FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

85 0 0
                                    

(5/6/2017. 1:47 pм)
(10/9/1438 A͟.H͟)


_A͟loqυence wrιтerѕ A͟ѕѕocιaтιon



*F͟A͟L͟A͟L͟A͟R͟ Z͟I͟K͟I͟R͟I͟ D͟A͟ T͟A͟S͟B͟I͟H͟I͟ D͟A͟ G͟O͟D͟I͟Y͟A͟ G͟A͟ A͟L͟L͟A͟H͟



wrιтιng вy ✍🏽
B͎a͎s͎i͎r͎a͎ S͎a͎b͎o͎ N͎a͎d͎a͎b͎o͎

*B͎i͎s͎m͎i͎l͎l͎a͎h͎i͎r͎-R͎a͎h͎m͎a͎n͎i͎r͎-R͎a͎h͎i͎i͎m͎


_D͎a͎ S͎u͎n͎a͎n͎ A͎L͎L͎A͎H͎, M͎a͎i͎ R͎a͎h͎a͎m͎a͎ M͎a͎i͎ J͎i͎n͎ K͎a͎i͎

*_Ya ALLAH na daga hannu na a gare ka, ni kaskantacciyar baiwa ce a gare ka Ya Allah, Ka biyawa Abeeda TuahTah bukatun ta na alkhairi, Ya Ubangijina Ka yaye mata dukkan wani abu da ya kasance baki a tare da ita alfarmar wannan watan mai albarka, Ya Ubangijina ka yaulata farin ciki a zuciyar ta albarkacin watan Ramadhana Amin Ya Allah. Ina mugun sonki a koda yaushe Yar Uwa ta

Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:


*Suratul ɗaha itace tayi Sanadiyyar Musuluntar Sayyadina Umar Bin Khatab (Rahmatullah). Wallahu A'alam



*ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE


_Allahumma anta Rabbi laa ilaaha illa anta, khallaqtani, wa'anaa abduka wa'anaa ala ahdika wa waadika mastaɗa'atu auudzu bika min sharri maa sana'atu abuu'u laka binimatika alayya wa abuu'u bidhanbi, faghfirlii fa innahu laa yaghfiru-dhunuba illa anta.

Ya ALLAH! Kai ne Ubangijina; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, kuma ni bawanka ne; kuma ina kan alkawarin da nayi maka (na kadaitaka da bauta) da kuma alkawarin da Ka yi miny(na shigar da wanda bai yi shirka da Kai ba gidan aljanna) gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina tabbatar da ni'imarka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; Ka gafarta mini, domin ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai. *Bukhari 7/150.*

Wanda ya karanta wannan addu'a da maraice yana mai imani da ita, idan ya mutu a cikin daren zai shiga aljanna; hakanan ma idan ya karanta ta da safe. In Shaa Allah


_Allahumma Inniy Asbahtu Ushihiduka, wa'ush'hidu hamalata arshike wama la'ikatika, wajamiy'a kalkika, annaka antallahu la ilaha illa anta wahdaka la shariyka laka, wa'anna Muhammadan abduka warasuwluka. Sau hudu

Ya Allah! Ni na wani gari ina shaidawa gare Ka, kuma ina shaidawa ga (mala'iku) masu daukan Al'arshinka, da mala'ikunka da dukkan halittarka cewa Kai, Kai ne ALLAH, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai kadai, babu abokin tarayya a gare Ka, kuma Muhammdu Bawanka ne kuma Manzonka ne (Sau hudu). *Abu Dawud 4/317, Bukhari ya ruwaito shi a cikin Adabul Mufrad, hadisi mai lamba 1201; da Al-Nasa'i a cikin Amalul Yaum Wal laila, hadisi mai lamba 9, da Ibn As-Sunni, hadisi mai lamba 70. Shaykh Ibn Baz yace isnadin Abu Dawud da Al-Nasa'i hasan ne, duba: Tuhfahtul Akhyar shafi 23

Wanda ya karanta kamar yadda ake ce Allah zai 'yanta shi daga wuta. Wallahu Ta'ala A'alam

*_Da maraice maimakon yace: asbahna; sai yace amsaina, na shiga maraice.

_Allahumma ma asbaha bii min ni'imatin, aw bi-ahadin min khalqik, faminka wahdaka la shariika lak, falakal-hamdu walakash-shukr


Ya Allah! Dukkan abin da ya wayi gari a gare ni na ni'ima, ko ga wani daga halittarka, to daga gare Ka ne, Kai kadai, babu abokin tarayya a gare Ka; kuma yabo ya tabbata a gare Ka kadai, kuma godiya ta tabbata a gare kadai. *Abu Dawud 4/318 da Al-Nasa'i a cikin Amalul Yaum Wal Laila hadisi mai lamba 7, da Ibn As-Sunni, hadisi mai lamba 41; da Ibn Hibban kamar yadda yazo cikin Mawarid, hadisi mai lamba 2361. Shaykh Ibn Baz yace hadisi ne hasan, duba [Tuhfahtul Akhyar ], Shafi 27.

Wanda ya fade ta da safe to wannan ya cika godiyar ranarsa, wanda kuma ya faďa da yamma ya cika godiyar darensa. Wallahu Ta'ala A'alam.



*Prayer For Wives And Children

*Rabbana hablanaa min 'azwaajinaa wa dhurriyyaatina qurrata a'yunin waj'alnaa lil-muttaqina imaamaa.

_Our Lord! Grant unto us wives and offspring who will be the comfort of our eyes and give us (the grace) to lead the righteous. *Q25:74*



Ga Tambayar Mu Ta Yau:


*Wanene Amirur Mu'uminin Na Farko Cikin Sahabbai?

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah


_May gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah


Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang