part 8/9

1.9K 62 0
                                    

[8/9, 2:08 PM] Ummey Zee Abakson: 💫 *Noorul Huda*💫

_Happy Belated born day Asmy B Aliyu, age with grace dear sis, Allah ya karo shekaru masu albarka ya nuna mana auren ki mu xo mu sha biki_😘

8.....

Kwace hannunta tayi kamar xata yi kuka tace "Doctor...." Yace "Toh in ruwan ki da rashin wanka na?" a hankali tace "Toh yi hakuri...." Murmushi yayi ya juya ya nufi daki ta bi sa da kallo, can ta ajiye jakar hannunta ta xauna tana kallon program din da ake a tv, bayan minti kusan ashirin taji an danna bell, mikewa tayi da sauri tana kallon kofar, ji tayi ance "Ohh ya Abuu me yasa kake kulle kofa ne yanxu, ni dai ka bude min Mami ce ta aiko ni wllh...." Da sauri Samantha ta mike ta shige bedroom dinsa ta tura kofar tayi lamo jiki, kwata kwata bata ji fitowarsa ba sai gyaran muryarsa da taji a bayanta ta juyo da sauri, daure yake da towel a waist, bakin gashin kirjinsa ya kwanta luf luf don ko goge jiki bai yi ba, a rikice ta juya xata bude kofar dakin ya riko hannunta  kamar xata yi kuka tace "Doctor ur sister is outside.... Shi yasa na shigo" key ta ga yasa ma kofar ta juyo da sauri tana kallonsa a tsorace, ya wara ido yace "Tell me what you are afraid of?" Girgixa kai tayi da sauri tace "Noo... Nothing" yayi 'yar dariya yace "Why is it that girls always have this negative thought?" Juyawa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Am not a bad person, erase that thought off ur mind immediately" a hankali tace "Ohk!" Ya kama hannunta ya nufi gado da ita ya xaunar da ita gefen gadon, snn ya dau kayansa ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya ya dau turaren gaban mirror ya feshe jikinsa da shi ya karasa kusa da ita ya feshe ta ita ma, boye fuskarta tayi jikin gado tana murmushi, can ta dago a hankali taga bbu shi a dakin, mikewa tayi tana kare ma dakin kallo, ko ina fes except from the bed that's untidy, murmushi tayi ta bude curtains din room din ta fara gyara gadon, cikin yan mintuna ta gama ta fita xuwa parlor, xaune ta gansa cup din coffee a hannunsa, ta wuce kitchen ta dauko sweeper da mop ta dawo ya bi ta da kallo har ta shiga bedroom, tana fitowa yace "Well done, thank you" tayi murmushi ta kai abubuwan hannunta kitchen ta fito, yace "Come and make a tea for ur self" tace "Nayi breakfast" yace "Nasan kin yi ae, karawa xa kiyi" tace "Noo na koshi sosai" kan kujera ta nufa ta dau jakarta yace "Ina xa ki?" Tace "Lesson!" Yace "Lesson da jakar kaya?" Ta kallesa tace "Aa xan ajiye gidan wasu family frnds dinmu ne, Mumy ta tafi Kaduna, Abba baya nan, ni kadai baxan iya zama a gida ba shine xan je gidansu" Abuturrab ya ajiye Mug din hannunsa yace "Sbda kina tsoron abu xai cinye ki?" Dariya tayi tace "A'a ni bana tsoro kawai bana son in xauna ni kadai ne" yace "Ohk...." Xaunawa tayi kan kujera ta dalilin ciwo da taji cikinta ya fara mata, kamar ko ya sani yace "Kin samu lafiya Yanxu?" Kai kawai ta gyada masa ta jinginar da kanta jikin kujera, ya bude warmer din dake dauke da wainar shinkafa ya debi biyu ya kalleta ya ga kallonsa take, yace "Taho mu ci" a hankali tace "Masa?" Ya gyada mata kai, tace "Sa min guda daya" yace "Sauko mu ci dai" ba musu ta sauko ta dawo kusa da shi ya kara masu guda biyu, ya debi rich vegetable soup din dake wani warmer a waje daban ya fara ci da spoon, dauka tayi ita ma ta fara ci, ganin yanda take ci kamar ana tilastata yace "Bai maki dadi ba ne" girgixa masa kai tayi da sauri tace "Yayi dadi...." Yace "Then me yasa kike haka da fuska" kamar xata yi kuka ta ajiye Masan hannunta ta kwanta gefensa tace "My tummy" sai kuma ta mike ta koma kan kujera ta kwanta, bin ta yayi da kallo ya ajiye spoon din hannunsa yace "Ya fara maki ciwo" kai ta gyada masa lkci daya hawaye ya cika idonta, a hankali yace "Sorry" mikewa yayi ya shiga bedroom sai ga shi ya fito da allura da Magani ya dawo kusa da ita ya shiga hada alluran, yana gamawa ya kalleta yace "Toh juyo in maki sai ki sha Magani" ba musu ta juyo har xata daga gown din sai ta tsaya kuma, kallonsa tayi hawayen da ke makale idonta ya silalo ta juya masa baya tace "Bude min zip din pls" bude zip din yyi a hankali, ta