💘💘💘💘
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
💘💘💘💘
_(BASE ON TRUE LIFE STORY)_
*Written By ~ Sis Nerja'art*
_*DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
_THE PEN OF LOVE. 😘 HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑_
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
Page 2⃣1⃣➖2⃣2⃣
Sapna tana isa gida d'akin ummah tafara shiga da sallamarta lokacin ummah tana zaune tana yankan farce, kallonta ummah tayi tana murmushi tace a'a mamana har kin dawo? Saman kujera Sapna tafad'a tazauna tace wlh ummah na dawo mummynsu ma tana gaisheki ga ma kayan bikki da suka bada, ummah tace masha Allah anko gode Allah yabasu zaman lafiya, Sapna tace Ameen sannan tatashi tad'auki jakarta tace ummah bari inshiga d'aki Ind'an watsa ruwa kafin akira magrib, ummah tace toh shikenan mamana.
Lubna ko da tafita motarta tashiga bata zarce ko'inaba sai gidan malaminta da Sallamarta tashiga cikin jin dad'i matansa suka tarbeta nan sukace aikam kinyi sa'a yanzunnan malam yashigo lubna tace Allah sarki matarsa d'aya tatashi tace bari inje infad'a masa zuwanki, ko da tashiga tasanar da shi cikin jin dad'i malam yace ace tashigo, ko da lubna tashiga malam cikin jin dad'i yakar6eta tare da nuna mata waje tazauna, malam yace me yake tafe dake ranki yadad'e?, lubna gyara zama tayi sannan tace malam wani aikine yake tafe da ni idan kacika min shi zan baka kud'i masu tsoka, cikin jin dad'i yace kifad'a aikinki nikuma incika miki shi,
Cikin jindad'i Lubna tace wata yarinyace nakeso kayi min aiki akanta inaso kasa tasoni kuma duk umurnin da zan bata ba zata k'etaresaba, kai ba ma ita kantaba hatta mahaifiyarta bazata ja da maganataba saboda naji ance mahaifinta ya rasu kaga aikin zai zo mana da sauk'i Dan haka inaso tazo a hannuna sai yarda nayi da ita.
Tunda tafara maganar malamin zane yake a k'asa yana sharewa sai chan yace minene sunanta tace sapna, saida yarubutu sunanta kusan sau ukku yana sharewa sannan daga k'arshe yad'ago kai yakalleta yace hajiya aikinki zaiyi wuya gaskiya saboda yarinyarnan akwai tsari a jikinta itada mahaifiyarta suna da k'arfin addu'a,
Cikin tashin hankali lubna tace yanzu malam ya kake gani za'ayi yanzu kataimakamin ko nawane wlh zan iya biya Indai zakayi min aikin nan, dariya malamin yayi yace ai babu abinda zai gagareni zanyi iyakar k'ok'arina in sunsan wata basusan wataba, yanzu yadda za'ayi kije gida zan yi bincike bayan sati d'aya kitafo min da gashin kanta ko ya yake saboda dashi zanyi aikin, mahaifiyarta ko kibarni da ita nasan yadda zanyi da ita saboda aikinta mai sauk'ine na yarinyar shine mai wahala ammah zaki bada dubu goma wanda za ayi sadaka da shi, cikin jin dad'i lubna tace godia nake malam ai nasan aikinka kamar yankan wuk'ane dan haka zan iya biyan ko nawane, dubu goma lubna tajawo ta aje gaban malam sannan ta d'auko dubu biyar ta aje tace wannan kuma nakane kasha ruwa kafin aiki yacika, malam washe baki yayi yace nagode sosai hajiya, tashi lubna tayi tafito matan malam dubu biyu tabasu sunata murna da godia sannan taje tashiga motarta tanufi gida lokacin dare ya yi, tun a mota takira deejah tafad'a mata yadda sukayi da malam tare da cewa tataimaka mata wajen ganin ta samo gashin kan sapna, cikin jin dad'i deejah tace gaskiya naji dad'i sosai da jin labarin nab nikuma insha Allahu zan samo miki gashin kanta cike da jin dad'i sukayi sallama.
