part 10

118 2 0
                                    

Kwanci tashi soyayyar mallam Nasir ta shiga raina wannan tabbas babu karya.gani nake kaman bazan iya rayuwa bashi ba.har Allah Allah nake yazo hira gurina duk da dai ba iya masa hirar nake ba don kunyarsa Dana ke ji.sai dai shi yayi ta mun hirar shima kuma jefi jefi.soyayyar mu dai wata iri ce Wanda ba baki ke furtawa ba zuciya ke furtawa.wallahi har mamakin kaina nake yi domin ban taba zaton zanso da namiji haka ba.INA zaune a daki INA karatun qur'ani a waya sai Hanifa tayi sallama tace anti wai kizo inji mamanmu.sai da nakai aya sannan na mike na nufi Fallon.anti khadija tace auta yau shiru a daki baki fito muyi hira ba.nace wallahi anti karatu nakeyi.tace daman imran ne ya samu aikin soja shine nake son muje Kaduna muyi masa sallama kafin ya tafi training. Nayi murna nace Allah ya Sanya Alkhairi.yanzu yaushe zamu tafi nace gobe in sha Allah idan su Hanifa sun tashi daga makaranta.nace mata to zan hada kayana.tace daman kuma alhaji yace ki kawo takardunki a nema miki nan polytechnic ki fara.idan naje zanyi wa baba bayani don nasan bazai so kiyi karatu cikin garin Kaduna ba zai fiso ki koma Zaria.Allah dai yasa ya yarda,nace amin domin nima nafiso karatun anan Dan kar inyi nisa da masoyina.da daddare mallam Nasir ya iso.na fita waje bayan mun gaisa ne nake shaida masa tafiyar mu ta gobe da kuma batun karatuna.yace babu komai Allah ya bada sa'a ai nima nafi son haka.kalaman soyayya dai babu irin Wanda baya gaya min.ni kuma kullum dada jikuwa nake cikin tsananin sonsa.nima dai na fara addu'ar Allah ya mallaka min mallam.hummm mallam abun sona,mallam abun alfaharina,mallam haske mai yaye duhuna.na shiga kogin son sa ya ilahi ka fitar dani.lubna naji ya kira sunana na firgigit na dago kai muka hada ido sai na sunkuyar da kaina,yace naga kinyi shiru toh bara dai na tafi.mukayi sallama INA shigowa gida bayan minti biyar sai naga sakonsa kamar haka(zuciya tunanin ki,bakina kalamanki,rayuwata hidimanki lubna Allah ya mallaka min ke har abada)sai nayi murmushi na lumshe idanu don dadin sakon.na shiga hada kayana INA dokin zuwa Zaria domin nayi kewar su hajja da babana.In sha Allah kuwa zanje Gidansu hajara domin na zaku in bata labari.ita kadai CE zata fahimci halin Dana ke ciki domin Samira yar son duniya CE.hafsa kuma mun kwana biyu bamu yi waya ba.
Washe gari muka isa Kaduna kaman karfe biyu da rabi na rana,muka tadda hajja zaune a kujera tana karanta arba'una hadith.na ruga na rungumeta su Hanifa ma suka biyo bayana.anti khadija tayi dariya tace lallai lubna baza ki girma ba kin zama dai dai dasu Hanifa,zaku balla hajjan ne.na zame kasa na zauna tare da fadin hajja nayi kewarku wallahi.tace auta nima haka wallahi khadija ta kwace mana ke daga hutun kwana biyu.duk muka SA dariya.nace INA baba ne wai,tace baba na kasuwa. na shiga kicin na debo mana abinci da abun sha,nako ji dadi domin hajja ta dafa mana shinkafa da wake da miyan kifi.miyau na har zuba yake don zakuwar in zauna inci.hajja NATA dariya tace auta Ai don ke na dafa daman.da yamma baba ya iso gida daga kasuwa.muka gaisa yace auta kin gudu kin bar mu.wato kinji dadin Kaduna.nayi dariya nace baba wallahi anti khadija CE ta hana ni dawowa.bayan mun Dan yi hira ne na koma daki na basu wuri domin su zanta da anti khadija.na shiga daki gabana na faduwa domin INA fargaban baba ya hanani karatu a Kaduna. Bayan minti sha biyar sai baba ya kira ni yace mun lubna ance min za'a sama miki boko a Kaduna.kina so koko,nace baba INA so mana.yace toh lubna na yarda da hakan ne domin Alhaji sulaiman ne yayi maganan. Ya batun malamin da aka ce min yana zuwa gurin ki.na sunkuyar da kai bance komai ba.baba yayi ajiyar zuciya yace lubna bawai naki maganar bane amma bana son hakan ya hanaki maida hankali gun karatu.Dan Allah yanda kika yi saukan alqur'ani lafiya haka nake son inga kin gama boko lafiya.nace in sha Allahu baba zanyi kokarin yin hakan

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now