Ziyarar Mutuwa
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.comA Yan kwanakin nan mutuwa ta kawo ziyara ga abokai na a shafin yanar gizo ta Facebook. Sati uku kenan da wuya na shiga shafin ban ci karo da sakon mutuwar aboki (friend) ba ko abokin aboki (mutual friend) ba, ni kuma Allah ya min saran shiga shafin mamaci don in ji tausayin kaina da tunanin wata rana hakan zai kasance a shafi na.
A wannan ziyarar ne nake ganin abin da yafi sakon mutuwar ɗaga min hankali don kuwa ina iske mamaci ya/ta yi posting abu yan kwanaki tsakanin ta/sa da mutuwar. Kenan ba'a sanin cewa za'a mace ɗin don da ana sani da tabbas firgici da tsoro ba zai bari mutum ya samu sukunin yin postin ba. Wasu ma za tsakanin post ɗin su da mutuwar su yan awanni ne kawai ko mintoci.
Jiya da dare mu ke maganar rashin lafiyar mahaifiyar kawar mu shamsiyya yusha'u ni da qawata Aisha yareema ashe lokacin da muke wannan hiran bakin sun iso gare ta ko suna shirin zuwa gareta. Mutuwar ta taɓa ni sosai. Muna fatan jinyar ta zama kaffara gareta.
Yan uwa hakika ba abin da ya kai mutuwa darasi, sannan mutuwar abokin Facebook darasi ne ga duk wani mai shafi a Facebook don abin da ya kamata mu yi tunani akai shine in su sun mutu bayan sun yi post ɗin alkhairi da za'a dinga gani ana aika musu lada saboda qaruwa, mu kuma da muka sa gulma da cin naman mutane da talla da zunubin wasu, da yi ma juna bakin ciki da hassada da duk wani mugun abu a social media in muka mutu muna aikata hakan fa?
Auno mala'ikan ɗaukan rai ya ziyarce ka/ki yayin da hannayenki ke typing zagi ko tsinuwa ga shugabanni? Ko ki./ka na Can kana gulma da cin nama ko Ace mutum na chan shafukan batsa ko ko ko...
Yan uwa mu kiyaye gaɓɓanmu daga aikata haramun domin za su bada sheda ranar da baki ba zai iya magana ba.
Allah ya jikan mamatanmu ya kai Rahma ga makwancin su ya sa su kasance cikin Raudha min riyaadil Janna. Mu kuma ya sa mu is ko su a sa'a.Ummu-Abdoul
24th February 2018
5:11pm Nigeria
YOU ARE READING
BA GIRIN-GIRIN BA
Mystery / ThrillerBAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA MANA HISABI AKAN HAKAN Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'a...