part 11

85 2 0
                                    

Sammako nayi zuwa gidan su hajara domin na kosa in ganta mu tattauna.na shiga da sallamata Ai kuwa sai gata a tsakar gida tana wankewanke Ai kuwa da ganina ta saki kofin robar hannunta ta nufo ni da gudu muka rungume juna.tace yaushe a garin kawalli,nace jiya muka shigo da rana.amma kuwa naji dadin ganinki ta Fada lokacin da take Jan hannuna mu shiga ciki.muka shiga falo na gaida mamansu.mamansu tace wazan gani haka lubna mutanen Kaduna.na tsuguna na gaida ta.muka shiga daki hajara tace bari in kawo miki abinci nace mata Ai ban Dade da karyawa ba,tace toh shi kenan kawalli Yaya kwana biyu.nace lafiya Alhamdulillah. Na kwanta kan gado na lumshe ido nace kawalli na shiga sabon rayuwa Wanda bana ji bana gani.na Fada kogin soyayyar wani Wanda a halin yanzu gani nake yi kaman bazan iya rayuwa ba tare dashi ba.hajara ta zaro ido tace kai kawalli waye wannan kuwa ya saka ki zuba haka lallai ya cire tuta kam.nace mata ba wani bane illah mallam Nasir.kawai sai ta saka dariya tace daman nasan haka zai faru Tun Dana ga take takensa a makaranta. Ta gyara zama tace amma lubna kinyi dace domin kuwa kinsan mallam mutumin kirki ne nace mata nasan hakan,tace amma kuma abunda nake tsoro shine kinga shi fa bai fiye fara'a da son mutane ba ke kuma akwai ki da fara'a ga son jama'a toh Yaya za ayi kenan.nayi murmushi nace in sha Allah hajara zan koya masa hakan in har ya kasance mijina duk muka sa dariya muka tafa.anan ne nake gaya mata batun karatun a Kaduna.hajara ta shiga damuwa domin zatayi kewana,Dan dagani har ita bamu da kawar data wuce junanmu.daga baya dai tayi mun Allah ya Sanya Alkhairi. Ta dauko min sabuwar wayarta ta nuna min tace min baba ya siyo mata waya.nayi mata murna domin yanzu mun samu abin magana da muna komai Nisan dake tsakaninmu.
Kwanan mu hudu a Zaria muka dawo Kaduna.daman ko na kosa inga Rabin raina don tunda nake Zaria muke waya kowa na bayyana kewar Dan uwansa.ana idar da isha'i kuwa sai gashi.yau kam hijjabi na zura na fita abunna,na same shi a kujerar dake haraban gidan.na tsuguna muka gaisa sannan na samu dayan kujeran na zauna.yace ya kika samu mutane Zaria,nace lafiya hajara ma tace in gaishe ka sai yayi dariya yace anje gurin kawalli kenan.ya juyo da kujerarsa ya kalle ni da kyau yace lubna baiwar Allah,shin lubna kina sona kuwa.nayi shiru na sunkuyar da kaina.mallam yace toh nidai da wayau ana korata ana nuna min ba a sona.nayi Sauri na dago kai nace haba mallam wallahi ba haka bane.yace toh Yaya ne sai kuma nayi shiru.yace toh Indai ana sona mataki na farko a daina kira na da mallam,a nemi suna irin na masoya a SA min.nayi murmushi na gyada kaina.bayan na shigo gida da yan mintuna sai naga sakonsa ya shigo wayana. Na duba sai naga sako kamar haka(bazan iya rayuwa baki ba,Ya Allah INA rokonka ka mallaka min Rabin raina).nayi murmushi na lumshe sai nima na rubuta masa (amin habibi na).a Daren nan kwana nayi INA nafila INA rokon Allah ya dauwamar da soyayyar mu.

rayuwa juyi juyiWhere stories live. Discover now