part 17

5.5K 243 2
                                    

💚💜❤🖤💙💛
NA CUCE TA
💛❤💜🖤💚💙

®zuwairat(ummu Maryam)

1⃣7⃣



Kafin ta kai bakin titi har maraice tayi saboda ahankali take tafiya ga ciwon Mara ga duk jikinta zafi ga jinin bai bar zuba ba don ji take kaman rag din data saka yayi wet. Nan bakin titi ta ajiye bag dinta ta zauna sama tana kuka
"Wallahi sai naje kin fada mashi ya cire min cikin..." Tafada cikin kuka
"Ke kika kaini gidan...." Take fadawa kanta, tafi minti talatin nan zaune kafin ta samu motan zuwa cikin daura, wayanda ke cikin motan kallon yanda yar karamar yarinya ke kuka Kawai suke sai tambayan ta suke amma Bata cewa komai. Lokacin data isa kofar gidan Hajiya Hajiya Aisha ko gani batayi sosai don har lokacin jinin bai tsaya ba, tana Dan bugawa ta tsaya, jin shuru yasa ta kara turawa sai taji bude yake, cikin gida ta shiga tana kuka, tana shiga Hajiya Aisha tana dawowa daga unguwa, kallon dija dake faman kuka tayi from head to toe ta kwalo idanuwa tana kallon kafan dija dake jini, da Sauri ta karaso wajenta
"Dija lafiya?..." Ta tambayeta tana kallon bag dinta dake kasa, cikin shessheka dija tace
"Ki maidani chan gidan ya cire min...." Tafada cikin kuka, kallon mamaki Hajiya tayi mata don Bata gane abinda take nufi ba, Hajiya Bata damu da abinda take cewa ba sai Kara cewa tayi
"Dija me akayi maki !!..." Ta tambayeta cikin tashin hankali tana daga doguwar rigan dake jikinta tana kara kallon jinin dake kafanta, tana cewa
"Inna lillahi..." Don anata tunanin raping dinta akayi, dija Bata amsa mata ba tacigaba dacewa
"Ki maidani..." Bata idaba Hajiya ta ce
"Wai meke damunki..." Ta daka mata tsawa da karfi,  da Sauri ta fara cewa
"Ammi tace ciki gareni....shine tace inzo ki maidani...a cire min..." Ta fada cikin kuka, idanuwa Hajiya ta kara zarowa
"Ban gane ciki ba...."  Hajiya Aisha ta tambayeta cikin tashin hankali don abinda bai taba faruwa da sauran yaran da take kaiwa gidan aiki bane
"Wai ina da ciki ammi tace...." Inji dija,
"Wannan jinin fa?..." Hajiya ta fada tana nuna legs dinta
"Nima ban Sani ba...." Ta amsa mata,
"To wa ya fadawa amminki kina da ciki?..." Hajiya ta sake tambayan ta,
"Nima ban saniba....cewa tayi ina da ciki wai in tafi da jikkata kuma wai Bata yafemin ba...tace kar in kara dawowa..." Hajiya Aisha dai tsayawa tayi tana kallon dija don ko kadan babu alaman ciki tattare daita,
"Village mentality... In ma cikin gareki sai ta koreki?...to bari ijn tambayeki...kin raba kwanciya da wani?...." Ta tambayeta, da Sauri dija ta girgiza mata kai Sannan tace
"Wani ne ya saka min wani abu a gabana..." Da Sauri Hajiya tace
"Waye?..." Cikin kuka dija tace
"Chan gidan da kika kaini...." Baki Hajiya ta bude tana mamakin abinda ke faruwa, dija kara dafe cikinta tayi, ta fara yarfe hannuwa tana cewa
"Wayyo cikina..."
"Me ya sami cikinki...." Hajiya ta tambayeta
"Ammi ta harbe min ciki..." ta fada cikin kuka, mai aikinta Hajiya ta kwalawa kira, sai tataho da gudu saboda yanda Hajiya ta kirata on top of her voice, kallon dija tayi ta tsorata, umarni Hajiya tayi mata da ta dauki bag din dija su shiga dakinta ta gyara mata jiki zata kaita hospital. Nan suka shiga dakin dija ta shiga wanka sai kuka take dukda muryanta bai fitowa saboda kuka. Hajiya kuma zama tayi falo ta rafka uban tagumi, tana aduan Allah yasa ba hakan bane don batasan abinda zai biyo Bata ba muddin hakan ya zamo gaskiya.