cire hannun gown din don akwai ves jikinta, ta sauke gown din kasa yanda xai iya yi mata alluran snn ta juya masa baya ta kwanta, daukar syringe din yayi ya mata alluran ta juyo tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Sorry!" Ya mike ya dauko table wata ya bata maganin ta sha snn ta koma ta kwanta, bayan awa daya ya kalleta ya ga idonta biyu, yace "Ya daina" ta gyada masa kai, har bayan azahar tana gidan a kwance, yana dawowa daga masallaci bayan anyi la'asar ya durkusa kusa da ita yace "Baki ci abincin ba har ynxu" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" mikewa yayi ya shiga daki ya shirya ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Xan je clinic in dawo yanxun..." Mikewa tayi tace "Gida nima xan je" ya hade rai yace "Noo kiyi kwanciyar ki kina tashi cikin xae fara, don't worry i will lock the door" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, har shidda bai dawo ba, ta sauko da kyar jin cikin xae fara mata ciwo ta xuba abincin da aka kawo masa daxu ta ci kadan ta dau sauran magungunan da ya bata ta sha ts koma ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa..
A hankali ya durkusa kusa da ita yana kallonta ganin tun da ya dawo take bacci, can ya kalli agogo ya dafata yace "Frnd!" Da gani kasan bacci me nauyi take da kyar ta bude idonta, yace "Cikin ya daina" ta gyada masa kai a hankali hade da lumshe ido, dagota yayi yace "Taso ki kwanta a ciki, there might be mosquitoes here" girgixa kai tayi cikin sanyin murya irin ta mai bacci tace "A'a gida xan tafi" bai kulata ba ya dagata ta rike sa ta dalilin jiri da taji, ya ja ta xuwa bedroom dinsa, tace "Noo Doctor I want to go home...." Kwantar da ita yyi kan gadonsa ya dau lallausan duvet ya rufa mata ya kai bakinsa kunnenta yace "Go to sleep" rufe ido tayi ya gyara mata gashin kanta a hankali yace "Sleep tight Sam~ha" mikewa yayi ya kashe mata fitilan dakin ya bar na bed side snn ya dau wani duvet din ya fita parlor don idan yace xai shiga wani dakin ma tare da k'ura xa su kwana, kashe wutan parlon yyi ya kwanta kan 3 seater ya lulluba da duvet hade da lumshe ido, ya dade bacci bai daukesa ba, daga karshe dai baccin yayi awon gaba da shi bai tashi farkawa ba sai ana kiran assalatu, mikewa xaune yyi bayan yyi adduar tashi daga bacci ya kusa minti ashirin a haka kafin ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala, raka'atainul fajr yyi yana ta xaune kan darduma har yaji xa a tada sllh a masallaci snn ya mike ya fita ya kullo kofar ta waje, ko da ya dawo durkushe ya ganta kusa da gado idonta lumshe ta hade tafin hannunta alamar addu'a take, ya jingina jikin kofa yana kallonta cike da tausayi har dai ta gama, tana ganinsa tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Good morning Doctor" ya mayar mata da murmushin yace "Morning how's ur health?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki yanxu" mikewa tayi ta fara gyaran gado, ya shiga bathroom sai ga shi ya fito da toothpaste da new toothbrush ya ajiye mata gaban mirror ta kallesa tace "Thank you" murmushi kawai yyi ya fita, main house ya nufa don xuwa gaida Mami, a kitchen ya sameta tana hada ma Abba breakfast ya gaisheta ta amsa tace "How was ur nyt!" Yace "Alhmdllh,  mene yasa su Ramla ba su yi girkin ba" tace "Na ma gama, he's travelling ne shi yasa...." Abuturrab yace "To where?" Tace "Shiga ka tambaye shi mana" juyawa yayi ya fita ya wuce part din Abbansa, yana kkrin rufe briefcase dinsa ya shigo, Abba yace "How you?" Xaunawa yyi kasa yace "Alhmdllh tafiya xa kayi Abba?" Abba yace "In shaa Allah, ya maganar da muka yi da kai ranan?" Shiru Abuturrab yyi, lkci daya jikinsa yayi sanyi, Abba yace "This is not a matter of u looking at me that way, Yakumbo tace hada bikin da na Yusuf xa ayi..." Kamar xai yi kuka yace "Abba ni fa bani da kowa" Abba yace "That's not a problem, sai ka fara nema yanxu don ina jin nn da watanni biyar ne bikin Yusuf din, idan kuma ka amince mu yi maka xabi it's okay my Stubborn!" Abuturrab bai ce komai ba, Mami ta shigo da sallama rike da tray din breakfast, mikewa Abuturrab yyi ya sallami Abban nasa ya fice, ji yyi ransa ya baci, bai ko kalli Khaleesat dake