FYADE; SAKACIN IYAYE
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
Yanda rayuwa ke tafiya, da wuya a wayi gari, rana ta fito ta faɗi ba tare da an ji labarin fyade ba daga kusa ko daga nesa. Kullum al'umma ba su da aikin yi sai tsine ma masu aikata wannan mugun aikin ba tare da an ɗauki mataki akan su ba. Hakan ya sa abin ya girmama har ya tashi daga munzalin yi ma yara mata fyade ya koma ga yan maza.
Abin ya munana har ya kai ga samari ma ba su tsira ba don shaqa musu kayan maye ake don a ci galaba akan su. Duk wannan na faruwa ne saboda sakacin iyaye.
Yanzu a duniyar da muke ciki babu wani gata da ɗa musulmi ke da shi sama da azkar musamman wa'inda manzo SAW ya ambace su da kariya. Maimakon iyaye su maida hankali wajen koya ma ya'yan su azkar ɗin nan sai aka maida hankali wajen sama musu ababen more rayuwa.
Yin azkar din fita gida na sa mutum ya zauna karkashin kulawar Allah har ya koma gida, ga addu'ar kamar haka BISMILLAHI TAWAKKALTU ALAL LAAHI WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH... ALLAHUMMA INNIE AUZU BIKA AN ADILLA AU UDALLA, AU AZILLA, AU UZALLA, AU AZLIMA AU UZLAMA AU AJHALA AU YUJHALA ALAYYA.
Addu'a ce mai sauki, duk yaron da zai iya haddace waka toh lallai zai iya haddace ko kashi na farko na addu'ar ne. Saboda haka wajibi ne ga iyaye da su koyar da Yaransu wannan addu'a.
Faɗin LAA ILAHA ILLA ALLAHU WAHDAHU LAA SHARIKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER sau 100 safiya da maraice na kare mutum daga dukkan sharri. Minti nawa zai ɗauke mu, mu zauna da iyalinmu mu yi shi da sauran adduoi safiya da maraice, yafi zaman kallon film da sauransu.
Abu na karshe, tofa musu Ayoyin Kur'ani a gaban su ba shine addu'ar kariya ba, ko tofashi a ruwa ayi musu tsarki duk wannan hanyar kaskantar da Kur'ani ne. Addu'ar da annabi ya bar mana don karanta ma ya'ya domin kariya shine U'EEZUKUMAA BI KALIMATILLAHIT-TAAMMAAT MIN KULLI SHAIDANIN WA HAAMMAAT WA MIN KULLI A'ININ LAAMMAAT.
Ubangiji Allah ya bamu ikon sauke hakkokin da suka rataya a wuyan mu, ya bamu ikon tarbiyyantar da ya'yanmu. Aameen YA RABBI.
17/02/2018
YOU ARE READING
BA GIRIN-GIRIN BA
Mystery / ThrillerBAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA MANA HISABI AKAN HAKAN Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'a...