part 26

1.7K 58 1
                                    

💫 *Noorul Huda*💫

26.....

Karfe goma da kusan rabi Abuturrab na kofar gida zaune yana danna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, sosai gabansa ya fadi da kamar baxae dauka ba sae kuma ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Abba yace "Kana ji na, ka taho gida yanxun nan am waiting for you, i mean immediately!" kasa cewa komai yayi jikinsa yayi sanyi sosai, yayi karfin halin mikewa ya shiga gida, xaune ya samu Hajiya Mariya parlor hannunta rike da Hisnul muslim, ya isa gabanta ya durkusa yace "Mumy wai kin ji Abba in xo, ni nasan all is not well tunda har hankalina yaki kwanciya" ita kanta sae da taji hankalinta ya tashi, ya girgixa kai ya daura kansa a kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ni baxan iya rabuwa da ita, ban san irin son da nake mata ba..." Dago kansa tayi taga hawaye idonsa, wanda hakan ya bata mamaki sosai anya ma ita ta taba ganin hawayensa, ta girgixa masa kai tace "Be a man Aliyu, ko kaje yanxu just show you know nothing about her whereabout, ni kuma in'sha Allah i will take care of her a nan, baxan bari taje ko ina ba, tashi kaje tunda yace yana jiran ka" mikewa Abuturrab yayi jiki ba kwari ya fita, har ya isa gida gabansa bae daina faduwa ba, kallon motar yan sandan dake bakin gate har lkcn ya dinga yi, can ya dake ya fito ya rufe motarsa ya shiga gidan, ko kallon yan sandan dake tsaye tsakar gidan bai yi ba ya nufi inda ya hango Abbansa dake tsaye sanye da uniform da gani kasan saukansa knn, Mami na tsaye daga gefensa Ga Mumy da tawagarta da alama shi dae ake jira, yana isa kuwa Abba ya sauke masa lafiyayyen mari ya sunkuyar da kai ya kasa dagowa,  cikin tsananin fushi Abba yace "Ina ka kai yar mutane?" Da sauri ya dago yace "Yar mutane kuma Abba" komawa baya yayi ganin Abba xae kuma marinsa, ya xaro ido yace "Bbu wata yarinya dake gu na Abba, gun aiki na fita, i know nothing about any girl...." Cakumosa Mumy tayi cikin tsananin fushi tace "Karya kake munafuki algungumi, gashi har ka koya ma 'ya ta karya, na rantse maku yasan inda take, don haka ya fito mun da ita idan ba haka ba a tada Nigeria, bbu ruwana da waye ubanka, ku fito min da yarinya ta....." Cikin kuka sosai ta kare maganar ta sake sa ta daura hannu a ka tace "Na shiga uku na lalace" Abba ya dinga yi ma Abuturrab wani kallo, Mami kam banda hawaye bbu abinda take, kasa kallon inda Mr David ke tsaye rungume da hannunsa Abuturrab yayi, cikin sanyin murya yace "Abba sharri ake son min, i know nothing about all this, toh ina xan kai yar mutane, xa a iya shiga ciki a duba ko tana nan..." Turasa Mumy tayi tana huci tace "Yesu! Kai baka jin kunyan karya ne, ina ce jiya birthday ka ja ta ku ka je, ina ce jiya ka bata zobe wae zaka aureta, ka mance hanyar jirgi daban ta mota daban, meye ya hada warce ta fito from a very good Christian home da musulmi, bbu hadin ku don haka ka fito min da 'ya ta idan ba haka ba in kashe ka har lahira!" Wani kallo Abuturrab yyi mata yace "Ni xa ki kashe kuma?" Girgiza kai yayi yana kallon 'yan sandan dake tsatstsaye yace "Ko da maganar nan xae kai mu kotu ku xaku xame min shaida kashe ni tace xata yi." Abba ya kalli sojoji uku dake tsaye gun yace "Ku saka min shi a guard room, ko ba shi ya dauketa ba sai ya fadi inda take, idan kuma yaki ba sae ta kashe sa ba ni xan harbe sa...." Ta gefen ido Abuturrab ya kalle sojojin kawai ya tafi kai kansa Guard room din kafin ma su nufo sa, Cikin tsawa Abba yace "Ku bi sa ku sa shi nace" Daga haka ya nufi yan sandan dake gun, Mumy ta watsa ma Mami wani kallo tana hawaye tace "Amma kin haifa ma kanki jaraba, don wnn d'an naki annoba ne a gari...." Vivian ta ja hannunta suka yi waje tana rusa kuka.  Har bayan azahar Abuturrab na guardroom daga shi sae singlet da dogon wando, bai wani damu ba don sbda shi ma aka yi guard room din a gidan, don haka inda sabo yaci ace ya saba, ko d'an shekara 15 aka saka a gun sae yaji jiki tsabar k'ankantar gun ga uban zafi, ko kwakkwaran motsi bae iya yi, a takure yake waje daya kansa ma baya iya dagawa straight sae a duke, tun bai kai sha biyar ba Abba ke jefasa nn idan yayi laifi kuma sae yafi awa biyar a haka, rabonsa da guard room tun yana 27 yrs wato 3yrs back da ya dauko wani maganan, karfe uku yaji an bude kofa daga waje, ko ba a gaya masa ba yasan Mami ce don ita kadae ke xuwa idan aka kullesa, ae ko ita ce, ta durkusa ta bude karamin kofar da yake ciki da aka sa ma uban kwado, da ganinta kasan ta ci kuka, kamar jira yake tana budesa ya fito duk ya jike jagab da gumi, kasa kallon idonta yayi, ya dafa gwiwansa kansa a sunkuye don gaba daya jikinsa yayi tsami, ga