na cuce ta 27

5.8K 422 44
                                    

❤💙💜💛💚🧡
NA CUCE TA
🧡💚❤💙💜💛


®Zuwairat (ummumaryam)



2⃣7⃣





Yau anyi ruwa sosai a jos hakan yasa garin yafi da sanyi, dija da rakube gefe daya a inda take kwanciya wato inda masu ganin doc ke zama, ji tayi sanyin yayi yawa, ga jikinta nayi mata itching don har ta mance rabon da tayi wanka, she can smell her body, amma hakan bai hanata jin sanyin ba, bodyguard dintane ya motsa don tana ganin cikinta amatsayin abinda ke tsaronta don duk yanda take da jin tsoro data tuna da akwai wani cikin jikinta sai ta rage jin tsoro, duk yanda take cikin damuwa data tuna abin cikinta sai ta saki murmushi, kawai sai ta zauna tana picturing face din abin dake cikinta,
"Da sanyi ko?...." Ta fada ahankali bakinta na rawa,
"Kaima kana jin sanyin?..." Ta sake fada tana kallon cikinta, kuma Allah so kind in tanawa cikin magana bai dadewa sai yayi motsi kaman yana replying ba karamin dadi hakan ke saka dija ba,
"Banji ba...da sanyi?..." Ta sake tambayan silent tummy dinta, shuru tayi tana sauraron movement as usual amma nothing, shafa cikin tayi,
"Babu motsin yau?.... Kayi motsi....kaga yau babu wuta ....tsoro nakeji ...kuma ga sanyi...." Ta fada tana shafa cikin ta, still shuru babu response, sikam daga hannunta tayi ta laftawa cikin duka, Wanda sai da ta dan saki kara saboda zafi. Nan take abinda ke cikinta ya fara juyawa kaman yanda take bukata, murmushi ta saki
"Nace kana jin sanyi?...." Ta tambayi cikin, motsi ya danyi
"To bari in rufeka...karkaji sanyi...." Ta fada ta bude bag dinta daya kara tsufa yayi dirty saboda yanda take pillow dashi always
Daya daga cikin kayanta da sukayi dirty ta dauko ta rufe cikinta,
"Sanyin ya dainako...." Ta tambayi cikin tana shafa shi tro and fro, dan biting lips dinta tayi sabida yanda sanyi ke rasta legs dinta, Riga daya ta kara daukowa ta rufe legs dinta sannan ta samu sauki. Dan juya kanta tayi gefe daya kawai sai yazid ya fado mata arai, sai take tunanin da batayiwa ammi gardama ba da yanzu tana zaune lafiya da family dinta, she's young and innocent amma yanzu tasan yiwa babba gardama is bad don ta koyi darasi a rayuwa, tasan duk abinda babba ya fada is always right don she promise herself never to disobey an elder again. Tana tuna sanda ammi ke kukan kan kar ta tafi ta barsu amma she wanted a better life for herself and her family, bata yi zaton such an awful destiny awaits her ba,
"Mutane basu da mutunci...in nayi kudi zan dinga taimako....in naga yar karamar yarinya zan taimaka mata....dukkan mutane basu iya taimaka min...." Tafada tana fashewa da kuka at the same time tana scratching jikinta, bata iya good ten minutes batayi scratching private part dinta ba saboda yanda take ji, cikin kuka tafara cewa
"Na gaji...nagaji.. Allah nagaji...Malam yace aljanna da dadi...ka kasheni ka sakani a aljanna...ni dai nagaji...." Ta fada tana dukan kasa same time abun cikinta ya kara motsi, dan saurarawa tayi sannan tace
"Da gaske nagaji...kawai mu mutu ko mun huta...ko mun samu wurin bacci mai kyau
..ko mun dinga samun abinci kan lokaci...." Tafada tana goge face dinta sannan tana tuna ta kusa gama kashe kudinta, despite tana managing sosai. At times tanajin kaman ta tafi kauyen su ammi  amma kuma the feeling of rejection sai ya hanata.

