💘💘💘💘
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA*_
💘💘💘💘
_(TRUE LIFE STORY)_
*Written By ~ Sis Nerja'art*
_*DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA AND SAINAH {UMMUN MEENAL}*_
_Kuyi hak'uri na canza sunan daga BA LAIFINA BANE zuwa DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[Onward together]*
*{ We give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
_THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑_
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
*BASED ON 2RUE LIFE*
Page 1⃣➖2⃣
Kwance take saman makeken gadon da yake cikin d'akin ta lullu6e jikinta da blanket idanuwanta a lumshe suke ammah ba bacci take ba,
Saman side bed d'in giya ce da sauran kayan maye a aje.Ahankali ta6ud'e idonta tare da jawo wayarta da take gefenta ta duba zaro manyan idanuwanta tayi ganin har k'arfe ukku ta yi.
Masha Allah nace ganin natural beauty, fara ce ammah ba chan ba tana da doguwar fuska ga tsawon gashin kai, idanuwanta manya ne sosai tana da dogon hanci siriri sai d'an k'aramin bakinta.
Janye blanket d'in da ta lullu6e da shi tayi tare da safkowa daga saman gadon doguwa ce ammah ba chan ba, tana da 'yar k'iba daidai jikinta.
Material ne red nd black colour a jikinta duk ya matseta duk motsin da xatayi sai jikinta ya amsa.
Dasauri tajawo veil d'inta tayafa.
Daidai lokacin aka bud'e toilet d'in da ke cikin d'akin wata macece mai k'iba tafito jawur da ita mai kyau sai dai 'yar gajera ce jikinta sanye da towel daidai gwiwarta tana rik'e da wani k'arami tana goge fuskarta da alama daga wanka tafito.
Kallonta takai wajenta tana murmushi tace" sapna sai ina kuma,
Cigaba tayi da d'aukar abinda take buk'ata tana zubawa cikin handbag d'inta ba tare da ta juyo ta kalleta ba tace mummy lubna gida zanje ne,
6ata fuska tayi tace haba sapna tun yanzu, " ba fa nan kika kwana ba duka fa wajen 11am kikazo.
Sowie mummy wlh na ce ma ummanah ba zan dad'e ba idan ban koma ba ai ba zataji dad'iba tunda bance mata zan kwana ba.
Fridge d'in da yake cikin d'akin tabud'e daga lemuna sai kwalaben kayan shaye-shaye a ciki kwalbar giya tad'auko taxura cikin jakkarta sannan tajuyo ta sakar ma matar murmushi har dimple d'inta yalotsa sannan tace bari inwuce mummy.""Ohk sapna sai munyi waya.""
Fitowa tayi daga d'akin a parlour ta iske Teema da wani mutum tayi d'ai-d'aya a jikinsa shi kuma yana ta shan sholisha daga gani ka san ba ya cikin hankalinsa.
Ba tare da ta kallesu ba tazo zata wuce Teema ce tad'ago kanta takalleta tace a'ah baby sapna 'yar wajen lubna har kin fito kenan sai kuma ina.
Ko inda suke bata kallaba tace, " gida zanje,
Ta6'e baki teema tayi tace kedai wlh kina da matsala sai ana hutawa sai kikawo wani zancen gida.Ba tare da sapna ta bata amsaba tafice daga d'akin.
Tafiya take har ta kusan kai bakin gate d'in gidan tacikaro da sumy tana shigowa tangyad'i kawai take domin a buge take.
