part 10/11

2K 65 0
                                    

[8/9, 2:09 PM] Ummey Zee Abakson: 💫 *Noorul Huda*💫

10....

Karasowa tayi xata xaga ta bayansa ya maza ya juya ya turata kan gado ta fadi, kafin ta juyo har ya fice ta mike da sauri ta bi sa, a stairs ya kusa cin karo da Ramlah ta je hado ma Mami tea, ya boye rigar a bayansa da sauri, tace "What are you hiding...." Bai tanka ta ba ya sauka ta bi sa da kallo sai ga Khaleesat da gudu tace "Sis meye hannunsa?" Ramlah ta buda hannu alamar bata sani ba, Abuturrab na fita ya dau umbrella dinsa ya nufi part dinsa, yana shiga yasa key kofa don yasan cunning sisters din nasa na iya biyo sa, har lkcn tana durkushe kusa da gado ta takure waje daya, kashe Acn dakin yyi gaba daya ya karaso ya durkusa gabanta ya mika mata rigar yace "Wear this" ba tare da ta kallesa ba ta sa hannu ta karba, ya mike ya bude closet dinsa ya fiddo jallabiya ya fita, tashi tsaye tsyi ta sa rigar taga iyakarsa da kadan ya wuce kneel, bathroom ta karasa har lkcn rawan sanyi take, ta shanya masa towel din ta fito ta koma inda take ta xauna, bayan kusan minti talatin har bacci ya fara daukarta taji muryarsa a kanta, bude ido tayi da sauri ta gansa durkushe gabanta yana sanye da jallabiya hannunsa rike da cup din tea yace "Take!" Sunkuyar da kanta tayi tasa hannu ta karba ya mike ya fita, ba laifi ta sha tea din da yawa ta ajiye wanda ta rage, ta kalli agogo taga goma ya kusa, wayarta ta tuna yana cikin jakar da ta yar a titi, jinginar da kanta tayi jikin gado a sanyaye, sae gashi ya dawo ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Toh tashi ki kwanta sarkin yan xuwa church!" Bata ce komai ba ta mike a hankali tana kallon gadon, hawa tayi ta takure gu daya ta kwanta, yayi murmushi ya rufa mata duvet yace "Sae da safe" murya can kasa tace "Thank you" kashe mata fitila yayi bayan ya dau wani bargon ya fita ya rufo kofar, parlor ya koma ya kwanta kan 3seater. Can cikin dare tarin ta ya tada sa, ya dde xaune ganin har lkcn yi take yasa shi mikewa ya nufi bedroom din, bude kofar yyi ya kunna fitila ya karasa ya cire bargon yana kallonta, kakkarwa ya ga tana yi ga numfashinta na sama, ta bude ido tana kallonsa, hannu ya daura kan goshinta yaji xafi sosai, ta rike hannunsa a hankali yace "Are you Asthmatic?" Girgixa masa kai tayi yace "But you have pneumonia?" Bai jira tace komai ba ya mike ya bude closet ya fiddo babban sweater dinsa ya dawo ya dagota ya sa mata da kan shi ya kwantar da ita, kallonta ya tsaya yi yana tunanin taimakon da xai mata ganin yanda numfashinta ke yi, mikewa yyi ya dauko rub ya dawo ya bude zip din sweatern ya mika mata yace "Tashi ki shafa a chest din ki, it will help...." Jin bata ce komai ba ya bude ya diba sai kuma ya rasa yanda zai yi, imagine yyi da daya daga sisters dinsa ne ke shoe din nn ya xae yi, daga rigar xae yi ya shafa masu, yana wannan tunanin kawae ya daga rigar baccin jikinta ya sa hannu ya fara shafa mata rub din all over her body, hannunsa ta rike da sauri tace "Doctor..." A hankali yace "Yes am only being the doctor I am" bai kuma sauraranta ba ya shafe duk jikinta da man xafin, rufe ido tayi taki budewa, yana gama ya xuge xip din sweatern ya lulluba mata bargo murya can kasa yace "Go to sleep" bata ce komai ba bata kuma bude idon ba ya mike ya kashe fitilar ya fita, har bakwai bata tashi a bacci ba shi ma bai tasheta ba sanin jiya bata wani yi bacci ba, wanka yyi ya fito ya gama shirinsa a dakin sannan ya dawo parlor ya kunna laptop yana dube dubensa, can ya mike ya shiga kitchen don hada coffee, yana fitowa ya ga