Mai aikin Hajiya Aisha  tambayan ta tayi abinda ke faruwa, dija fada mata komai tayi, fashewa tayi da kuka saboda tausayi don itama taga cikin sanda dija ke saka wasu kayan bayan ta fito daga bathroom, duk pant da rag da dija ta saka ya cike, pad mai aikin Hajiya ta Bata ta nuna mata yanda zatayi amfani dashi. Few minutes later Hajiya ta shigo ta umarceta data biyota, nan suka kama hanyan hospital, inda doctor ya shaida mata da gaske dija na dauke da cikin wata biyar kuma ya Kara dacewa tana bukanta bed rest, don kar cikin ya yamu matsala, hannu Hajiya ta dafa ga kai tana kuka, don gani take dija tayi karanta da sanin namiji balle ciki, kiran dija waje tayi, saida suka kebe Sannan tace
"Dija tsakanin ki da Allah wa yayi maki ciki?..." Ta tambayeta cikin sanyin murya, sabon kuka dija ta fara tana cewa
"Nima ban San yanda ake ciki ba..." Hajiya goge hawayen face dinta tayi
"Wa ya saba saka maki abun fitsarinshi...." Hajiya Aisha ta tambayeta, da Sauri dija tace
"Wannan mutumin dake gidan da kika kaini ne ya saka min wani abu... Ban San ko meye ba..." Hajiya kara fashewa tayi da kuka tana tuna lokacin da dija ta susuce kan dole sai an maido ta gida Ashe wannan ne dalilin,
"Nashiga uku..." Hajiya ta fada cikin kuka,
"Waye daga cikin yan gidan?..."
"Wannan babban...Wanda akace zaayiwa biki..." Ta fada cikin kuka,  itadai Hajiya shuru tayi tana tunanin abinyi don da Bata kaita ba da bazaayi mata ciki ba, dakin doctor suka koma Hajiya ta zauna Sannan tacewa doctor
"Dan Allah a cire cikin... Yarinyan tayi karanta...Sannan ba aure gareta ba.."
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun..." Doc ya fada Sannan yacigaba dacewa
"Gaskiya Hajiya bamu irin wannan danyen aikin nan wurin.. Sannan INA baki shawaran bai kamata ayi kisan kai ba don Allah ya kaddara hakan zai faru...sins din zasu yi yawa...Kawai ni shawara ta shine ki kaita gidan da akayi mata ciki, in da hali kilan ya aureta..." Doc Wanda ba bahaushe bane ya fada mata, cikin kuka Hajiya tace
"Ai mu bamu irin wannan abun..."
"To Baku irin wannan abun amma anayiwa yara raping?... This is an act of molestation... Kawai ni shawara ce na baki..." Yafada Sannan ya mike, bayan ya rubuta mata drugs da zaa sayawa dija
Hajiya kasa tafiya tayi don duk ta rasa abinyi, banda faduwan gaba babu abinda ke damunta, kallon dija dake tsaye gefen ta hannun ta dafe da cikin ta tayi
"Ya akayi kika yarda...bakisan babu kyau kwanciya da namijin da ba aurenki yayi ba?...gashi yanzu yayi maki cikin shege..." Hajiya ta fada, dija kara fashewa tayi da kuka don tanajin yanda ake magana kan cikin shege cikin tatsunniya kuma babu Wanda ya tabayi a garinsu sai ita,
"Ki kaini ya cire min..." Ta fada,Hajiya tsoki taja saboda haushi babu kaman yanda dija ke nuna Bata San komai dangane da abinda ke faruwa ba,
"Wa zai cire maki?.." Hajiya ta tambayeta tqnq hararanta,
"Shi Wanda ya saka min..." Tafada tana kuka. Wani irin dogon tsoki Hajiya ta kara ja,
"Sakarcinki yayi yawa..shiyasa kikaje kika gwale kafa...to ni babu ruwana...gidanku zaki koma...daga taimako bazaki batamin suna ba...ba a kanki NA fara kai yara aikatau ba..." Tafada tana mikewa, fita tayi dija ta bi bayanta suka shiga mota suka bar hospital. Chemist tabi ta sayi Maganin da aka rubuta ma dija. Sannan suka koma gida. Da kyar mai aikin Hajiya tasata taci abinci Sannan tasha Maganin kafin ta kwanta.  

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now