part 12/16

2.3K 55 0
                                    

[8/9, 2:10 PM] Ummey Zee Abakson: 💫 *Noorul Huda*💫

12___13
Hade rai yayi ya xauna Mami dake kallonsa tace "Ya aka yi Aliyu?" Kin cewa komai yayi Ilham da khaleesat suka yi lamo jikinta, lkci daya duk ya jefa masu wani arnen kallo ya mike kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin kamar xae tashi sama, Mami ta kallesu tace "Kun nemi tsokanarsa koh?" Ilham ta turo baki tace "Ba abinda muka yi masa" har magrib su ilham basu yarda sun bar dakin Mami ba, nan ta tabbatar ba karamin laifi suka yi ma yayan nasu ba, bbu yanda bata yi da su ba su fadi me suka yi masa suka ki magana, har part dinsa Mami taje bayan Isha ta shiga har bedroom dinsa ganin baya parlor ta gansa xaune gefen gado hannunsa rike da waya, karasawa tayi tana kallon kofar bathroom jin k'aran washing machine, ya ajiye wayar hannunsa yace "Mamina...." Mami tace  "dama akwai washing machine a nan?" Yace "Ehh akwai...." Tace "Wanki kake?" Yace "No, just singlets..." Xaunawa tayi tace "Laifin me su ilham suka maka ne wai?" Ya shafa kansa yace "Ya wuce Mami...." Mami ta tabe baki tace "Toh ku kuka sani, naga tun daxu baka shigo ba" yace "Ehh Mami dama yanxu xan shigo" tace "Ohk, toh xan samu a d'an siyo min fruit?" Ya kalleta yace "Toh Mami" mikewa tayi tace "kar ka siyo lemo just apples, grapes and watermelon" yace "Toh Mami, yaushe Abba xai dawo" tace "Baka da numbersa ne?" Murmushi yayi tace "Atoh" daga haka ta nufi kofa ta fita, mikewa yayi ya shiga bathroom ya kashe machine din ya fito da har xai dau makulin mota ya fasa don bbu wani nisa ya dau kudi kawai ya fita, kamar bai son tafiyar yake yi, duk bai da sukuni, yana isa bakin hanya dai dai gun masu saida fruits yayi xaman sa har sai da aka tambayesa mai xai siya, ya kalli mutumin ya gaya masa, wata mota ce tayi parking dai dai gun, ya dinga kallon motar har aka bude, gabansa ya fadi ganinta ta fito, bata ko lura da shi ba ta taho gun mai sayar da fruits din, mikewa yayi yana kallon cikin motar yana son sanin ita da waye, ido hudu yayi da Mum dinta da ta hakikince bayan mota, da ganinta kasan daga church suke, dauke kai yayi ya taka xuwa gun mai fruit din da har ya gama xuba masa nasa a leda yana xuba mata nata, kallonta kawae Abuturrab yake ganin mood dinta kamar mara lafiya yasan kuma tun abun da ya faru daxu ne, lkci daya kamar ance ta juyo ta juyo, kasa daina kallonsa tayi sae shi ne ya dauke ido sanin uwarta baxa ta rasa kallon su ba, ai ko kamar ya sani kallon nasu take kamar idanuwanta xa suyi magana, xagawa yayi ya dau ledan fruits dinsa ya sa hannu aljihu ya ciro kudi hade da wayarsa ya d'an saci kallon uwar ta yaga fa har lkcn kallon direction dinsu take, yi yayi kamar xai mika ma mai fruits kudi, ya tsaya daga bayanta cikin dubara ya kamo hannunta ya saka mata wayarsa a ciki, snn yayi saurin mika ma mai fruits kudinsa ya juya ya bar wajen, ita kanta jikinta ya bata mum dinta na kallon gun duk ta tsorata kada ace taga sanda ya bata waya, tana karban ledan fruits din tayi saurin jefa wayar a ciki ta basa kudinsa sannan ta juyo ta nufi gun mota, tana shiga motar mumy ta jefo mata tambayar da ya tsorata, "Samantha kin san wannan mutumin ne?" Cewar mumy kenan tana kallonta ido a zare, Samantha da Gabanta ya shiga  faduwa tace "Wani mutum mumy?" Uwar tace "Wanda ya siya fruits yanxu" Samantha ta girgixa kai da sauri amma bata ce komai ba don bata iya karya ba, cike da masifa uwar tace "Karya kike, I saw the way he was looking at you, ina raba ki da non believers din nan baki ji ko, meye hadin ki da musulmi?" Hawaye cike idonta tace "Kiyi hakuri Mumy...." Wani tsawa tayi mata tace "Sorry for ur self, stupid girl kawai, ina cross din wuyar ki, Kin kara cirewa koh?" Hawaye cike idonta tace "Na mance shi gaban mirror" har suka isa gida masifa Mumy ke mata, Ta kankame ledan fruits din Don tasan kashinta ya bushe idan ta karbi ledan ta ga waya, a dinning ta ajiye ledan tayi saurin ciro wayar ta boye a rigarta ta wuce sama da sauri. Misalin sha daya tana durkushe gaban gadon ta hade hannayenta biyu idonta lumshe tana addu'a xata kwanta taji vibration din wayar a karkashin pillow da ta ajiye, mikewa tayi da sauri ta isa gun kofa ta sa key snn ta dawo ta dau wayar, number ne bbu suna, a hankali ya daga ta kai kunne, daga daya bangaren taji ance "Hellow frnd!" Murya can kasa tace "ina yini" yace "Lafiya lau, baki yi bacci ba?" Ta gyada kai kamar yana ganinta tace "xan yi yanxu" cikin sanyin murya yace "Ohk, am sorry dear for what happened in the afternoon, plss Kiyi hakuri...." Da sauri tace "Ae ya wuce" yace "No nasan it's still touching you, for my sake kiyi hakuri don Allah" hawaye ya cika idonta a hankali tace "I've already forgiven and forget.... My religion prohibit us from not forgiving, cause we are also being forgiven by the almighty God" ya lumshe ido yace "Ohk my dear, thanks much, ya daren?" Tace "It's nyc..." Yace "Good, gobe xa ki sch koh?" Tace "Ehh" yace "Toh sai da safe...." Da sauri tace "Toh ina xan baka phone dinka?" Yace "No, na baki so that xan dinga jin muryar ki" murmushi tayi tace "Muryata kuma?" Yace "Yeah dear, ur sweet voice..." Xaro ido tayi, tayi dariya tace "Ni ba ruwana, byee" murmushi yayi ya lumshe ido jin dariyarta, cikin sanyin murya yace "Ohk dear, sleep tighttt" a hankali tace "Thank you...." Daga haka ta katse wayar, kwanciya tayi tana kallon wayar kirar Infinix, ganin a bude yake ta shiga gallery, hotunan sisters dinsa ta fara cin karo da, gabanta ya fadi sosai tana kallonsu, A hankali ta dinga wuce su, yawanci duk hotunansu ne, sai na mami tana gani kuma ta gane mum dinsa ce sbda kamar da ta gani, wani hotonsa ta gani yana sanye da white Coat dinsu na likita, wuyarsa sakale da stethoscope fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, sosai hoton yayi kyau, pink lips dinsa ta tsura ma ido, lkci daya incident din ranan ya fado mata gabanta ya fadi sosai, da sauri ta wuce hoton, haka tayi ta kallon hotuna har suka kare, ta lumshe ido daga haka bacci ya dauketa wayar na kwance kirjinta. Washegari da asuba vibration din wayar ne ya tada ta, mikewa xaune tayi da sauri, ta jawo wayar tana kallo taga number jiya ne, a hankali ta d'aga ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "still sleeping" murya can kasa tace "Na tashi" yace "Noo na tashe ki dai" murmushi tayi yace "Alryt, na dawo mosque shine nace bari in tashe ki duk da nasan bbu abinda xa ki yi....." Tace "Xan yi addu'a mana" yace "Wani addu'a?" Tace "Wanne kai kayi yanxu?" Yace "Sallah naje masallaci nayi mana" tace "Toh nima yanxu xan yi nawa