FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

334 0 0
                                    

(13/6/2017. 4:21 Am)
  (18/9/1438 A.H)




® *_Eloquence Writers Association_




*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH*



Writing by ✍🏽
   Basira Sabo Nadabo






*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim*

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai_



Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*Daren Lailatul Kadar Yafi Wattanni Dubu. Wallahu Ta'ala A'alam*




*FALALAR TASBIHI, DA GODIYA GA ALLAH, DA YIN LA'ILAAHA ILALLAHU DA YIN KABBARA*



Daga Abu Musa Al-Ash'ari, ALLAH ya yarda dashi ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce mini: 'Ya Abdullah bin K'ais! Ba na shiryar da kai ba zuwa ga wata taska daga cikin taskokin aljanna ba? Sai nace shiryar da Ni' Sai ya ce: 'Ka ce:

_La hawla wala quwwata illa billah._

Babu dabara babu karfi sai da ALLAH. *Bukhari da Fat'hul Bari 11/213 da Muslim 1/2076.*



Daga Samura bin Jundub, ALLAH ya yarda dashi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Mafi soyuwar zance a wajen ALLAH shine:

_Subhanal-lah, walhandu'lillah, wala ilaha illal-lah, wallahu Akbar_

Tsarki ya tabbata ga ALLAH, kuma yabo ya tabbata ga ALLAH, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH, kuma ALLAH ne Mafi Girma. *Muslim 3/1685.*


Sa'ad bin Abi Wakkas, Allah ya yarda dashi ya ce: 'Wani balaraben kauye yazo wajen Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai yace: koya min wadansu kalmomi da zan rika faďa, Sai Manzon Allah ya ce: Ka ce:

_La'ilaha illal-lah wahdahu laa shariika lah, Allahu akbaru kabiira, walhamdu lillahi kadhira, subhanal-lahi rabbil-alamin, la hawla wala quwwata illa billahil-aziiziil-hakiim. Allahumagh-fir lii, warhamnii, wahdinii, warzuqnii._

Babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH; babu abokin tarayya a gare Shi. ALLAH ne Mafi girman, Ina girmama Shi,  girmamawa. Kuma godiya ta tabbata ga ALLAH da Kamar. Tsarki ya tabbata ga ALLAH. Ubangijin talikai. Babu dabara babu karfi sai da ALLAH. Mabuwayi Mai hikima.  *Muslim 4/2072 da Abu Dawud 1/220.*

...... Sai mutumin yace: wadannan na Ubangijina ne, ni kuma nawa fa? Sai Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: Ka ce:

_Allahummagh-fir lii, warhamnii, wahdinii, warzuqnii._

Ya Allah! Ka yi mini gafara, ka ji Kai na, Ka shirye ni, Ka azurta ni. *Muslim 4/2072 da Abu Dawud 1/220.*


Tarik ibn Ashyam Al-Ashja'i Allah ya yarda dashi, ya ce: Idan mutum ya musulunta, sai Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koya masa sallah, sannan ya umarce shi ya rika addu'a da wadannan kalmomin:

_Allahummagh-fir lii, warhamnii, wahdinii, warzuqnii._

Ya Allah! Ka yi mini gafara, Ka ji Kai na, Ka shirye ni, Ka amintar dani daga bala'i, Ka azurta ni. *Muslim 4/2073.*

Jabir ibn Abdullah, ALLAH ya yarda dashi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Mafificiyar addu'a Itace fadin:

_Alhamdulillah_

Dukkan yabo ya tabbata ga ALLAH. *Tirmizi 5/462, Ibn Majah 2/1249 da Hakim 1/503, kuma ya inganta shi, Zahabi kuma yayi muwafaka dashi. Duba: Sahihul Jami 1/362.*

..... Kuma mafificin zikiri shi ne fadin:

_LA'ILAAHA ILALLAH_

Babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH. *Tirmizi 5/462, Ibn Majah 2/1249 da Hakim 1/503, kuma ya inganta shi, Zahabi kuma yayi muwafaka dashi. Duba: Sahihul Jami 1/362*


Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Ayyuka nagargaru masu wanzuwa sune fadin:

_Subhanal-lahi, Walhamdulillahi, Wala'ilaha illal-lah, Wallahu Akbar, Wala hawla wala quwwata illa billahi._

Tsarki ya tabbata ga ALLAH, kuma yabo ya tabbata ga ALLAH, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH, kuma ALLAH ne Mafi girma, kuma babu dabara babu karfi sai da ALLAH. *Ahmad hadisi na 513 da isnadi mai inganci. Duba Majma'ul Zuwa'id 1/297. Hafiz Ibn Hajar yace Nasa'i ya ruwaito shi, kuma Ibn Hibban da Hakim sun inganta shi.*






Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Lissafo Sunayen Annabawa 10 Da Aka Lissafo A Al'Qur'Ani Mai Girma*



Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah*

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah


Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

     Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Onde histórias criam vida. Descubra agora