  Yau wedding dinsu shahid sauran 3 days, mufida na tsaye bakin wardrobe tana packing kaya cikin bag, yazid na kwance yana kallon ta, kawai sai tunanin Allah yasa ya shawo kanta kawai yake don yayi deciding ba zaije wedding din ba, instead zai kara komawa jos during the weekend ko Allah yasa yaga dija, dan juyowa tayi ta kalleshi shima ya kalleta tare da sakar mata murmushi, itama maida Mashi martani tayi sannan tace
"Baby na gama packing nawa....it's your turn...." Ta  fada zipping bag din
Dan murmushi karfin hali yayi yana lumshe eyes kaman mai jin bacci
"Baby...I think ba zan je ba...." Ya fada ahankali, mufida dakata zipping tayi ta tsaya tana kallon shi for a moment sannan tace
"Why dear?...." Ta tambaya tana komawa kan gado kusa dashi, jawota yayi
"Cos I look horrible... Banason a dinga tambayan what's wrong with me...akwai kije...zan zo daukanki next week...." Yafada yana shafa gashin kanta,
"Haba dear...how is that possible... Ace two of your siblings zasuyi aure kuma your are absent... Gaskiya muje kawai...ko wedding fatiha kayi attending...." Ahankali ya girgiza mata kai
"No baby...kawai kije...after all we have a lot at the office... Kinga few days back da banyi aiki ba yasa aikin sun zama Lodi....." Kai kawai mufida ta dinga girgizawa,
"Baby yau Thursday.... Mu tafi gobe Friday...sai ka zauna gidanmu...amma gaskiya I don't want to travel with out you..." Tafada tana lafewa jikinshi, kissing kanta yayi
"Sorry sweetheart... Just this once...go with out me...", mikewa tayi daga jikinshi
" if you are not going.. Am not... Kai da abunka kace baka zuwa... Ina amfanin zuwa na ni?..." Tafada tana mikewa daga kan gado, wurin bag datayi packing ta nufa ta duka zatayi unzipping, da Sauri ya mike
"Baby mommies zasuyi fushi in baki je ba...." Yafda yana rike mata hannu kar tayi zipping bag din,
"What about you?.. Bazasuyi fushi in baka je ba?..." Tafada kaman zatayi kuka, tallabo face dinta yayi
"Bazasuyi ba...you know they don't care about me any more..." Yafada cikin sanyin murya
"They care mana...muje ko kuma  in fasa zuwa...."
"No dear ki zakije....go first thing tomorrow morning... Ni kuma zan zo jibi...." Yayi mata karya, turo baki tayi
"I don't believe you...." Dariya yayi
"My word is my bond....just go and enjoy yourself...." Hararanshi tayi
"Wane irin enjoyment zanyi babu kai?...." Tafada sounding naughty, dariya yayi
"To muje muyi wanka sai in baki na sati daya...." Yafada yana daukanta.
Dariya itama tayi
"Na sati daya na zalunci kenan...."
"Ai kinsan am always gentle...."
"This days ko...amma before you are rude in bed...." Tafada tana tuna yanda yake handling dinta kafin pregnancy case din nan ya fito,
"Yanzu baby am rude?... Duk sauki na?...to yau sai na kwada maki rudeness... Yau my name is rudeboy...." Yafada yana tura kofan bathroom da kaanshi, dasauri ta diro daga hannunshi,
"Gaskiya banson rudeboy...just be gentle...." Tafada tsoro na kwance kan face dinta,
"Ai so nake yau in bar maki tabo yanda da kinje kano dadin na nan jikinki..." Hararanshi ta karayi tare da komawa gefe
"Banson... Na hakura...." Dariya yayi
"Just joking...kinsan I can't do anything  like that..." Yafada yana cika bathtub da ruwa at the same time yana tunanin how well he's trying don ji yake kaman ya Dora hannunshi kai ya dinga ihu in ya tuna cewa his seven months baby na Chan wani waje cikin wahala
"That's if she make it...." Yafada under his breath
Mufida kura Mashi ido tayi son in da sabo ta saba several time zai dinga yiwa kanshi magana at times taji wani lokacin kuma batajin abina yake cewa amma she knows it's all about khadija.

The following day suka shirya bayan breakfast wanda  ba wani cin kirki yake ba don in don sonshine ya samu liquid abu ya sha ba kawai cos in sau goma zai kai abu cikin bakinshi sai ya tuna da dija ko ta ci ko bata ci ba hakan yasa ko kadan baison cin abinci amma yasan rashi hakan zai batawa mufida rai so dole yake forcing kanshi yana cin abinci.
Trolley bag dake shake da kayan sawan mufida ya dauka ita kuma mufida ta tsaya kashe electronic dake falon. Bakin kofan falon ya tsaya yana jiranta sai da ta gama ta taka cikin kasaita  ta karasa inda yake tsaye, hannuwa ya bude mata ta fada jikinshi
"I will miss you..." Ya rada mata cikin kunne,
"For just a day ko....tunda kace zakazo gobe...." Tafada tana kara lafewa jikinshi,
"Amma kaman shekara nakeji...cos am gonna be lonely...." Ya ce mata, kissing dinta yayi for a moment sannan ya bude kofa
"Ladies first..." Ya fada yana nuna mata kofa ahankali ta wuce tana murmushi bayanta yabi tare da locking door dinsu sannan ya kama hannunta suka sauka zauwa parking lot. 

