part 17

1.3K 57 1
                                    

💫 *Noorul Huda*💫

17.....

Maryam bint Imran shi ne sunanta, mahaifiyarta kuma Hannah, an san Maryam a mace mai son ibada da tsoron Allah a Jerusalem, Mala'ika Jibril shi ya xo mata da wahayin haihuwar Isa Pbuh, da farko taji tsoron ganinsa ta kuma  nemi tsarin Allah daga gare shi, and he told her he was only a messenger from Allah, yana kuma yi mata albishir da kyautar A righteous son from Allah, Maryam tayi mamaki da jin hakan don tasan bata da aure kuma ita budurwa ce, a nan tace "Amma taya hakan xae yiwu..." Nan mala'ika jibril yace mata hakan xa'ayi domin Allah yana halittan abinda yaga dama, when he decrees a matter he only says to it 'Be' and it is. (Qur'an 3:47) and that was how Maryam (As) submitted to the will of Allah SWT and secluded her self from society and gave birth to Isa (AS) right under a Date palm tree (Bishiyar dabino) which serve as her source of Nourishment during labour not in a manger as said in your Bible." Murmushi Samantha tayi bata ce komai ba, Yayi murmushin shi ma ya ci gaba, "Maryam ta koma gun 'yan uwanta da Isa pbuh a hannunta, wanda hakan yasa aka fara condemning nata a garin a cewarsu ta aikata sa6o, ko kadan Maryam bata girgixa da surutansu ba tana rike da Annabi isa a cot dinsa, Allah SWT bai barta a haka ba don a nan take isa AS ya bude baki yace "Lallai ni bawan Allah ne...." Shiru yayi ganin yanda ta bude idanuwa tana kallonsa, yace "Ya?" A hankali tace "Uhm ci gaba..." Murmushi yayi ya langwabar da kai yace "He continued saying, Allah has made him blessed wheresoever he be, he has enjoined on him prayer and alms as long as he live, and to be dutiful to his mother, and Allah has made him not arrogant, unblest, and peace be upon him the day he was born, and the day he will die, and the day he shall be raised.... Qur'an 19:30-34."  A tare suka kalli kofa da sauri jin an bude,  Ilham tayi tsaye bakin kofar tana kallonsu, mikewa yayi fuska daure yace "You re very stupid, baki da hankali xa ki shigo min parlor haka??" Fita tayi kamar xata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Mami ce tace in kira ka..." Yace "Get out!" Rufe kofar tayi ta wuce, Samantha da duk jikinta yayi sanyi ta kallesa tace "Saboda ni kayi mata haka?" Xaunawa yayi kan kujera fuska daure yace "No" ta mike cikin sanyin murya tace "Ohk xan tafi" tashi yayi da sauri yace "No but ae ba mu gama ba Samha" tace "Xa mu ci gaba next time, kaga ur mum is calling" d'an murmushi yayi yace "Alryt... Thanks for the food dear" murmushin ta mayar masa ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, komawa yayi ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera hade da lumshe ido, yafi minti goma a haka can ya mike jiki a sanyaye ya fita xuwa main house, sosai gabansa ya fadi ganin yakumbo, sae dae ya fuske ya xauna ya gaisheta tace "Sae yanxu ka ga dama kenan" ya shafa kai yace "A'a" Mami dae sae kallonsa take, Yakumbo tace "Toh ya maganar mu ta ranan, kasan dae kai ake jira ko?" Ta gefen ido ya kalleta yace "Ni ake jira kuma?" Yakumbo ta kalli Mami a fusace tace "Ki fa gaya masa don ya raina ku ni bai isa ba ne... Ni xae dinga ma tambayar walakanci?" Abuturrab yace "No ban gane xancen bane yakumbo." Buda baki tayi tana kallonsa, ita dai Mami uffan bata ce ba, Can ya mike yace "Kar ki damu Yakumbo xan kawo maki ita har gida ta gaishe ki, shknn dai koh?"