gaishesa a parlor ba ya fice ya koma bangaren sa ya kusa minti ashirin xaune a waje kafin ya shiga ciki, shara ya sameta take a parlor, ya xauna kan kujera yace "Wel done" murmushi tayi bata ce komai ba, har ta gama ta shiga kitchen ma ta gyara, ya mike ya shiga bedroom yana fitowa ya kalleta yace "Na hada maki ruwan wanka a bathroom...." Xata yi magana wayarta ya dau ring a jaka, karasawa tayi da sauri ta ciro wayar taga Mumy ce ke kiranta, kallonsa tayi sai kuma ta xauna ta daga ta kai kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace "Samantha kin shirya tafiya church kuwa?" Turo baki tayi tace "Mumy baki ko tambaye ni ya ciki na ba..." Mumy tace "Ohk ya cikin" kamar xata yi kuka tace "Yana sauki..." Mumy tace "Ohk toh ki shirya kar fa kiyi latti, and make sure yau ma ki tafi gidansu Stellq kar ki kwana ke kadai" Samantha ta kalli Abuturrab dake ta kallonta a hankali tace "Ohk mum" daga haka uwar ta katse wayar, Ta mike tana kallonsa tace "Xan je gida in shirya" yace "Cinye ki xa ayi a nn idan kika shirya," murmushi tayi tace "A'a xan dauko abu ne" yace "Pad?" Xaro ido tayi tace "A'a fah!" Yace "Toh me?" Ta langwabar da kai tayi shiru, yace "Toh tafi kiyi Wankan ki" a hankali tace "Toh" snn ta nufi bedroom din, ko kafin ta fito har ya kai mata jakar kayanta dakin, tana fitowa ta shirya da sauri da sauri tana tsaye gaban mirror xata daura dankwali aka bude kofar dakin, juyawa tayi da sauri, tayi still a gun ganin Ilham, ita kanta ilham kasa motsi tayi bakin kofar, can ta juya da sauri ta fita daga dakin, Abuturrab dake baya gun Gym dinsa ya zagayo don daukan Coke ya ga takalman Sister tasa a bakin kofa, kasa shiga yyi sai gata ta fito, bata ko kallesa ba xata wuce sa ya rikota da sauri yace "me kike nema nn Ilham" fixge hannunta tayi tace "Yaya wacece ita?" Jawota yyi jikinsa yace "listen she's just a frnd lil sis....." Kamar xata yi kuka tace "Noo yaya me yasa kake haka...." Dago kanta yayi yace "Wllh frnd dita ce ilham, trust me.... You've got a decent brother" tace "Amma ae bai kamata ta shigo maka gida har bedroom ba sae kace ba musulma ba" yace "No but she's a Christian, an innocent Christian" shiru Ilham tayi Tana kallonsa, yace "Trust me sis" tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Promise you won't say anything... Even to Khaleesat and Ramlah" turo baki tayi tace "Naji" yayi murmushi ya ja hancinta yace "That's my sis, taho inyi maki introducing dinta, she's a nyc gal" girgixa kai tayi a takaice tace "Noo I hate Christians" daga haka ta wuce ta bar sa gun a tsaye ya bi ta da kallo, can ya shiga parlon yaga Samantha na hada kayanta tana ganinsa kamar xata yi kuka tace "Am sorry doctor...." Yace "For what?" Hawaye ya cika idonta tace "Ur sis...." Murmushi yayi yace "Ae bbu ruwanta ita...." Bata kuma cewa komai ba ta dau jakarta tace "Xan tafi" ya mata wani kallo yace "Sai kin yi breakfast" tace "Noo nayi late for church" yace "toh baxa ki fita ba sai kin yi breakfast ki sha Magani" shiru tayi tana kallonsa, yace "Yes!" Daga haka ya wuce bedroom, xaunawa tayi parlor tayi tagumi, bata ji shigowar Ilham ba sai ganinta tayi parlon rike da tray din abinci, ko kallonta ilham bata yi ba ta ajiye xata fita sai kuma ta nufi bedroom dinsa, Samantha ta bi ta da kallo duk jikinta yyi sanyi, Abuturrab na ganin Ilham yace "Sis kin rufe kofar...." Ta hade rai tace "Breakfast na kawo maka gashi can a parlor" mikewa yayi ya kama hannunta suka fito parlor yana kallon Samantha yace "Meet my Lil sis Rabi'ah but we do call her ilham!" Samantha ta kalleta tana kirkiran murmushi tace "it's nyc meeting you ilham" Bbu yabo bbu fallasa Ilham tace "Same" ta kwace hannunta tayi hanyar kofa, ko kadan Abuturrab bai ji ddin yanda ta amsa ba, ya bi bayanta suka fita a tare, sai da suka yi nisa ya fixgota yace "Why did you answer her that way?" Bluntly tace "Because I don't like her" hade rai yayi yace "Then you don't like me also" da mamaki tace "Toh meye hadin ka da ita ma yaya, ni I hate her...." Wani tsawa yayi mata tayi tsit, strictly yace "Idan kika sake cewa you hate her I won't take it likely with you, me tayi maki?"

💫Noorul Huda💫حيث تعيش القصص. اكتشف الآن