kofa a bude ya kalli kofar bedroom ya ga a bude shi ma, da sauri ya karasa bedroom din don a tunaninsa tashi tayi, tayi wucewarta, still yayi bakin kofa ganin khaleesat tsaye, ta juyo tana  masa wani irin kallo, duk ya daburce, juyawa tayi xata wuce ya rikota ya ja ta suka fita balcony yace "look leesat, she's just a frnd.... Bata da lafiya ne wllh..." Kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwana, ko nace maka wani abu ne.... Ni dai bance komai ba, ba ruwana" marairaice mata yyi yace "Baki yadda da brothern ki ba knn?" Wani kallo ta jefa masa ta warce hannunta tace "Eh ni ban yrda da kai ba kuma, dama shi yasa this days baka son muna xuwa wajen ka koh?" Hade rai yayi yace "I said she's my patient, are you daft?" Tabe baki tayi ta juya tayi wucewarta, da sauri ya bi ta ya fixgota fuskarsa daure yace "One word about what you just saw will mean you spelling dooomm" saketa yayi ya koma parlonsa, bai dade da shigowa ba peter ya kawo masa breakfast, takwas saura 'yan mintuna ya shiga bedroom bayan ya gama cin abinda xae ci na abincin da aka kawo masa, xaune ya ganta kan gado ta lulluba da bargo, tana ganinsa ta sunkuyar da kai, ya karaso bakin gadon yana kallon gashinta da yyi scatter all over, yace "Good morning" kallonsa tayi tayi murmushi bata ce komai ba, cire bargon jikinta yyi ta jawo da sauri ta rufe, buda ido yayi sai kuma ya d'an yi murmushi yace "ohk.... How's ur health?" Kai ta gyada masa ya juya ya fita, mikewa tayi bayan ta cire bargon ta nufi bathroom, ta tara ruwan xafi ta tsirka sannan ta wanke fuskarta, ta dau Listerine mouth wash/freshner dake bayin ta wanke bakinta snn ta fito, tsaye ta gansa dakin gaban mirror ta juya masa baya da sauri, karasawa yyi bayanta ya dafa shoulders dinta ya juyo da ita, ji tayi kamar ta nutse cikin sarkewar murya tace "Ina kwana...." Kallon kwayar idonta yake sai kuma yayi murmushi bai dai ce komai ba, ta sunkuyar da kanta, saketa yyi yace "xan tafi aiki yanxu....." Da sauri ta dago tana kallonsa tace "Nima xan je sch" kallon agogo yayi da sauri ita ma ta kalla, kamar xata yi kuka tace "Why did you not wake me" ya langwabar da kai yace "Coz you are sick" tace "Ni na samu lafiya.... I can still go" yace "Toh uniform din ki fa?" Xaro ido tayi tunawa da tayi ae fa ta jefar a titi, a hankali tace "Na yadda jakar a hanya doctor" shiru yyi yana kallonta snn yace "Ohk, let me get it for you" daga haka ya juya ya fita, ta koma a hankali ta xauna kamar warce ta tuno abu kuma ta mike ta shiga bathroom ta fara hada ruwan wanka, bayan kusan minti sha biyar ta fito daure da towel dinsa, xaro ido tayi ganinsa ta juya da sauri xata koma bayin ya dakatar da ita ta hanyar cewa "do I look like a monster!" kasa shiga bayin tayi ta kuma kasa juyowa, ya tsura mata ido daga sama har kasa, haka kawae yaji ya kasa tsayuwa, can ta juyo a hankali jin bai kuma cewa komai ba tana kallonsa, dauke kai yayi gabansa ya shiga faduwa, ta karaso a sanyaye tace "Am...am sorry!" Yayi karfin halin kallonta yace "Better, uniform din ki sun jike, kawai ki bari gobe ki tafi schl din" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauke idonsa yace "Let me get you something to put on, but before then...." Gaban madubi ya nufa ya nuna mata lotions hadda na gashi yace "You manage this" sunkuyar da kanta tayi ya juya ya fita. Main House ya tafi ya ga Mami ce kadai a parlor tana kallon wani program, kanninsa duk sun tafi boko, ta kalli agogo tace "Baka tafi aikin ba har yanxu Haiydar" yace "Ehh yanxu xan tafi, wasu takaddu da na ba ilham xan karba" daga haka ya wuce