FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

55 0 0
                                    

(18/6/2017. 5:45. A.M)
    (24/9/1438. A.H)







® Eloquence Writers Association






FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH






Writing by ✍🏽
     Basira Sabo Nadabo











Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai





Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:


*Bishiyar Da Allah Ya Fara Halitta A Bishiyoyin Duniya Shine: _Bishiyar Zaitun_ Wallahu Ta'ala A'alam




*YAĎa SALLAMA A CIKIN AL'UMMA


Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Baza ku shiga aljanna ba sai kunyi imani, kuma baza kuyi imani ba sai kunso juna. Shin ba na nuna muku wani abu da in kunyi shi zaku so juna ba?  Ku ya ɗa sallama a tsakanin ku *Muslim 1/74 da wasu malamai.


Ammar, ALLAH ya yarda dashi, ya ce: 'Abubuwa uku, wanda duk ya haɗa su, ya haɗa imani: mutum yayi adalci ga kansa, da yaɗa gaisuwar sallama a cikin al'umma, da yin kyauta a cikin rashin wadata. *Bukhari da Fat'hul Bari 1/82. Ya ruwaito shi daga maganar Ammar, ba tare da ya ambaci isnadinsa ba.



'''Daga Abdullah bin Umar, Allah ya yarda dashi, ya ce: 'Wani mutum ya tambayi Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: wane ne a cikin musulunci yafi alheri? Sai ya ce: 'ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba. *Bukhari da Fat'hul Bari 1/55 da Muslim 1/65.



Allah ka bamu ikon yaɗa sallama a tsakanin mu, ALLAH ka kara mana ikon bin umurnin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Amin Ya Allah.

Don Allah duk wanda na yiwa laifi da sani na da rashin sani na Don Allah ku yafe min, nima duk wanda yayi min laifi da sanin sa da rashin sanin sa nima na yafe muku, ALLAH ka yafe mana baki ɗaya. Amin Ya Allah



_Ya ALLAH munyi tawassali da sunayen ka, Ya Allah Don Tsarkin Mulkinka, Don Darajan Cikakkiyar Kalmarka, Don Hasken Al-kibilarka Ya Allah, Don Soyayyar dake tsakanin ka da Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,  ALLAH kayi mana rahama ka yafe mana, ka kara mana lafiya wanda basu da lafiya Allah ka basu lafiya mu da muke dashi Ya Allah ka kara mana lafiya, iyayenmu da duk wanda suka rigamu gidan gaskiya tun daga zamanin Annabi Adam har zuwa yau Ya Allah Don darajar Kursiyyunka Allah kayi musu Rahama, mu kuma in tamu tazo kasa mu cika da imani. Amin Ya Allah



*Ya Allah kasa mu dace da Lailatul Qadar Don Tsarkin Sunayen Ka Ya ALLAH

Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Shekarun Annabi Isa (A.S) Nawa Ne A Lokacin Da ALLAH Ya Dauke Shi Zuwa Sama?


Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan Number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah

May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah


Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

   Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Donde viven las historias. Descúbrelo ahora