine baza ki gaida  ba yau ko,nace masa  ba kaki siyo min wayar da kace zaka siyo min ba.Yaya imran ya zauna bisa  kujera yace Ai na Fada miki sai kinci jarabawar ki sannar in sai miki waya.hajja tace kayi  min dai dai,so take  waya ya dauke mata hankali taki  karatun jarabawar tasu.Yaya Maryam tace ah haba  Ai babu abunda zai hana lubna karatu Ai yarinyar akwai kwakwalwa,nace yauwa Yaya gaya musu dai.muna cikin haka Babanmu ya shigo yayi sallama ya zauna kan kujera,duk muka tsuguna muka gida shi.bayan an gaisa sai Yaya Maryam tace daman baba INA so in tambaye ka izini zanje gidan Anty khadija can Kaduna.baba yace Amman dai ba dadewa zakiyi ba.Yaya Maryam tace baba ba dadewa zanyi ba,kwana uku kawai zanyi.baba yace toh Allah ya kaimu.ni kuma sai naji haushi nace haba  yaya Maryam INA murna kin dawo kuma zaki tafi ki barni.Yaya maryam tace yi hakuri lubna Ai kwana uku kawai zanyi.

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now