part 22

87 2 0
                                    

Arziki ya samu domin yanzu nasir ya sayi mota yana kuma Neman gida domin ya siya mana.ya saman mana gida a unguwar rimi.ya dauke ni mukaje naga gidan,gidan yana nan Dan madaidai ci daki uku ne da falo sai kuma wani daki da katon falo da daki daya mai ban daki aciki.gida yayi kyau Alhamdulillah. Mun tare a gidan kowa NATA yi mana murna.rayuwa ta dawo sabo komai ya canza arziki ya samu.ana cikin haka ne na samu wani cikin lokacin Bilkisu shekaranta  biyu.a hankali nasir ya fara canza halinsa ya koma dabi'unsa Nada.baya dawowa gida da wuri ga yawan Fada komai nayi ban iya ba.wata sa'in ma idan ya dawo Aiki sai yaki yimin magana sai dai yayi ta wasa da Bilkisu.inyi ta tambayarsa abunda yake damunsa amma yayi banza dani.abun na daure min kai,ana zaman lafiya kuma ya tsiro da wani sabon Abu.watarana ya dawo gida yace bashi da lafiya na dauke shi na kaishi asibiti likita ya duba shi yace sai an kwantar dashi domin sai anyi masa wasu yan gwaje gwaje.muna zaune sai jikinsa ya kara yin zafi sai akayi masa allurar bacci ya samu bacci,ni kuma sai nace bari inje gida domin in hado abinci da sauran abubuwa kafin ya tashi.na tafi gida na dafo mai faten dankali da koda a ciki,nayi shi ruwa ruwa sannan na hada mai fruit salad.na shiga bayi nayi wanka sannan na wuce na kai Bilkisu gidan anti khadija domin nasan yau a asibiti zan kwana dashi.INA komawa asibiti na shiga dakin sai naga wata mace zaune kusa dashi tana bashi abinci shi kuma ya Dan jingina da pillow a bayansa,kaina ya daure domin ban taba ganinta ba.na dai daure nayi sallama na shiga dukkansu babu Wanda ya amsa min.nace masa nasir wacece wannan sai yace min INA ruwanki,nace ya zaka CE INA ruwana bayan naga wata mace na baka abinci a baki wadda ban Santa ba ban kuma San Inda ta fito ba,ya fara min masifa sai ita kuma ta fara bashi hakuri da hausanta da bai nuna sosai ba.nan nagane bama bahaushiya bace.yace min in dauki abinci na in tafi dashi Bilkisu zata kula dashi.na kalle shi cikin mamaki nace masa nasir matanka kake kora kan wata yar iska.yayi min ihu wai in fita bai son ganina,a fusace na fita zuciyata na zafi kaman an kunna wuta a ciki.na wuce gida ko biyawa in dauko Bilkisu banyi ba domin bana so anti khadija ta tambaye ni abunda yasa ban kwana a asibiti ba.nayi mata waya nace mata kar Suzo domin anyi masa allurar bacci.INA shiga gida na Fada daki na rusa wani irin kuka cikin tashin hankali.ni lubna mai zan gani haka wannan wace irin rayuwace daga wannan sai wannan INA zan saka kaina .sakayyar da Nasir zai yimin kenan.amma babu komai.ranar banyi bacci ba kwana nayi INA kuka mai tsananin takaici,daga bisani na dauro alwala na shiga yin nafila INA rokon Allah ya yaye min wannan bakin ciki.sai karfe shida na Dan samu baccin awa biyu.takwas na farka da safe na kuma hada breakfast na nufi asibiti gabana na fadi domin bansan mai zan Tatar ba wannan karon.na shiga da sallamata sai naga nasir a kwance shi kadai,na gaishe shi,ya amsa tare da bata fuska.nace in zuba maka abinci kaci yace min in zuba masa,na mike na zuba masa a plate na fara bashi a baki yana ci yana hada rai.a haka muka wuni yana ta cin magani.su anti khadija suka zo suka dubashi suka kuma tafiya da Bilkisu. Su mamanshi duk sunzo sun tafi aka barni daga ni sai shi.misalin karfe takwas na dare sai naga ya dauki wayarsa ya danna yasa a kunne,sai naji yace kizo,sai kuma ya aje wayar.na kalle shi ban dai CE masa komai ba.bayan minti talatin sai ga macen nan mai suna Bilkisu ta kuma zuwa,ta shigo tana cin cingam tana yatsina fuska.tana iso wa tace(I am here Darling) yace mata to sannu da zuwa,tace yauwa da wani hausanta mai kama Dana yarbawa.tace ya jikin yace lafiya.sai ya kalle ni yace toh sai da safe ko,kawai sai na mike na fita jiki babu kwari na shiga Mota na zauna na kifa kai kan sitiyarin mota wani irin azababben kuka yazo min tare da bakin ciki. Naji duniyar tayi min baki babu sauran haske a cikin ta.hawayena suka ci gaba da kwarara yayin da na tada motan  na fita daga asibitin.da nakai gida na yarda jakata a kan gado na kifa kaina kan pillow na cigaba da kuka mai tsanani.har tsakar dare INA kuka sannan nayi alwala Nazo nayi sallar nafila na zauna akan dadduma INA kuka mai tsanani INA gayawa Allah.nayi kuka na kuma yi addu'a har gari ya waye.da safe naji kaman kar in koma asibitin sai kuma wata zuciya tace min inje domin kar wasu suzo suga bana nan ayi min wani Sharrin daban.nayi wanka na dafa abun breakfast na tafi dashi.na shiga asibitin banga wannan macen mai suna Bilkisu ba.sai nace wato raba mana jinyar yakeyi.ni inyi da rana don kar mutane su gane ita kuma tazo da daddare Dan munafinci da kuma tsabar cinmutunci da mugunta.na kuma bashi abinci yaci.a haka dai akayi kwana hudu a asibitin ni INA zuwa da safe ita kuma tazo da daddare bayan mutane sun watse.a yan kwanakin nan kullum cikin kuka nake har nafi mai ciwon ramewa ga kuma ciki.bayan kwana hudu aka sallame mu Ashe wai ulcer CE ke damunsa da kuma malaria.

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now