Da Sauri ya ajiyeta park don cewa tayi bata iya driving from abj to Kn wai zai bata wahala, empty golf ya amsar mata ya biya ta shiga sannan ya kama hanyan office.

Around noon yana zaune a office yana tunanin rayuwa, yanzu yasan sauran two months dija ta haihu kuma baisan irin halin da zai shigaba muddin har lokacin yayi bai ga dija ba hakan yasa yayi niyyan  in ya tafi jos wannan Karin zai je TV and radio stations ya bada description dinta don a tayashi cigiyan ta don ya tambayi pics dinta ammi bata dashi.
"Kai..." Yaji an fada ana dukan desk din gabanshi, hakan ya maidoshi hayyacinshi, gyara speck din face dinshi yayi yana murmushi
"Kai yanzu baka da abunyi sai tunanin..." Inji sultan dake  zama kan leather seat dake facing yazid
"Ba tunani nake ba...kawai am just absent minded ne...." Ya amsa Mashi,
"Kai ustaz ne amma sai shegen karya....akamaka red handed amma kace ba haka ba...in ba tunani kake na did you know sanda na shigo ciki?..." Sultan ya tambayeshi, murmushi kawai yayi bai kara cewa komai ba, sultan zai bude baki yayi magana wyanshi ya fara ringing, murmushi yayi yana cewa
"My mommy..." Yafada yana picking wayan, yazid dai kura Mashi ido yayi don yanzu ya mance rabonda mom ta kirashi sannan in ya kirata discussion dinsu very brief ba kaman da da suke hours suna hira a kan waya ba.
"Mommy I promised zanzo ai....tare zamu cinye wannan weekend...." Yazid yaji sultan na fadawa mom dinshi
Murmushi kawai yazid yake saboda yanda sultan ke labartawa da mom dinshi, sunfi minti ashirin suna waya sannan sukayi bankwana, dariya sultan yayi yana cewa
"Wallahi zullumin tuki daga nan zuwa jos kawai nake..." Surprise look yazid yayi Mashi tare da dafa goshinshi
"Kasan na mance you are from jos?.... It escape my mind wallahi...." Dariya sultan ya karayi
"Da gaske kake?..."
"Wallahi kam...ai for the last two months sau uku baje jos....kuma a hotel nake kwana kafin in dawo...."
"Kam....amma baka kyau ta ba....ga gidajen mu chan har da guest house...." Inji sultan
"Ai I tell you na mance...ko gobe ma zan goma jos....." Yafada not sounding happy kaman da farko,
"To me kakeyi a jos?..."  Sultan ya tambayeshi, shuru yazid yayi yana Dana sanin fada Mashi yana zuwa jos don ya mance zai tambayeshi dalilin.
"Ina zuwa wajen families ne..." Yazid yayi Mashi karya, girgiza kai sultan yayi
"Ban yarda ba ...kodai mata zaka kara...amma zuwa jos don ganin family har sau uku a cikin wata biyu is not accepted...." Dariya yazid yayi
"Ai ba mugun abu bane...kawai na fada maka gaskiya...."
"Hmmm ai ku ustazai ne...baku karya...saidai Ku fadi ba daidai ba....." Inji sultan, yazid dan daure fuska yayi  don yasan he's no saint,
"Gobe sai mu tafi tare kawai..." Inji sultan,
"Ai ni ba cikin gari zani ba....sai dai zan kwana gidan Ku ne...."
"Ai wannan ba matsala bane ...kawai muje tare ..zanyi escorting dinka zuwa inda zaka...." Da Sauri yazid ya girgiza Mashi kai
"No.... "
"OK...muje sai kayi amfani da motan gidanmu kaje inda zaka ...." Sultan ya fada mashi,
"OK then....daman banson kwana a hotel wallahi...." Haka suka cigaba da hira sannan sultan ya koma office dinshi, the following day which was Saturday suka kama hanyan jos run da sassafe, da motan sultan sukayi amfani.

NA CUCE TAWhere stories live. Discover now