sama ta bi sa da kallo, yana shiga ya kulle dakin ya bude closet dinsu, ganin tafi son saka dogayen riguna ya fiddo mata da wani bakin abaya da ya gani gogagge da veil dinsa, har da sabbin inner dinsu ya dauko mata, tunanin yanda xae fita da kayan ya fara yi, can ya leka window sai kuma ya dawo ya dau towel dinsu dake baje a kan gado yayi wrapping din kayan ya koma gun windown ya jefar ya  rufe wajen, snn ya dawo ya bude bedside drawer ya fiddo full scap sheet dinsu har uku ya linke yana rike da shi a hannu ya fita, ya sallami Mami da ta bi sa da kallo ya fita, yana xagawa ya dau kayan ya nufi part dinsa, xaune ya sameta gaban madubi har lkcn tana shafa mai, kallo daya yayi mata ya dauke kai ya ajiye mata kayan kan gado ya juya ya fita, cikin few minutes ta ga gama shiryawa ta fito ta samesa xaune a parlor, sosai kayan suka mata kyau kamar balarabiya haka ya dinga kallonta har ta karaso kanta a kasa tace "Thank you Dr!" Yace "Welcome, ga breakfast" girgixa masa kai tayi tace "A'a, gida xan tafi" d'aga kafada yyi yace "As you wish, uniform din suna balcony" tace "Toh" snn ta nufi kofa ya bi ta da ido, sae da ta bude kofar snn ta juya ta kallesa suka hada ido, dauke kai tayi da sauri ta fita, ya lumshe ido na kusan minti bakwai sai kuma ya mike ya dau makullin motarsa ya fita. Ko da ta isa gida bata damu da ta kunna wayarta ba sanin ba lallai ya kawo ba, duk da tasan kila su Mumy na ta kiranta, gabanta ya fadi tunawa da tayi Mumy xata iya kiran gidan su Stella su ce bata je ba, mikewa tayi da sauri ta fita xuwa gun mai gadi tace "Plss ka aran min wayar ka idan kana da flashing power xan kira su Mumy ne" mika mata yayi ta karba, tana flashing ba a jima ba kiran Mumy ya shigo ta daga tace "Mumy!" Daga daya bangaren Mumy tace "Samantha me ya samu phone din ki" kamar xata yi kuka tace "Ya fada ruwa" Mumy tace "How manage, me ya sa baki tafi schl ba" tace "Mumy am coughing, am not feeling fine" Mumy tace "Baki je gidansu Stella din ba kenan?" Tace "Ehh mumy am at home" Mumy tace "You are covered with the blood of Jesus my daughter, don't worry gobe ina hanya, ki dau kudi ki siyo maganin tari" a hankali tace "ohk Mumy" daga haka suka yi sallama, Samantha tayi kwanciyarta, sai can kusan sha daya ta tashi ta fara gyara ko ina na gidan kafin sha biyu ta gama, ta wanke uniform dinta ta shanya snn ta shiga kitchen nan ma ta gyara ko ina, tunanin abinda xata girka ta shiga yi, can tayi deciding tayi jollof rice da sauce din cow meat sai fried plantain anjima, kafin ta fita ta hada tea ta soya kwai ta fito ta ci ta kwanta sai bacci, ba ita ta tashi ba sai hudu, ta kunna TV tayi kallon kusan awa daya, mikewa tayi jin tana jin  yunwa ta shiga kitchen don yin girkin, da yake akwai komai a gida kafin karfe shidda da rabi ta gama tayi slicing lettuces, tomatoes, cucumbers, onions, and carrot ta ajiye su gefe, ta debi abincin da xata ci ta fita xuwa parlor, ajiyewa tayi ya huce ta tafi wanka, tana daure da towel ta dawo ta dau abincin ta, tana fara ci Abuturrab ya fado mata haka kawai taji tana son kai masa duk da ba da yawa tayi ba, kallon agogo tayi taga bakwai ya gota, tasan ya dawo aiki yanxu, bata wani ci abincin da yawa ba ta mike ta koma kitchen ta xuba masa shinkafar a warmer, ta debi sauce din a wani cooler, ta dau wani transparent breakable bowl ta xuba masa vegetables din ta rufe, ta sa su gaba daya a basket snn ta dawo parlor ta ajiye, sama ta tafi xuwa saka kaya, ta shirya cikin doguwar riga me tsantsi, ta daura veil a kai ta fita.

💫Noorul Huda💫Donde viven las historias. Descúbrelo ahora