part 7

131 3 0
                                    

Anty khadija da yaran ta guda biyu Hanifa da huzaifa sun ji dadin ganina.Kaduna ta sauya min sosai domin na Dade ban je ba.mijin Anty khadija,Alhaji sulaiman tanko mutum ne mai kirki da kuma kyauta.babban ma'aikacin gwamnati ne a Kaduna.Gidansu kullum da jama'a Masu Neman taimako.INA  zaune bisa  carpet INA cin abincin rana na jiyo wayata tana ruri a cikin daki.na tashi na nufi dakin don ganin mai kiran wayar.murna ya kama ni Dana ga Samira CE ke kirata.na kara a kunne nayi sallama.Samira tace haba lubna an share mutane kwana biyu.nace ba haka bane.wallahi INA Kaduna ne sai SA,tayi yar kara tace da gaske kawas,Ai nima INA Kaduna Nazo gurin kannuwar Mamana domin akwai wata makarantar  koyan girki da ake son inyi.nace amma kuwa nayi murna sosai,kinga zamu dinga ganin juna  kenan.tace in sha Allah.mukayi sallama da alkawarin zatazo wurina.
  Kwanana hudu da isowa Kaduna sai naga wayar mallam Nasir,na dauka muka gaisa sai yayi shiru nima nayi shiru.Jim kadan sai yace min akwai maganan da yake son muyi,das das  das  haka zuciyata ta dinga bugawa,sai nace masa toh INA jinka,yace Ai maganar bata waya bace.in sha Allah zanzo Zaria bayan nan da kwana biyu sai muyi maganar.nace masa toh ni Ai INA Kaduna. Yace Alhamdulillah Ai faduwa tazo dai dai da zama nima INA Kaduna domin anyi min transfer zuwa wata makaranta anan.nace toh babu komai Allah ya kawo ka.na kwanta kan gado na yarda  wayar kusa dani INA tunanin mai mallam Nasir zai CE min.hummm Allah yasa dai lafiya.bayan minti biyar  sai ga huzaifa yace min mamanmu na kiranki.na fita falo na sameta ta zuzzuba mana kwadon zogale a plate.tace mun auta zo muci kwado mana.nace gaskiya nifa sugar zan zuba a nawa.tayi dariya tace toh shazumami debo ki duba.INA idar da sallar magariba sai naji sako  ya shigo wayata.na duba sai naga mallam Nasir ya rubuto min assalamu alaykum lubna.don Allah ki turo min adireshin Inda kike.na rubuta na tura masa.bayan sallar isha'i sai sako ya shigo wayata sai na duba naga mallam Nasir ya rubuto cewa yana kofar gidan.na tashi na saka gyale na na Dan fesa turare,daman ni kwalliya bata dameni ba,ballantana ma ban ga dalilin da zanyi kwalliya don mallam Nasir yazo ba.wallahi Dana fita sai da gaba na ya fadi.domin irin kyan  da mallam Nasir yayi ba a magana.sanye yake da jeans trouser da kuma farar Riga.agogonsa baki gashi  ya sako bakin gilashi.yana hango ni sai ya zare gilashin daga fuskarsa.fuskarsa dai babu yabo babu fallasa domin shi daman ba mai yawan dariya bane.ya jingina da Babur dinsa Wanda tasha wanki Fes.yace min lubna nasan zakiyi mamakin ganina a gurin ki ko.toh ba wani Abu bane ya kawo ni illa in bayyana miki sonki  dake  zuciyata.saura  kadan in zube kasa don tashin hankali,na dai daure na gyara tsayuwata na sunkuyar da kaina.yace kinyi shiru baki CE komai ba.um kawai nace masa.yace Tun kina makaranta zuciyata ta kamu da son ki,kawai dai naki  yi miki magana ne domin kada hankalinki ya rabu biyu.na Dada sunkuyar da kaina  kasa.yace min lubna zuciyata bata taba son wata mace in bake ba,wallahi na kasa sukuni sai SA dai nace bari in bayyana miki meke cikin raina.mamaki ya kamani dajin kalamansa domin ban taba zata zai iya furta irin wannan kalaman ba.na runtse ido na don kunya domin ji nake kaman in bace  daga gurin.daya lura da haka sai yace toh lubna ni zan wuce naga dare yayi ko.nace to sai da safe.nayi wuf na shige gida domin daman na kosa in bar gurin.ya Allah na me kunne na ya jiye min ne wai.

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now