A Zangon Qahɗaanie kuwa tun da aka kai Alhamzie asibiti labari ya iske iyalinsa akan ya rasu. Nan yan uwansa da yake zumunci da suna kusa suka hallara a gidansa don tarbon gawar sa yayin da yan maza su ka isa asibiti don tahowa da shi.
Da isar su ne suka iske labarin yana Raye sai dai ya jikkata sosai saboda asarar jini da yayi.
"A cinya aka harbe shi" faɗin mijin er sa ta fari. Don ya riga isa wajen kasancewar yana cikin wa'inda su ka fara isa inda abin ya faru.
"Wai waye wannan ya aikata wannan aika-aika" wani matashi ya tambaya, kallo ɗaya zaka masa ka san malami ne zaahidi. Don kuwa yakan jikin sa kaɗai ya isa ya nuna tsantsan talaucin da yake fama dashi.
"ga dai abin da aka kawo ma matansa cikin rawani sa, ganin kifin a bushe yana nufin Aamir na cikin hatsari, in bai niyyar kashe shi ba yanzu toh ana rantsar da shi sarki zai gama da Aamir" Yusuf kanen Aamir ya faɗi wanda shi matan su ka mika ma sakon ganin ai rawanin da yayi amfani da shi a ranar kenan.
"Ai yanzu lokacin bayyana kanmu ne yayi, zamu ce mu muka harbi Alhamzie don mushen can da ke mulkin zalunci ya saki jiki da shi, daga haka sai mu ba ɗaukacin al'umman qahɗaanie shiriya su tuba su bi hanyar gaskiya" wannan zaahidin ya faɗi yana zazzare idanu.
"Amma kuma ai bamu san shirin da ya ke ba, kada mu yi sauri mu ga abin da ba hakan ba" Yusuf ya faɗi yana mai jin tsoro. Amma shi zaahidin nan ya tsaya kai da fata akan gara a nuna musu akwai shiri na musamman, sannan a yi ma fada shigo shigo ba zurfi. Hakan ya sa su bada sanarwan su suka harbi Amir al Ansari.
***
Tun da Zubaida ta isa Kasar Masar ta haɗu da wanda ya kira kansa Abdullah ta mace masa, baki ne mai tsawo da kyan sura, sannan yana da wani irin zaiba a idanunsa da ke tafiya da zukatan yan mata. Ta iske shi a namiji da ya iya sarrafa mace, ita kuma karatun da ta taso da shi kenan a aure, hakan ya sa gaba ɗaya ta ke ganin ta a Aljanna.
Tun da ta isa bata taba jin haushi ba sai da mahaifiyarsu take faɗa mata wa Fatima ta aura sannan auren ramla bai yiwu ba nan ta zauna da mahaifiyar nata su na tsine ma Fatima da mahaifinsu don Zubaida faɗi tayi
"Ammie kin tabbata da ba so yake ya dinga haura mata ba kamar fatima shi ya sa yake cewa shi ba zai ɗaura mata aure ba" tace kanta tsaye ba tare da da la'akari da girman ɓatancin da take faɗi akan mahaifinta ba. Nan uwar ta shiga waswasi don sheɗan ya sha raya mata wannan shakuwa da ke tsakanin Fatima da Alhaji yahuza babu Allah a ciki.
"ke dai ki iya bakinki, ita Ramla yanzu zan san yanda za'a yi na turo miki ita ko kuma in shi Abdullah na da wani a kasa da zai aureta ya taimaka ya zo a ɗaura" haka su ka tsaida magana akan haka su ka yi sallama suna cike da begen juna.
Abdullah na dawowa kuwa ta zauna ta feshe masa komi tana karfafa mahaifinta ba ya so Ramla ta yi aure ne don ya samu ya dinga haure mata kamar yanda yake yi da Fatima. Nan su ka haɗu suna tsine ma Fatima da fatan dukkan wani bala'i ya sauka a gareta da mijinta, shi yana yi ne saboda ubangidan sa mafi ma uba a wajen sa Aamir Al Ansari, sannan yana yi don ya kara samun yardanta yayin da su ka tashi shuka ma su Fatima wani bala'in.
"Yauwa akwai ɗan uwa na, yaron kawu na ne, kin san na ce miki mahaifiyata er Ghana ce toh shi yana chan amma mutumin Allah ne, don kuwa zan iya rantsuwa akan shi waliyyi ne, zan masa magana sai ya je su daidaita da Ramla ayi auren a wuce wajen" yace bayan ya lissafa ya ga hakan ne zai kara ba su damar mallakar fada in su biyu suna auren mafi soyuwa a wajen sarki. Ba su tashi a wajen ba sai da suka kira Hajiya Amina a daular Qahɗaanie suka mata albishir sannan ya kira wanda ya laqa ma Nasiruddeen ya faɗa masa ya masa mata yana so ya shirya ya je Qahɗaanie ayi komai cikin wata biyu zuwa uku. A bangaren Nasiruddeen bai ko Musa ba don Abdullah ya bashi labarin dace da yayi da mata ruwan Fulani da Larabawa.
YOU ARE READING
BA GIRIN-GIRIN BA
Mystery / ThrillerBAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA MANA HISABI AKAN HAKAN Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'a...