FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

292 0 0
                                    

[4/6/2017. 10:30 am]
     [9/9/1438 A.H]


® *_Eloquence Writers Association



*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH



Writing by ✍🏽
     Basira Sabo Nadabo



*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai




Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:


*Sallar Farillar Da Mai Kasaru bazai Gajarta Ba Itace Sallar Asuba Da Magriba, Amma Duk Sallar Da Ake Raka'a Hudu Shine Mai Kasaru Zai Gajarta Ta. Wallahu Ta'ala A'alam




*ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE

Bayan Mun Karanta Ayatul-Kursi, Sai Mu Karanta Surorin Nan:

Ana karanta waɗannan surorin (kowacce daga ciki har zuwa karshenta) bayan sallar Asuba da bayan sallar Magariba sau uku. *Abu Dawud 4/322, da Tirmizi 5/567, Duba Sahih Tirmizi 3/182.*

*Suratun-Nas (Mankind)

_Qul a'udhu birabbin-Naas(i) zuwa karshe.

*Suratul-Falaq (The Daybreak)

_Qul a'udhu bi Rabbil falaq(i)

*Suratul-Ikhlas (The Purity)

_Qul Huwallahu Ahad

Wanda ya karanta ta yayin da ya wayi gari za'a a tsare shi daga aljanu har ya kai maraice. Wanda kuma ya karanta ta da yamma za'a tsare shi daga aljanu har ya wayi gari.

Kuma wanda ya karanta su safe da yamma sau uku zasu isar masa daga dukkan komai.

_Asbahaa wa'asbahal mulku lillaahi walhamdulillahi, laa'ilaaha'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa huwa'alaa kulli shay'in Qadeer. Rabbi'as'aluka khayra maa fee haazal-yawmi wa khayra maa baa'dahu wa'a'uuzu bika min sharri maa ba'dahu, Rabbi a'uuzu bika minal-kasali, wa suu'il-kibari,  Rabbi a'uuzu bika min'azaabin fin-naari wa'azaabin fill-qabri.

Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH, mulki ya tabbata gare Shi, kuma yabo ya tabbata gare Shi, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Ya Ubangijina! Ina rokonka alherin da ke cikin wannan rana, da alherin dake bayanta. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin dake cikin wannan rana, da sharrin dake bayanta. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga lalaci, da mummunan tsufa. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga azaba a cikin wuta, da kuma azaba a cikin kabari. *Muslim 4/2088.

*Idan Kuma Maraicene Sai Yace:

_Amsainaa wa amsal lillaahi Rabbil aalamiina, Allahumainni as'aluka kahira hazihil lailati, fat'hahaa, wa nasarahaa, wanuurahaawa barakadahaa, wa hudaahaa, wa hudaahaa, wa hudaahaa, wa baraktahaa, wa hudaahaa, wa'a'uuzu bika min sharri maa fiiha wa sharri maa ba'adahaa...

Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga maraice yana mai tabbata ga Allah. Ya Ubangiji! Ina rokonka alherin dake cikin wannan dare da alherin dake bayansa kuma ina neman tsarinka daga sharrin dake cikin wannan dare da sharrin dake bayansa *Muslim 4/2088.*

_Allahumma bika asbahna wabika amsaina wabika nahya wabika namuutu wa-ilaikaal-nushuur.

Ya Allah! Da Ikonka ne muka wayi gari, kuma da Ikonka ne muka shiga maraice, kuma da Ikonka ne muke rayuwa, kuma da Ikonka ne muke mutuwa, kuma izuwa gare Ka ne matattara take.  *Tirmizi 5/466, duba: Sahih Tirmizi 3/142.*

*Da Yamma Kuma Sai Yace:

_Allahumma bika amsaina wabika asbahna wabika nahya namuutu, wa-ilaikal masir(u).

Ya Allah! Da Ikonka ne muka shiga maraice, kuma da Ikonka ne muka wayi gari, kuma da Ikonka ne muke rayuwa, kuma da Ikonka ne muke mutuwa, kuma izuwa gare Ka ne makoma take. *Tirmizi 5/466,duba: Sahih Tirmizi 3/142.*


*Prayer For Steadfastness In Faith

*Rabbana afrigh 'alainaa sabran wa tawaffana muslimiin(a)

_Our Lord! Pour out on us patience and steadfastness and make us die as Muslims (men who bow to Your will). *Q7:126*

*Prayer For Victory Over Opponents

*Rabbana iftah bainanaa wa baina qauminaa bil-haqqi wa Anta Khairul-Faatihiin(a).

_Our Lord! Decide between us and our people in truth for You are the Best to decide. *Q7:89.*


Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Wata Sura Ce Tayi Sanadiyyar Musuluntar Sayyadina Umar Bin Khatab (Rahmatullah)?


Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah



Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

    Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now