part 15

91 4 0
                                    

Rayuwar auren mu dadi da habibina.komai muna yinsa cikin ruwan sanyi.bayan kwana uku ne muka nufi gidan iyayensa.muka je gurin mahaifiyarsa hajiya Halima,Matan akwai ta da kirki.ta amshe ni hannu biyu.sai kuma kannensa Maryam da kuma ummi  Wanda na lura kwata kwata baya  sakin musu fuska.na kula ma tsoronsa suke ji.akwai kaninsa dake makarantar kwana a bauci.babbansa mallam abubakar Allah yayi masa rasuwa shekara takwas da suka wuce.yan gidan sunyi murna da ganina Tun balle ma maryam da take sa'a  ta.muka shiga daki sukayi ta Jana da hira.
       Bayan sati daya na koma makaranta habibi kuma ya koma Aiki.da daddare bayan sati biyu sai zahra tayi min waya tace zasu zo gidana gobe.nayi ta murna na gayawa habibi na dake gefe na a zaune,sai yace shifa bai yadda da haka ba.na kalle shi nace ban gane ba,sai yace shifa  baya son mutane suna zuwa masa gida.nayi shiru bance komai ba na koma na kwanta.na lura habibi ko makotan mu da suka shigo baya bari na shiga gurin su.amma sai ban bama abun mahimmanci ba don na zata amarci ne.washe gari da su zahra suka bugo waya sai nayi musu karya nace Ai zamuje gaida wata yar  uwansu habibi a asibiti.INA zaune akan kujera naji wayata na ruri na duba naga Yaya Imran ne.na dauka da murnata muka gaisa.bayan mun gaisa ne yake gaya mun an tura su yaki kasar somalia.ban ji dadi ba amma nasan yanayin  aikinsa nace masa Allah ya bada sa'a  yasa kuma dawo dashi lafiya.hankalina ya tashi Dana natsu na tuna yaki fa aka tura shi anan na fara kuka na kuma kiransa a waya,yayi ta bani hakuri yace haba auta in sha Allah zan dawo lafiya.
      Kwanci tashi yau auren mu wata biyu da habibina,yau dai nace masa gaskiya ya kamata muje Gidansu Anty khadija sai yace mun gaskiya shi baza shi ba.nace masa tunda mukayi aure fa bamu je  ba.sai yace toh sai mene,nan take mamaki ya kamani kawai sai kallonsa nakeyi.can dare dai sai yace min in tashi muje.da Sauri Sauri na shirya domin nayi kewar Hanifa da huzaifa.muna isa na Tatar dasu basuyi bacci ba duk suka taho suka rungume ni.anti khadija ko kallona kawai takeyi tace auta sai yau kuka zo duba mu.nayi murmushi nace wallahi anti makaranta ne kuma idan na dawo na gaji.muka gaisa muka shiga hira.tace min yaushe zakije Zaria ki gaida su hajja.nace mata sai nayi ma Nasir magana.tace toh babu damuwa.bayan minti ashirin nasir yayi min waya in fito mu tafi nace masa ya shigo su gaisa da anti khadija, wai shifa bazai shigo ba kawai inzo mu tafi.hakanan jiki babu kwari nayi mata sallama tace min toh Nasir din bazai shigo bane.nace mata Ai yace dare yayi zamu dawo da rana in sha Allah sai Ku gaisa,tace toh babu komai Allah ya kaimu.da muka isa gida nayi masa maganan mai yisa bai shiga ya gaida anti khadija ba kawai sai ya Daka min tsawa wai Ai bani zan gaya masa abunda zai yi ba.na shiga daki na kwanta  a gado na fara kuka sai gashi ya biyo ni yana bani hakuri.A kullum sai dai muyi waya da hajja domin fafur Nasir ya hana ni zuwa Zaria. Gidan anti khadija kuwa tunda mukaje da daddaren nan ban kara zuwa ba.gashi ya hanani shiga makota.Tun makotan suma suna shigowa har suka gaji suka daina.daga makaranta sai gida saboda yace in har na biya wani gurin bai yafe  ba.A hankali mallam kullum kara canza hali yake yi.A wannan halinne ma bayan wata shida na samu ciki.cikin na bani wuya  sosai.idan na fara amai sai nasir ya fara min masifa wai INA damunsa shifa  baya son amai.a nan ne ma ya samu damar hanani zuwa makaranta wai saboda cikina,wai in bari in Dan ji sauki.muna zaman haka ne ya fara cewa in daka  masa sakwara kullum gashi da kyar nake tashi.Awo kawai nasir ke barina inje.anti khadija tazo dubani nasir da kyar ya gaishe ta yasa kai kawai ya fita abinsa.rannar sai sha biyu da rabi  na dare ya shigo gidan.da nayi masa magana kawai sai naji saukan mari a kumatuna,na rike fuska da tafin hannuna kawai na saka ihu na zube kasa,anan ya tafi ya barni ina kuka mai tsananin takaici.ya shige daki yayi kwanciyarsa.haka na kwana INA kuka ranar kaman zuciyata zai fita domin ban taba tunanin nasir zai iya daga hannu ya mare  ni ba.hajara tayi min zuwan bazata daga Zaria.kallo  kawai take bina dashi domin ta lura duk na canza na lalace.tace kawalli me yake damunki ne haka ,sai kawai nace mata ciki ne ke bani wuya.muna cikin hira gabana na fadi domin nasan nasir bazai so ya ganta gidan  ba,domin ko yan uwansa ma ba kasafai yake bari suzo  ba.karfe biyar  na yamma ya dawo gida Ai kuwa yana ganinta ya hade rai ya wuce ko kallonta bai yi ba ya shiga daki.ta Bini da kallo kawai sai na sunkuyar da kai na.Jim kadan ya kwala min kira na bishi dakin. Yace min kiyi maza ki Fada mata ta bar min gida kafin ranku ya baci.kawai na fita daga dakin na rasa yadda zanyi ince wa hajara ta tafi.na koma falo na zauna INA ta kame  kame,data ga haka kawai sai tace kawalli ni zan tafi daman na Fada wa kanwar babana  gidan ta zan kwana.mukayi sallama dukkanmu jiki a mace.da daddare mallam ya fisgo ni gado ya kusance ni irin kusantar da bai kamata kayiwa mai Sabon ciki ba.Ai kuwa yana sake ni sai amai kaman hanjin cikina zasu fito.bayan na gama aman  ne na dawo na Dan kwanta  yace min in tashi inyi masa tuwon shikafa miyan kubewa.wayyo Allah na na shiga uku INA zansa kaina.na nufi kicin jiri na diba na.na daura girkin yayin da wasu hawaye Masu zafi suka zubo min.

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now