💘💘💘💘
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
💘💘💘💘
_(BASE ON TRUE LIFE STORY)_
*Written By ~ Sis Nerja'art*
_*DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
_THE PEN OF LOVE. 😘 HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑_
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔Page 2⃣7⃣
Sapna yau tunda tayi sallar isha'i bata tsaya doguwar hiraba takwanta saboda wani irin bacci da takeji, ummah ma da tajita shuru talek'o d'akin da mamakinta taga Sapna har ta yi bacci maida mata d'akin tayi tarufe,
Sapna cikin baccinta taji wayarta tana ringing dakyar tabud'e idonta tana tsaki tajawo wayar da shirin tayi rejecting d'in call d'in ganin sunan mummy lubna ya bayyana yasa tayi picking d'in call d'in cikin muryar bacci tace hello mummy, daga chan 6angaren lubna ce da Amfah manne da juna sunsa hand's free suna murmushi lubna tace baby ba dai har kinyi bacciba? Sapna ahankali tace eh wlh mummy bacci nake,
Lubna tace halan kind'an sha wani abun,?
Sapna tace a'a ba abinda nasha gajiyace kawai,
Lubna tace ohk, daughter yau baki lek'omu ba lafiya dai ko?
Sapna cikin k'osawa da maganar tace lafiya lau wani aikine nad'anyi ma ummah dat's y ban fitaba yau,
Lubna tace Ayya ammah dai gobe zaki shigo ko?
Sapna tace mummy ko dai jibi.
Lubna tace no gobe dai saboda akwai muhimmiyar maganar da zamuyi da ke,
Sapna tace mummy da ni kuma? Allah dai yasa ba akan mutanenki bane,
Dariya lubna tayi tace toh sarkin tsoro ba akansu bane saidai kin shigo goben kinji ko ma dai minene, Sapna tace ohk Allah yakaimu bata jira Jin me lubna zataceba takashe wayar gaba d'aya sannan takoma baccintaDaga chan 6angaren Sapna na kashe wayar lubna da amfah suka kalli Juna suka bushe da dariya amfah tace k'awata bakida dama wlh, lubna tace ai saima goben idan ta zo anan zakiga rashin damata saboda ko me za'ayi gobe yarinyarnan bazan saurara mataba, amfah tace wlh kau k'awata kar a saurara mata k'ara muyagi kasonmu, lubna murmushi tayi tace bari dai goben tayi yanzu dai kizo muyi bacci dan nima baccin nakeji.
wanshe kare Sapna tun da tatashi takejin jikinta ya yi sanyi, wajen 10am da tagama had'a musu breakfast tad'aura musu girkin rana burabusko da stew tayi musu sauri take tagama saboda tun safe lubna take damunta da waya akan tazo, wajen 12 ta gama duk wani aiki da zatayi wanka tashiga tayo saida tayi sallar azahar sannan tashirya cikin material Pink my ratsin blue ba wata kwalliyar kirki tayiba ammah ta yi kyau sosai tafeshe jikinta da turaruka masu k'amshi sannan tad'auko veil d'inta blue d'an k'arami tayafa takalmanta tazura blue tad'auki jakkanta swaga tarataya a kafad'anta ta yi kyau sosai.
Fitowa tayi tanufi d'akin ummah talek'a tace ummah zan je wajen Aunty lubna, ummah tace toh mamana sai kin dawo kigaishe da ita, sapna tace toh ummah zataji.
Tana fita tasamu abun hawa tahau tace yakaita burget, har k'ofar gidan lubna ta safka tasallami mai abun hawan,
Da sallamarta tashiga gidan a parlour tasamu su teemah nan taga suna ta mata gani-gani, sapna d'auke kai tayi batare da ta ce musu komai ba tashige d'akin lubna, ko da ta shiga babu kowa d'akin motsin da taji a toilet yatabbatar mata da lubna wanka takeyi, saman bed side tahango Apples kusan guda shidda cikin babban plate sai 'yar k'aramar knife sai shainin takeyi, murmushi sapna tayi taje bakin gadon tazauna sannan tad'auki Apple d'aya da wuk'ar tana yankawa tana ci,
