part 30/31

3.2K 88 13
                                    

[8/24, 8:02 PM] ‪+234 703 972 6966‬: 💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar 📚✍🏻

31.....
Alhaji Umar ya saci kallon Abba da uwarsa bai dai ce komai ba haka d'an uwansa Alhaji Jibril, juyawa Abba yayi kamar xae tashi ya fice daga parlon, Alhaji jibril ya ce "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kawo mafita yasa ya gane abinda yake shirin yi" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ae ni Allah ya isa tsakaninmu da Aliyu, wnn abun kunyar da me yayi kama da wani ido xa mu kalli 'yan adawan mu, me ya burgesa game da crista arniya, ni dai ina ganin jarabawa, Aliyu ya cucemu, yaro kamar shaidan, duk artabun da aka dinga yi jiya ace ba a kamasa ba har ya gudu ko ina ya tafi..."  A bangaren mumy kuwa tun daga jiya har yau kuka ne ya xamto abincin ta da ruwanta, tayi kukan tayi xage xagen, tayi iface ifacen, banda bata hakuri bbu abinda yan uwa da abokan arxiki suke, har cewa tayi da ta sani tun daren shekaranjiya ta kashe samantha tasan ba ita a duniyar ne kawai da ace ta bi musulmi sun gudu, gidan nasu cike yake da members din Church dinsu, mata da maxa, pastors har daga kaduna da Abuja sae da suka xo, masu addu'a nayi, masu xirga xirga da Abban samantha xuwa gidansu Abuturrab nayi, da ace Dad din Abuturrab ba babban soldier bane da ya shiga uku don ba abu me kyau bane xae biyo bayan irin sintirin da suke fiye da su ashirin har da matasa, daga karshe tsawa yayi masu yace "Su je duk inda xa su su nemi Aliyu su kashe sa ya basu go ahead, kada wanda ya kara d'aga masa hankali tunda basa ganin kokarinsa, bbu yanda suka iya ga gida cike da sojoji, haka suka juya sumui sumui suka fita. Abuturrab na xaune tsakar gida suna labari hira da Abba bayan la'asar, Alto bata kuma cewa a ta da Samantha tayi sllh ba a tunaninta bata da tsarki ne, Binta na xaune tana sirfa gero sai dai duk motsin da idonta xae yi a kan Abuturrab yake sauka, yana lura da irin kallon da take masa, sae abun ya basa dariya ya dai ci gaba da hirarsa da Alto, Samantha ce ta fito ta nufi bandaki da sauri ta fara amai tun kan ta isa, mikewa Abuturrab yayi haka Alto da Hansae dake wanke wanke suka dings cewa subhanallahi, Abuturrab ya d'agota a rikice yace  "Meya faru?" Ta fashe masa da kuka tana rike da cikinta tace "Ciwo yake min" Hansae ta kawo ruwa a buta tace "Ikon Allah to bara in jika ma sa6ara" Abuturrab ya karbi ruwan ya wanke mata fuskarta snn ta shiga da ita ciki. Kwanciya tayi ya xauna gefenta yace "It's ur period right?"  Juyawa tayi bata ce komai ba, ya mike ya fita, Tsaye ya ga Hansai har ta jika maganin da tace, yayi murmushi yace  "Ae baxa ta sha ba Baaba, bbu gun sayar da magani nan ne?" Alto yace "Kai da tafiya sosai, Binta ta raka ka gun da xaka samu babur ka hau, sae kayi kamar xaka shiga Gombe...." Abuturrab ya durkusa yace "ohh daga kauyen nan sae gombe?" Alto yace "A'a akwai kauyuka har uku a gaba..." Abuturrab ya mike yace "Toh shknn bari in je..." Tuni Binta ta dauraye hannunta tace "Mu tafi..." Ya kalleta yace "Ae na gane hanya yanxu, da kin yi xaman ki" Tace "Yo ae baka san inda xaka samu babur ba" Hansae tace "Gaskiya ne, bari ta rakaka gun sai ta juyo" toh kawai yace suka fita gidan, tun da suka fita Binta ke xuba bai kalleta ba bare ya tanka ta ba, tafiyarsa kawai yake, har suka isa inda babur uku suke sbda masu fita kauyen, duk machine din sun rube, Binta tace "Bako ne daga birni wae wajen kauyen nan xaku fitar da shi xae siya magani" Bata rufe baki ba ko wanne ya dinga cewa ya hau, na gabansa ya hau mutumin ya tada machine din, ya d'an kalleta yace "Sae na dawo" daga haka yace ma mai machine din su tafi. Sae kusan karfe shidda Abuturrab ya dawo rike da leda, Alto dake kade shanayensa a waje yace "Ka dawo?" Abuturrab yace "Ehh na dawo Baffa sannu da aiki" Alto yace "Ka dai samo maganin koh?" Kai Abuturrab ya gyada masa yace "Na samo" daga haka ya shiga, Binta kadae ce tsakar gida tana kwasan tuwo, ta washe baki tace "Har ka dawo Aliyu?" Kallonta yayi don sae da tasa Mami ta fado masa, ta fi kowa kiransa da Aliyu, yace "Na dawo! Bbu kowa dakin?" Tace "Ehh ita kadai ce" ya duka ya shiga Bukkar, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa a sanyaye ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yace "Samha!" Ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja, cikin sanyin murya yace "Kuka kike?" Sauke idonta tayi ya kamo hannunta yace "Am making you suffer koh, i know you re not use to all this Samha.... But for the sake of my love endure it for just a while..." Ta fashe da kuka tace "Am not complaining" gefenta ya dawo ya xauna ya jawota jikinsa yace "Bance kina complain ba, but you re not use to this such of life..." Bata ce komai ba yace "Kin fara period din ne?" Ta girgixa masa kai, yace "But it's on it way koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dago kanta yace "Shareni ma kika yi" kwace kanta tayi tace "How did you know?" Yayi murmushi ya daura kansa a kafadanta yace "I know because i am a doctor...." Tayi masa wani kallo ta gefen ido tace "Ko dai sa ido, kawai don ka ga na yi amai?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "Ni din, toh shknn in ma ya xo ya fara wahalar min da ke ko kallonku baxan yi ba, ya gama wujijjiga ki ya xuba abinsa ya wuce" murmushi tayi ta boye fuskarta a jikinsa, lkci daya Binta ta fado dakin, da sauri ya saketa ita ma ta ja baya, Binta na ganin haka ita ma da sauri ta fita, Ya kalli Samantha yaga ta wani hade rai, bai ce komai ba ya dau ledan da ya kawo ya bude, pad leda biyu sae inner wears da allurori da drugs, perfume, Toothpaste, brush soap da sponge sai gown har biyu da veil ya xube mata su gabanta, ta dauke kai bata ce komai ba, Ya bude daya ledan ya fiddo ledojin kaji biyu ya ajiye mata daya ya ajiye dayan a gefe, sae kuma Bread biyu da Blue band daya da ya siyo da kayan tea sae table water babba, mikewa yayi ya dau ledan kaza da daya bread din ya fita don kai ma su Binta. Bayan Isha Abuturrab na xaune tare da Baffa Binta ta fito tace "Aliyu ina jin fa ciwon cikin ne ya dawo sae juye juye take" Hansai dake cin tuwo tace "Subhanallahi, ka bata magungunan kuwa?" mikewa yayi ya shiga dakin Binta ta bi bayansa, ya durkusa gabanta yace "Sannu dear, but are you flowing?" Ta girgixa masa kai hawaye na sakko mata, dagota yayi ya bude ledan da magani ke ciki ya ballan mata biyu ya bata da ruwan goran ta sha, sae da yaga ta d'an nutsu snn ya mike ya fita, Hansai ce kadai a tsakar gida sai Binta da ta gaji da tsayuwa tun daxu dakin ta fito, Hansai tace "Ta samu bacci ne?" Yace "A'a ya mata sauki ne" Hansai tace "Toh Allah dai ya sauwake, dama ashe matar ka ce?" Kallon Binta yayi don yasan ta yi mata wata magana kenan, ya gyada kai kawai, tace "Allah sarki, ae ni nayi xaton kanwar ka ce, ashe mai daki ce, to shiga ciki sai ka tsaya tare da ita tunda ma bata da lafiya" yace "Toh" Hansai tace "Binta xata kawo maku bargo" juyawa yayi ya koma dakin, ba a dau lkci ba Binta tayi sallama bakin kofa ya fita ya karbi bargon ya dawo dakin, xaunawa yayi yana kallon samantha yaga har ta fara bacci, ya shimfida 'dan bargon a kasa ya rage lamp din dakin sosai ya kwanta. Can cikin dare ta kusa fadowa kansa bayan ta sauka daga kan katifa, ya mike xaune ya rikota yace "Me ya faru?" Rikesa tayi tace "Amai nake ji" ya rungumeta yace "Amma cikin ya daina?" Kai ta gyada masa, ya fara shafa mata bayanta a hankali murya can kasa yace "Aman xai koma kin ji?" Bata ce komai ba sae rufe idonta da tayi, haka ya dinga yi mata har taji aman ya koma, ta xame jikinta ta koma kan gado ta kwanta, ya jima xaune ganin kamar tayi bacci ya koma ya kwanta. Washegari da asuba tun da ya idar da sllhn