Washegari lahadi da yamma Abuturrab ya shirya don wucewa gun aiki, Yana rufe gate ya dawo xai shiga motarsa ya hangota tana tahowa, tsayawa yayi har ta karaso sanye take da Abayarta dake ta sheki tsabar iron, tayi Islam is peace da veil din abayar, bbu make up fuskarta sai eye pencil dake idonta da lip balm da ta shafa a pink lips dinta, amma ba karamin kyau tayi ba, tayi murmushi tace "Ina yini?" Yana kallonta yace "Lafiya! Ina xa ki?" Tace "Catechism yau Sunday!" Yace "Ohk shigo in yi dropping din ki" tace "Thought clinic xaka?" Yace "Yeah" ta langwabar da kai tace "Toh ae ba hanyar bane" yace "Idan xa ki shigo malama ki shigo" a hankali ta karasa ta bude motar ta shiga, shi ma ya shiga ya ja motar suka dau hanyar titi, ganin hanyar da ya dauka ta kallesa sai dai bata ce komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi ganin har sun wuce hanyar asibitin ta kallesa tace "Ina xaka kai ni Doctor?" Ba tare da ya dauke idonsa daga kan titi ba yace "Sayar da ki xan je in yi" bata ce komai ba, haka ya dinga tafiyarsa, ji yayi ta fashe da kuka, ya d'an saci kallonta yayi murmushi yace "Toh ae ba kuka ya kamata kiyi ba, you are supposed to be reciting ur last prayer...." Cikin muryar kuka tace "Ni dai ba wasa nake ba ka ajiye ni in koma gidanmu" yace "Ke da gidan ku kuma har abada..." Ta kuma fashewa da kuka, wani anguwa suka shigo basu wani shiga ciki ba yayi horn a bakin wani gate ba a dau lkci ba mai gadi ya leko ya bude gate din snn ya shigar da motar compound din, yana gama parking, ya kamo hannunta ta fixge, yayi murmushi yace "Yanxu kin yadda xan sayar da ki" hararansa tayi tace "Baka yi kama da wanda xai iya saida Bird ba bare ka saida mutum just that you didn't tell me you are taking me this far nayi xaton asibiti xa mu je" sai kuma ta fashe da kuka sosai, jawota yayi jikinsa yace "Ohk am sorry plsss, ba jimawa xa muyi ba, gidan mum dita ne nan...." Turasa tayi da mamaki tana kallonsa tace "Mum?" Yace "Yeah, my mum sister" ta fashe da wani sabon kukan tace "Ni dai ba ruwana ka kai ni titi in hau tricycle in koma gida" yace "Ohh she's nyc, and she will love seeing you, bata da matsala" bai jira cewarta ba ya ciro handki ya fara share mata hawayen idonta, daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata kofar ya fito da ita. Bbu kowa parlorn ya sa ta xauna kan kujera snn ya tafi dakin Mum, Hajiya Mariya dake gyaran kayanta a closet tana kallonsa da mamaki tace "Aliyu, daga ina haka?" Yace "Gida Mum" tace "Ikon Allah, sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh, da bakuwa muke" bai jira cewarta ba ya fita, sai ga ta ta biyosa, tun bata iso parlon ba take kallon Samantha har ta iso, Samantha ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Murmushi dauke fuskar Hajiya Mariya tace "Sannu da xuwa bakuwa" Samantha bata iya ta kalleta ba ta xamo kasa a hankali tace "Ina yini Mumy" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau, ya hanya?" Kasa cewa komai Samantha tayi, Hajiya Mariya ta xauna tana kallonta tace "To koma kan kujeran mana" bata dago ba bata kuma ce komai ba, Abuturrab yayi murmushi yace "Mum meet Samantha.... But I do call her Samha.." Hajiya Mariya tace "Ohh maa sha Allah, but this Samha is too shy, taki xama kan kujera" Yace "No she's comfortable there" Hajiya Mariya tace "A'a ni ba ruwana ta koma kan kujera" daga nan ta mike ta nufi fridge don dauko masu drink, kallonta yayi yace "tashi koma kan kujera" bata kallesa ba bata kuma tashi ba, ya mike yace "Toh bari in daga ki" da sauri ta koma baya tace "No bana so ka bari plss" kamar xata yi kuka tayi maganan, ya wara ido yace "Toh kuka xa ki min?" Kin cewa komai tayi, Hajiya Mariya ta dawo parlon da ruwa da lemo ta karasa kusa da ita ta ajiye tana kallonta tace "Yanxu baxa ki