addu'an" ya tabe baki yace "Toh ayi addu'a lfya" tace "Ohk thank you..." Katse wayar yayi ya ajiye yana girgixa kai. Mikewa tayi ta durkusa jikin gadonta ta hade hannayenta ta lumshe ido, ta kusa minti goma a haka kafin ta mike ta shiga bathroom ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta fito, bata 6ata lkci gun shiryawa cikin uniform dinta ba ta fito ta shiga dakin mumy ta ganta xaune kan study table dinta idonta sanye da glass bible a gabanta, karasawa tayi tace "Ina kwana Mumy" Mumy ta rufe Bible din tace "Lafiya lau, kin yi addu'a?" Ta gyada kai tace "Nayi" Mumy tace "Yaushe ne waec din naku?" Tace "Ba na gaya maki ba, it's on Monday" Mumy tace "Good, kina karatu dai koh" tace "Ina yi Mumy" daga haka ta fita, sai kusan takwas da rabi ta bar gida don revision kawai suke a sch, a motar gidansu xa a kai ta sch din, suna isa layin gidansu Abuturrab sai ga shi shi ma ya fito da mota, bai yi gigin hawa kan titi ba ya jira su fara wucewa, gaba daya ya tsura ido ya ga Inda xai ganta cikin motar, dama ita ma tun daga nisa ta hangosa, a hankali ta sauke glass har suka iso dai dai gate din, ta wara ido hade da d'aga masa hannu, kashe mata ido daya yyi, ta xaro ido hade da toshe baki kar tayi dariya, haka ya bi motar da kallo har suka wucesa, ya lumshe ido ya karasa motarsa ya shiga ya dau hanyar gun aiki,
Tun daga ranan basu sake haduwa ba, bai kuma damu ba don ko da yaushe cikin waya suke, ita kuwa kwata kwata ta daina bin hanyar gidansu don ma kada su hadu, ta gwammace taje ta xagaya duk da nisan tafiyar don ita tsoron sisters dinsa take, a haka har suka fara waec. Ta fito daga wanka knn bayan ta dawo daga 3rd paper dinta, tana tsaye gaban mirror tana goge dogon gashinta don karkashin shower tayi wankan kuma bata rufe gashin ba, vibration din waya taji ta koma gun gado ta dau wayar, d'agawa tayi ta kai kunne hade da langwabar da kai, daga daya bangaren yace "How was the paper?" tace "Uhm yayi sauki...." Yace "Upon the runs?" Wara ido tayi tace "No, ni ban Karba ba" yace "Alryt, me kike yi yanxu?" Tace "Wanka nayi...." Ya d'an yi shiru sannan yace "Ohk, kin ci abinci?" Ta girgixa kai tace "Nobody is at home, yanxu xan girka" yace "Me xa ki dafa?" Ta yi shiru kamar me naxari sannan tace "Kila in dafa indomie" yace "Uhm nima xan ci" ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Indomie din?" Yace "Yeah, am very hungry, no body is at home here also" tace "Eyya, kuma baka iya girki ba koh?" Yace "Eh mana, but gashi xa ki yi mana ae" murmushi tayi tace "Da gaske zaka ci?" Yace "Ehh mana am jet serious..." Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Ohk, toh wa xai karbar maka?" Yace "Oh baxa ki kawo min ba" shiru tayi sai kuma tace "A'a ka dai xo ka karba" yace "Toh shknn just leave it" tace "Ka fasa ci?" A takaice yace "Ehh" tace "Ohk toh" katse wayar yayi, tayi murmushi, ta karasa goge jikinta ta shafa lotion ta fito da abayar ta red and black ta sa, ta daure kanta da dankwali ta feshe turare ta fita, irish ta shiga ferewa cikin kankanin lkci ta gama ta soya, snn tayi sauce din hanta, tuni kamshi ya bade gidan ta xuba su a warmer ta tsaftace kitchen din ta fito, abincin ta dauka ta fita ta kulle gidan don tasan sae bayan isha mumy xata dawo daga service, tun fitowarta gate dinsu gabanta ke faduwa