3: Tarbiyya

2.3K 286 284
                                    

Assalamu Alaikum warahmatullah

Da fatan kuna lafiya. Exams time table is out, 2 more posts before the date Insha'Allah. Se kuma 13th December da zan gama Insha'Allah from then daily updates if my thesis permit. 

Don't forget to vote, comment  and share 

أحبكم يجري في دمي 😘😍💞💕

Bin ta su ka yi da kallo har ta ɓace ma ganin su. Nan su ka ji karan tashin motar ta kirar vibe, sannan Alhaji Yahuza ya maida kallon shi ga matansa

"Duk wata wacce ta sake goranta ma ɗaya daga cikin ya'ya na gorin aure toh a bakin aurenta da ni, ko da kuwa ita ta haifi yar, ko da kuwa a bayan ido na ne, in ta rufe ta kwashi zunubin zaman zina ita kaɗai.

Rawa ake ma Allah ya sa mutum yayi aure? Na tabbata da rawa ake da dukkanku na gidajen iyayenku ba aure. Kun fi ta son taga tayi aure ne? Ba Za ku sa ma yata damuwa ba,  in ba zaku bi ta da addu'a da fatan alkhairi ba toh ku kyale min ita" yace rai a ɓace

"Amma Alhaji haka za'a sa mata ido tana haɗa kafadu da mu" mahaifiyarta tace tana mai jin haushin yanda yake ɗaure ba karya kugu

"A'a, sa ta zamu yi a gaba ta bi duk samari da mazan aure da suka bata sha'awa tana rokon su arzikin zuwa neman aurenta. Ko so kuke in ɗauki hoton ta ina yawo masallaci mai so ya zo ya ɗauka.

Ko yau ta rasu bata ci baya ba, ba haka aka so ba amma kuma alkhairi ne gareta don ina da tabbacin ba ta taɓa zina ba. Wasu ma sun haifa sun yar an kuma aure su balle nawa kintsatssa" Ya ce yana mikewa haɗe da kakkabe riga

"Alhaji toh wa ye yayi haihuwan gaba da Fatiha, ni dai na san duk a ledan mu ka auro mu balle ka saki magana" waigowa yayi duk da ya san ita kaɗai ce zata iya maida masa amsa ta kwana lafiya shi ya sa a hali irin haka take shigar ma abokan zamanta fada ko da kuwa ita aka cuta.

Sai da ya kare ma dukkansu kallo sannan yace;

"Ke dai kin san kan ki, ko da yake kila ma ba ki san kanki ba bare saura" Nan ya fita ya barsu duka kamar ruwa ya cinye su. Kowannensu da abin da yake sakawa a rai.

Makarantar su fatima ya isa nan ya iske sun shiga taron,jira yayi har su ka kammala. 

Tana fitowa tayi arba da shi, nan ta nemi duk wani damuwa ta rasa, fuska yalawace da fara'a ta iske shi

"Abie Allah ya bar min kai" Ta faɗi cikin farin ciki. 

"Aminin kwarai ke saurin isa ga amini lokacin da wata damuwa ta samu amininsa, a ina zamu zauna ko mu karasa wajen cin abinci ne" Ya ce yana daga mata gira 

"A'a mu je lambun fada" tace tana jin farin ciki na wanke bakin cikin da ta fito gida dashi. 

Tafiyar minti ashirin ya sada su da lambun fada, suna yi suna tsere tsakanin su don kowannensu a cikin motarsa yake. 

Lambun fada babban waje ne da ya kunshi ababen shakatawa tun daga furanni, tsuntsaye da saiwa kala kala. Lambun ya kasance daya daga cikin abin da Daular ke samun kuɗin shiga don in zaka shiga wajen sau ɗari a rana duk shiga sai ka yanki tikiti na nutud hamsin. 

Sannan duk wani abin lashe baki da ake siyarwa a waje  daga aljihun masarauta ne don haka riban na amfanin al'umma ne. 

Bayan sun zauna aka kawo musu abin taɓa ka lashe ne ya kalle ta yace

" Faɗa min damuwar ki, na san kina ta tunanin wacce za ki kai m kukan ki ne ko" Ya faɗi yana dariya

"Abbie aure nake so, babu wanda ya ke so na yanzu, duk masu zuwa min da an kwana biyu sai su nemi yin zina da ni, Abbie kallon wata mai nakasa ake min saboda rashin aure" Ta ce tana hawaye

BA GIRIN-GIRIN BA Where stories live. Discover now