hau kujera ba bakuwata" girgixa kai kawai tayi, Haka kawai Hajiya Mariya taji ta burgeta a xuciyarta kuwa tunani take wnn din ce Christian din da Abuturrab ke fadi mata, kitchen ta koma ta xubo masu fried rice din da tayi, ganin ynda Samantha taki sakin jiki ta bar masu parlon, tana wucewa ta dago kamar xata yi kuka tace "Doctor plss mu wuce" ya hade rai yace "Gidan Mum dita ne nn fa" tayi shiru bata ce komai ba, ba karamin takurata yayi ba ta ci abincin shi ma kadan, hade rai yayi ya sauko kasa ya karbi spoon din ya debi abincin ya kai bakinta, kamar xata yi kuka tace "Doctor ka bari plss" dafa forehead dinta yayi ta bude bakin da sauri ya xuba mata ya kai sauran baki, sunkuyar da kanta tayi tana taunar abincin a hankali, can ta kallesa a hankali tace "Doctor  wllh na koshi" yace "Me kika ci?" Tace "Pounded yam and vegetable" yace "Shine baki kawo min ba?" Ta wara ido tace "Kana so?" Yace "Ehh mana" ta langwabar da kai tace "Toh xan maka" mikewa tayi tace "Kitchen fah?" Ya nuna mata hanyar kitchen ta dau tray din abincin ta nufi can, mikewa yyi ya shiga bedroom din Hajiya Mariya. Tana shiga kitchen taga kayan wanke wanke a hade cikin sink, liquid soap ta dauka da sponge ta hada ruwan kumfa ta fara wanke su, cikin kankanin lkci ta gama don bai da wani yawa, ta tsaftace kitchen din ta goge har Gas snn ta dau sweeper ta fito parlor, Abuturrab ya xauna gefen Mum din sa dake waya har ta kare wayar snn ta kallesa tace "Ita ce yarinyar Aliyu?" Kai ya gyada mata, ta girgixa kai tace "She's cool and pretty, kuma bata yi shige da yare ba kamar bafulatana, and kamar ba Christian ba" murmushi yayi yace "Abbanta bafulatani ne ae...." Shiru Hajiya Mariya tayi, can tace "Allah sarki.... Toh yanxu ta yarda xata yi converting din ne?" Xaro ido yayi yace "Mumy ni fa bamu taba magana irin wanda nake maki da ita ba...." Da mamaki tace "Kana nufin bata san kana sonta ba?" Shiru yyi sai kuma ya girgixa kai a hankali yace "Ko ma ta sani bata taba nuna ta sani ba" Hajiya Mariya tace "Toh fah, then it's better ka fadi mata soon as possible kaji ra'ayinta" ya lumshe ido yace "Ohk mum" 'yan shawarwari ta basa sannan tace ya tafi parlor ya bar ta ita kadai, mikewa yayi ya fita, xaune ya sameta idonta na kan tv, ya karaso ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Sae bayan magrib xa mu tafi koh?" Ta dago da sauri ta kallesa xata yi magana sai ga Hajiya Mariya wanda hakan yasa tayi shiru, Hajiya Mariya tace "Sannu my daughter, mun bar ki ke daya koh?" Murmushi Samantha tayi bata ce komai ba, ya kalli agogo yace "Mumy xa mu wuce...." Tace "So early?" Yace "Mun dade fa Mumy" tace "A'a ba wani dadewa" daki ta koma ba a dau lkci ba ta fito rike da leda ta mika ma Samantha tace "kiyi hakuri bbu yawa kin ji...." Da sauri ta girgixa kai tace "A'a nagode Mumy" Mumy ta mika ma Abuturrab tace "Toh gashi ka bata tunda kunya ta take" har mota ta rakasu sai da suka fita sannan ta koma ciki, a hankali yake driving din, can ya juya ya kalleta, idonta na waje tana kallon titi, kamo hannunta yayi ta juyo tana kallonsa, ya murza fingers dinta yace "Kin san me?" Janye hannunta take son yi ya ki saketa, murya can kasa  yace "My mum.... Kinsan me tace?" Kallonsa ta sake yi snn tace "A'a" murmushi yayi murya can kasa tace "Wai tana son ki, she likes you, how she wish you were a Muslim sai ki xama in-law dinta" murmushi tayi ta kwace hannunta bata ce komai ba, yace "Kin yi shiru" wara ido tayi tace "Uhm and unfortunately am not a Muslim"

*Haske Writers Asso*📚✍🏻  sorry for the delay!

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now