DUK TSUNTSUNDA YAJA RUWA part 35

823 48 0
                                    

💘💘💘💘

    _*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

                  💘💘💘💘

   _(BASE ON TRUE LIFE STORY)_

*Written By ~ Sis Nerja'art*

_*DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL*_

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
      *[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
_THE  PEN OF LOVE. 😘 HEART  TORCHING  ❤  TEAR  OF  SORROWS   😭  CURDLES  🙂  GIGGLES  😁  AND  MARRIEGE  THINK💑_
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣5⃣

Haydar tunda yaje asibiti a daddafe yake aiki duk yadda yaso yature tunanin sapna a ransa ammah yakasa dan ma Allah ya taimakesa yau baida patients sosai hatta shi kansa Dr Ahmad saida yayi mamakin ganin yadda haydar yacanza yau baida kuzari a tare da shi, ko da yatambayesa ko baida lafiya, haydar cewa yayi lafiyarsa lau kawai yanayin ne nayau yacanza masa,

shidai Ahmad ba dan ya yardaba kawai dan ya san halin abokin nasane da zurfin ciki.


Sapna hankalinta gaba d'aya yana wajen kallo bata ankaraba sai gani tayi k'arfe sha biyun rana tayi,  dasauri tatashi tashiga kitchen jalop rice ce tayi musu wacce taji kayan lambu nan da nan gidan yagauraye da k'amshin girkinta,  bayan ta gama ta gyara wajen, bedroom tashiga saida tayi wanka tashirya sannan tayi sallar azuhur,  bayan ta gama tadawo parlour tazauna tacigaba da kallo sai wajen k'arfe ukku sannan haydar yadawo gidan,

sapna ciki-ciki tace sannu da zuwa batare da ta kallesaba, Haydar shuru yayi kamar ba zai amsaba yatsaya yana kallonta sai kuma chan yace sannu, sannan yashige bedroom.

sapna ta ji haushin yanayin yadda ya amsa mata, tsaki taja tace ka dai ji dashi,

Bayan ya gama kimtsawa yafito yanufi dining, sapna tashi tayi tabi bayansa saida tayi serving d'insa sannan itama tazuba nata tazauna taci,  bayan sun gama tattare kayan takai kitchen,  lokacin da tadawo haydar har ya canza channel d'in da take kallo,  turo baki tayi tace yaya haydar ba fa nan nake kalloba,  batare da ya kalletaba yace toh Ai ni nan nake sha'awar kallo,

Sapna cike da jin haushi tawuce tashiga bedroom tazauna, idanuwanta takai bisa bedside da ya aje wayarsa cikin jin dad'i tad'auki wayar talalubo number d'in ummah takira,

bugu biyu ummah tad'auka jin muryar ummah da tayine yasa taji sanyi a ranta ahankali tace ummana ina wuni?
Umma ma cike da jin dad'i tace lafiya lou mamana ya kuke?
Sapna tace lafiya lou ummah nayi missing d'inki.
ummah tace ban yardaba keda kikaje kika kashe waya dan ma kar mu dameki,  ai shi haydar yana kira kullum muna gaisawa.
Sapna marairaicewa tayi tace ummah wlh ba haka bane, ummah tace toh yayane idan ba haka bane?
Sapna kamar tafad'a ma ummah kwacemata waya da haydar yayi sai kuma taji ba zata iyaba gudun kar Hankalin ummah yatashi tad'auka basu zaman lafiya,
muryar ummah taji tana cewa kinyi shuru.
Murmushi Sapna tayi tace Ummah wayanace tafad'i ta lalace saisa kikaji ni shuru.
Ummah tace ayya Allah sarki toh maimakon kibada agyara miki?
Murmushi Sapna tayi tace ai ya ce zai kai min wajen gyara.
Ummah tace toh shikenan dafatan dai kuna zaune lafiya babu wata matsala?
Sapna tace lafiya lou muke ummah,
Ummah tace Masha Allah haka akeso kidaita hak'uri domin shi zaman aure sai da hak'uri, kizauna da danginsa tsakani ga Allah banda yawo.
Sapna tace toh shikenan ummah insha Allahu zan kiyaye,  ya wajensu baba sani?  Ummah tace suna nan lafiya lau,  Sapna tace Allah sarki Ummah yanzu ke kad'ai ce gidan,  dariya ummah tayi tace injiwa yafad'a miki ai nayi wata sabuwar 'yar aiki dattijuya yanzu haka na bata d'akinki ta zauna kinsan zama mutum d'aya babu dad'i.
Cikin jin dad'i Sapna tace aikam dai ummah hakan da kikayi shine daidai ammah kamar kina jira intafi daga tafiyata har anbada gadon d'akina,
dariya ummah tayi tace toh ya za'ayi daman ai ita mace zamanta a gidansu na d'an lokacine gidan mijinta shine ake fatan yakasance dauwamamme,
Numfashi Sapna taja tace haka ne ummah,
Ummah tace toh sai anjima kigaishe min da haydar d'in,
Sapna tace insha Allahu za ya.... jin za a bud'e dakin yasa tayi saurin kashe wayar batare da ta gama wayar ba.

DUK TSUNTSUNDA YAJA RUWAWhere stories live. Discover now