tunawa da su Ilham da tayi, amma cewa da yayi babu kowa gidan yasa hankalinta ya d'an kwanta, ba karamin karfin hali tayi na tura gate ba ta shiga bayan ta isa gidan, a hankali ta rufe gate din, ta nufi kofar parlor da sauri, ta murda kamar me tsoron handle din ta shiga snn ta rufe, kwance ta gansa kan doguwar kujera singlet da short nicker kadai ne jikinsa, k'in karasawa tayi ta ajiye abincin hannunta tana kirkiran murmushi tace "Uhm gashi na kawo ma, xan wuce...." Mikewa xaune yayi yana kallonta, can ya mike ya isa Inda take, ta sunkuyar da kai kamar munafuka, ya fi minti daya yana kallonta, snn a hankali ya kai hannu ya tsinke Rosary din wuyarta, ta dago da sauri mamaki dauke fuskarta tana kallonsa sai dai ta kasa cewa komai, ganin yanda ya tsareta da brown eyes dinsa still yasa ta sauke idonta a hankali, dago kanta yayi xae yi magana suna hada ido ya kasa cewa komai, da sauri ta sake sunkuyar da kanta ta juya xata bar wajen, ya jawota xuwa jikinsa murya can kasa yace "I....i missed you" kasa cewa komai tayi, ya hade fingers dinta da nasa hakan yasa ta dago a hankali, lumshe ido yayi ya daura warm lips dinsa a forehead dinta, da sauri ta rufe idonta, a hankali ya dinga gangarowa da bakinsa har kan hancinta sannan lips dinta, lkci daya ta rike breathe dinta, ya jinginar da ita jikin kofa ya lumshe ido ya hade bakinsu, bai saketa ba har sae da yayi me isarsa, ko ina na jikinta 6ari yake, yana xame bakinsa daga nata kuwa ta juya da sauri ta fice, bin bayanta yayi da rinannun idonsa ya datse gate din, hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa tace "Ka bude min kofa" hannunta xai kama ta koma baya da sauri, xai matsa kusa da ita ta fasa wani ihu da yaji har tsakiyar kansa, bai san lkcn da ya bata hanya ta fita ba.   Washegari Abuturrab na xaune parlon Abbansa, fuskarsa ba walwala yana sauraren yakumbo, can dai ya d'aga kai ya kalli Abba ya ga kallonsa yake, sauke kansa yayi, a fusace yakumbo tace "Ya xaka min shiru Ina maka magana Aliyu...." Ya gyara xama yace "Naji Umma, sai dai ni bana son auren xumunci...." Mikewa tayi tace "Ae ko ya xama dole ka so auren xumunci tunda ka kasa fidda mace ka aura.... Kayi xaton Umar so yake nuna maka da ya bar ka kake ta shashancin ka kaki ajiye iyali, ni ban taba ganin irin haka ba, wai xamani ya xo yanxu sai ka ga d'a namiji yana xaune gidan iyayensa yaki aure wae sae ana tilasta shi sai kace ba ribar sa bace, kai baka san gata ake maka ba koh?" A takaice yace "A bani yan kwanaki xan xabi matar aure, bani da ra'ayin na xumunci..." Tabe baki tayi tace "Ae shknn fitsararre, amma ka sani in dai bata da qualities din xama surkar mu wllh sai dai ka mutu, auren xumunci ba fashi..." Bai ce komai ba sai dai da ganinsa kasan he's boiling from inside, mikewa yayi ya dake yace "Toh shknn" tace "Ehe, kuma sati uku na baka...." Bai tanka ta ba yayi ficewarsa, ta kalli Abba tace "kasan me yasa nake son ganin Aliyu yayi aure Umar?" Abba ya kalleta yace "A'a yaya" ta koma ta xauna tace "Saboda 'yan adawar mu, masu maka gorin rashin 'ya 'ya maza, in sha Allahu sai Ali ya cika maka gida da jikoki maza....." Abba ya girgixa kai hade da murmshi  bai ce komai ba sanin ba kowa take nufi ba banda 'yan ubansu...."   