20 : Amana

1.3K 237 142
                                    

Afuwan Afuwan for the long silence. Manage this, love u ol.

This page is urs @Reine_Gh thnx for d cover

Ummu-Abdoul 😍😘💕💞

Cikin kwana biyu ya kammala duk wani shiri da ya kamata yayi, duk wata motsi na Qahɗaanie yana sane da shi, abin mamaki bai ga mahaifinsa ba balle iyayensa mata, hankalinsa in yayi dubu toh ya tashi, ya ba kansa laifi ya fi a qirga don gani yake da ya turje ya ki barin gari da tabbas hakan bai kai ga faruwa ba.

"Azeezatie, Habibty, Nisfie ukhra!" Ya ce yana kwanciya a gefen ta matsawa tayi zuwa quryan gado. Tun da ya faɗa mata jirginsa zata tashi karfe sha biyu na daren ranar ta ke kuka. Tun tana yi a ɓoye har ta bayyanar, yaran su ka sata a gaba su na tambaya. Da fari ya share ta sai kuma zuciyar ta gagara hakura da sauraron amon kukanta.

"Da kin adana kukan ki zuwa lokacin da sakon mutuwa ta zata riske ki, Qahɗaanie zan je kuma mijin yar uwarki ya amshe fada, kasancewar dan ta'adda ne" ya fadi mata kai tsaye don ya san lallaɓa ta ba zai sa tayi shiru ba amma hangen fitina ya fi maido mata da hankali.

"shi ne sai yanzu zaka faɗa min, awanni uku sukai saura jirgin ka ya tashi zuwa ga halaka" tace masa tana mikewa a firgice

"Kin san de ba ke kaɗai ba ce ko, in wani abin ya samu baby na sai kotu ta raba mu" yace yana ɗaga mata gira. 

"wai yaushe za ka shiryu ne, mugun fata ka ke jefawa Qahɗaanie ko" tace tana dukan shi da filo. Dariya ya sa mata sannan ya kamo ta zuwa jikin shi. Saitin kunnen ta ya je ya ce

"Ya'yana za su iya zama marayu a kowane lokaci daga yanzu, ki shirya kawai a kowane lokaci za ki iya shiga halin takaba"

"AbdulHaleeeeeem!" Ta faɗi cikin kuka don kwanyarta ya gagara iya hango hakan na faruwa da su. Rungume shi tayi tsam kamar ta komar da shi ciki. 

"kar ka tafi ka ji" tace masa cikin rada

" Ki zama mai dauriya, ke ce karfi na in kin yi kasa wa zai ta da ni. Addu'a nake so ki min, in ban je ba, Abbie, Ummie, Mamie, Ammie, mai martaba, Qalbi, AbdulHaseeb duk su na cikin hatsari. Ummu hafsa ta rasu, mutane sun yi gudun Hijira, rayuka sun salwanta kin ga kenan gaba ɗaya babu wani gata sama da Allah sai kuma ni da za'a samu nasara daga Allah ta hanya ta. Ki zama mai karfi da tsayayyar zuciya, ki zama jaruma ki zama mai yawan addua" sannu a hankali kalaman sa su ka saukar mata da natsuwa sosai, hakan ya sa ta kara yin alfahari da mijinta tare da jinjinawa kokarin sa. 

Nafilfiloli su ka yi na neman nasara sannan ya kama hanyar zuwa filin jirgi cikin rakiyar Santonio amintaccen direban Don clemenza. Bayan tafiyar su Don da kansa ya ɗauke su zuwa gidan shi don samun cikakken tsaro duk da ya san mutan Kasar Sun san su a matsayin ahlin sa.

***

Washe gari da karfe hudu na maraice AbdulHaleem ya sauka a filin jirgin Kasar Ghana. Maimakon ya nufi ofishin jakadancin Qahɗaanie da ke Accra kamar yanda ya bayyana kansa da fasfo mai nuna daga masarauta ya ke. Se ya karya jiki ya shige gari kamar ba Bako ba.

Gidan abinci ya fara isa ya ci, sannan ya nemi wajen buga waya na kuɗi ya sanar da su fatima isarsa Ghana tare da mata sallama don ya san samun nasara daga gare shi ne kaɗai zai jiyar da ita muryar sa. Sun yi dogon hira yayi magana da yan uku sannan su ka yi sallama. Daga nan ya kira Don ya sanar masa babu abin da yake faɗa masa se "ka yi amfani da hankali sannan ka san rayuwar Mahaifin ka na hannun ka, saboda haka babu tsoro a cikin lissafinka, ko zaka ga mutuwa toh ka tabbatar da ka yaqe shi" Don ya maimaita yafi sau a kirga har su ka yi sallama.

BA GIRIN-GIRIN BA Where stories live. Discover now