wuyarsa da ya rike, muryarta yaji tace "Aliyu ina 'yar mutane" bai d'ago ba kuma bai ce komai ba, can dai ya dago da kyar jin tayi shiru, tausayinta yaji sosai shi dai yasan tun da kwakwalwarsa ta fara aiki irin na mutane rabon Mami da samun kwanciyar hankali, ko da yaushe cikin dauko magana yake ba babba ba ba karami ba kuma a kanta komai ke karewa don Abba cewa yake ita ta 6ata shi, kwanan nan ne ma abun ya lafa bayan ya fara aiki don ko lkcn yana sch hankalin iyayensa ba a kwance yake ba, kamar xae yi kuka yace "Mami ni fa ban san komai kan maganar nan ba sae xalina ake ci kawai!" Hawaye ya gani idonta ya xube nan kasa yace "Noo Mami don Allah kiyi hakuri...." Dakewa tayi tace "Ina yar mutane take Ali?" Shiru yayi kafin ya dago a hankali ya goge xufar dake fuskarsa yace "Mami...." Sai kuma yayi shiru, sauke idonsa kasa yayi yace "Tana nan!" Mami ta durkusa gabansa ta dago kansa tace "A ina?" Kallonta yayi murya can kasa yace "Mami.... Mami ita nake so and i want to convert her...." Komawa baya Mami tayi da mugun mamaki tana kallonsa kamar idanuwanta xa su fito, cikin rawar murya tace "Aliyuu!" Marairaice mata yayi yace "Mami ni idan ban aureta ba Allah xan iya mutuwa wllh, i will be nothing without her" hawaye ne ya cika idonsa, wanda rabon ta da ganin hakan tun yana d'an shekara goma, ko me xaka yi masa baxa ka taba ganin hawayensa ba sai dai idonsa yayi jajir kirjinsa yayi ta sama da kasa tsabar dacin rai da rashin ji irin nasa, ya daura kansa a jikinta muryarsa na rawa yace "First love support me plss, i love her, ni baxan iya rabuwa da ita ba, kuma Mami idan na musuluntar da ita lada xan samu fah..." Hawaye kawae Mami take duk jikinta yayi sanyi, ita kam tana ganin jarabawa tun da ta haifi Aliyu, ta saita kanta cikin sanyin murya tace "Toh tana ina?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Tana gidan Mumy!" Da mugun mamaki tace "Mariya?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta sauke ajiyar xuciya a hankali, jin tayi shiru ya dago da sauri yace "Mami plss kar fa ki ce ma kowa haka, don Allah kar ki fadi Mami...." A rude ya kare maganar, cikin kwantar da murya tace "Ka gwammace kayi ta shan wahala knn, to ai shknn, shiru xan yi da baki na idan ma ya kashe ka kai ka ja ma kanka, tashi ka shiga ciki kafin a ganmu dama cewa yake ni ke supporting din ka" kallon d'an kurkukun yayi kafin ya marairaice yace "Mami k'ishi nake ji sosai wllh" mikewa tayi tace tana xuwa snn ta fita, ya fi kowa sanin halin Mami yasan wannan duk pretending take masa, ya kalli bunch of keys din da ta ajiye nan kasa bayan ta bude sa, ya dauka da sauri ya cire biyu ya tona kasa ya boye a cikin d'an room din, yana nan durkushe yana yi yana lekan sojoji biyun dake tsaye waje har ta dawo ya sunkuyar da kansa da sauri, Ruwan babban gora me sanyi ta kawo masa da Hollandia yoghurt, sae dambun nama cike a plate tace toh tashi ka shiga kafin ya yo nan, karban ruwan yayi ya sha kusan rabi, Key din dake ajiye kawae take kallo can ta dauka tana weighing dinsa ta kallesa strictly tace "Ka cire key a nan bani!" Da sauri yace "Key kuma Mami" wani kallo tayi masa tace "mike tsaye" yana tashi ta sa hannu aljihunsa ta dudduba taga babu, ta leka guard room din ma bata ga alamar key ba tace "Toh shiga ciki" ya ajiye ruwan hannunsa fuskar nan tasa kamar xae yi kuka ya durkusa ya shiga ta tura masa abubuwan da ta kawo snn ta rufe gun da kwado ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita. Ko minti goma ba ayi da fitarta ba yasa key ya bude gun a hankali ya fito, ya dau shirt dinsa dake rataye gun ya kakkabe ya saka snn ya saka takalmansa ya nufi kofa da sauri, lkci daya ya banke kofar ya fice a dari da sittin kafin sojojin su ankara, ae ko suka bi sa da gudu, gudu yake kamar jirgi xae tashi sama, wani soldier ya ciro whistle a aljihunsa ya dinga hurawa, ae ko sae ga sojoji har uku sun fito, Abba ma ya fito balconynsa a sama ya rungume hannu da mugun mamaki yana kallon Abuturrab, komawa yayi don dauko bindigarsa amma kafin ya dawo tuni ya isa gate da karfi ya finciko mai gadin sojan dake bakin gate yana kkrin datse gate din ya wani wurgar da shi ya fixgo gate din ya fice, gudu kawai yake kamar xae tashi sama, wanda hakan ya tsorata mutane duk suka fara gudu su ma, ko kallonsu bai yi ba har ya iso titi ya tsayar da mai adai daita bai jira ya tsaya ba ya afka ciki yace "Mu je muje da sauri....." Mai adai daita ya ja machine dinsa da sauri don shi ma ya tsorata, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ya share xufar fuskarsa ya bude button din riga.

*Haske writers asso*📚✍🏻  It's Khaleesat Haiydar👌🏻

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now