asuba a dakin yayi ta tunanin inda xa su gashi bai da enough cash a hannunsa, kudin account din Hajiya Mariya ma bbu yawa, mikewa Samantha tayi xaune ya juya yana kallonta, ganin yanda ta bata fuska ya dawo kusa da ita yace "What?" Kamar xata yi kuka ta nuna masa cikinta, yace "Ya fara ne?" Ta gyada masa kai ta mike ta nufi inda ya ajiye kayan jiya ta dau pad da brush da toothpaste yana kallonta yace "In raka ki?" Wani kallo tayi masa yayi murmushi yana shafa kai yace "Ohk sorry" ko da ta dawo tilasta ta yayi ta ci bread da butter sbda alluran da xae mata, da kyar tana juye juye ta ci kadan ta sha ruwa yayi mata alluran ta kwanta, sae da gari ya fara wayewa snn ta samu bacci ya dauketa ya mike ya fita, Binta dake shara ta gaishesa da fillanci ya amsa yana tambayar ta tashi lfya, tayi murmushi ta tafi ta dauko wani flask da cooler ta dawo ta mika masa tace "Gashi karin kumallon ku" karba yayi yace "Mun gode" ya koma daki ya ajiye, tayi sallama bakin Hut din tace "Ga kofi" fitowa yayi ya karbi cup din ya koma ya ajiye, Muryan Alto ya ji da fillanci yana cewa "Ali na tafi kiwo sae na dawo" Abuturrab ya fito ya gaida sa, Alto yace "Ya mai jikin?" Abuturrab yace "Taji sauki Baffa, kilan baxa ka dawo ka same mu ba anjima xa mu dau hanya" Baffa yace "Allah mai girma, shi yasa ba a sabo da bako, baxa ku jira hat in dawo da rana ba" Abuturrab yayi murmushi yace "So nake mu isa gida da wuri ne" Baffa yace "Toh Allah ya tsare, ni bani da komai da xan baku, amma Binta xata tatsar maku nonon shanu ku tafi da shi bamu da komai baya ga wannan" Abuturrab yace "Ayya ba komai Baffa mun gode da karramawar ma" Alto yace "Toh Allah ya tsare, ku gaida mutan gida Allah ya tsare gaba" Abuturrab ya fiddo dubu goma cikin kudin jikinsa ya mika masa yace "Ga wannan ba yawa Baffa, in shaa Allah wataran xamu kawo maku ziyara" Alto ya bude ido yace "A yi haka?" Abuturrab yace "Kai dai ka karba Baffa" Alto ya karba da hannu biyu ya dinga sa masa albarka yana masu Allah ya tsare hanya har ya fita, Wanka Abuturrab ya shiga kewayen gidan yayi ya fito ya shiga Bukka, har lkcn bacci samantha take, ya shirya cikin kayansa da ya wanke jiya ya fita da na Baffa yana kallon Binta dake xaune tsakar gidan ita kadai yace "Baaba fa?" Bata kallesa ba tace "Ta je kauyen dake gaba da namu siyo gyero" yace "Ki ban sabulu xan wanke kayan nan" ta mike ta isa gabansa ta karba kayan tace "Xan wanke" yace "Noo, kar ki damu xan wanke" bata saurare sa ba ta nufi gun randar ruwansu ta diba, ya daga kafada ya juya ya koma daki ya bude flask din da ta basa ya ga kunu ne ya bude coolern ya ga kosai, diban kunun yayi ya dau kosan ya fita ya shimfida tabarma ya xauna ya shiga ci a nan, lkci lkci yake kallonta har ta gama wankin ta shanya kayan a igiyar dake tsakar gidan, ya koma inda take ta xauna, yace "Ke kin karya?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Yaushe Baaba xata dawo?" Tace "Kila tana hanya yanxu" yace "Bakya xuwa makaranta ne?" Ta kallesa tace "Yau alhamis" ya d'an buda ido yace "Haka fa" Bai kuma cewa komai ba, can tace "Bacci take ne?" Yace "Ehh" haka suka yi ta xama tsakar gidan shiru har Hansae ta dawo ya mike ya karbar mata kayan hannunta snn suka gaisa. Sai kusan tara da rabi Samantha ta tashi, har lkcn Abuturrab na xaune waje, ta mike ta dau sabulu da sponge ta fita, su biyu ne tsakar gidan shi da Binta dake wanke gyero, Samantha bata ko kallesu ba Abuturrab da ya bi ta da ido yace "Wanka xa ki yi?" Binta na jin haka ta mike tace "Bara in juye maki ruwan xafin ki" daga haka ta dau bokiti ta nufi gun murhu ta juye ruwan kai ta kai bokitin gun randa ta  sirka ta kai kewaye tace "Bara in dauko maki sabulu" Samantha tace "Akwai sabulu a nn" Binta ta dauko kwando ta mika mata Samantha ta shiga bayin, mikewa Abuturrab yayi ya shiga daki.

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now