Yakumbo yaya ce ga mahaifin Abuturrab don daga ita sai shi, kuma ta basa shekara daddaya har tara, su uku ne gun iyayensu, sai yan uba rututu, autarsu Maryam tana aure a Cairo, iyayensu gaba daya sun rasu tun kafin Maryam ta cika shekaru shidda yakumbo kuma tayi aure lkcn, bayan rasuwar mahaifansu ta maido da kannin nata gabanta duk da ba wani karfi gare mijinta ba a lkcn ga kuma 'ya yanta maza biyu sanin idan ta bar su gun kishiyar uwarsu wahala xa su sha, don hatta iyayensu ba wasu masu shi bane, ita kuma stepmum din tasu bbu laifi tana da abun hannunta don iyayenta suna da rufin asiri, ita kuma 'ya 'yanta takwas da kakansu Abuturrab, bata damu da 'ya yan mijin nata ba haka suka ta xama gidan yayarsu yakumbo (Fatima) har xuwa lkcn da kowa ya kama gabansa, 'ya yan yakumbo biyar duk maza sai autar ta Sumayya, manyan maxanta biyu duk sun yi aure, sae na ukun yanxu da take son a hada aurensa da na Abuturrab, Maryam kuma 'ya yanta uku, 'yan biyu maza sai autar ta khadija, sosai yakumbo tayi fafutuka kan makarantar Mahaifin Abuturrab don lkcn yana shekarsa ta biyu a jami'a Abbansu ya rasu don Mahaifiyarsu ta riga sa rasuwa, cikin ikon Allah Abban Abuturrab na gama karatun ya tafi NDA da taimakon mijin yayar tasa, bayan shekara daya ya samu aiki as a militant duk ta damesa sai da yayi aure, ya auri Mami (Hajarah) bafulatana kuma marainiya kamarsa, sun kuma hadu ne lkcn da yake service a Adamawa, bai shekara biyu da fara aiki ba Mami ta haifo masa d'an sa na fari Abuturrab a wnn shekaran kuma Allah yayi ma Mijin yakumbo rasuwa a hatsarin mota, sosai Abban Abuturrab yake kula da yayar tasa duk da 'ya yan ta duk sun riga sa fara aiki, promotions sosai ya dinga samu gun aiki sbda iliminsa da kwazo, sai gashi kafin shekara biyar ya xama babban soja Wanda hakan ya d'aga hankalin step members dinsu, Mami bata sake haihuwa ba sai Abuturrab na da shekara tara ta haifi Ramla a lkcn kuma Maryam ma ta haifi yan biyunta maza, autarta kuma sa'ar khaleesat ce, Yakumbo mace ce mai fada da isa ga masifa shi yasa ko kadan basa shiri da Abuturrab, kwata kwata bai son xuwanta gidansu, gashi duk abinda tace da Abba shi xae yi, baya taba tsallake magananta, iyakar biyayyar da xai ma mahaifiyarsu yake mata, a fusace ya shiga bedroom din Mami ta bi sa da ido har ya xauna, ganin ya ki cewa komai Mami tace "Ya aka yi?" Kamar xai mata kuka yace "Mami wai meyasa yakumbo take ma mutane haka ne, ni fa wllh tana cin darajar Abba da wataran sai munyi dauki ba dadi da ita...." Ta hararesa tace "Toh ka je yanxun ma kuyi mana tunda ka isa...." Marairaice mata yayi yace "Ba haka Mami ba ji fa wai maganan auren xumunci take min, kuma nasan kila tace da fitsararrun yaran yaya Khabir koh yaya Munnir xata hada ni, (Manyan mazan yakumbo)" Mami ta tabe baki tace "Wannan kuma kai ya dama.... Da baka tsaya ruwan ido ba ae da yanxu kayi auren ka, toh wai ina ya matan da kake bani a waya muke gaisawa?" Dariya yayi yace "Kai Mami ba wani ruwan ido fah, wa ennan kuma ae ba sonsu nake ba, kawayena ne kawai" ta tabe baki tace "Toh me kawaye, ae kuma sai kasan yanda xa ka yi" Mikewa yayi yace "Ke Mami baki taba neman min solution sai dai ki yi ta fito da faults dina, any way xan tafi gun Momma na anjima nasan she will surely find a way out for me" daga haka ya fita ta bisa da kallo tana murmushi.

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now