💘💘💘💘
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
💘💘💘💘
_(BASE ON TRUE LIFE STORY)_
*Written By ~ Sis Nerja'art*
_*DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
_THE PEN OF LOVE. 😘 HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑_
*JUST GIVE US FOLLOW....*✔https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
_*Nagode sosai my fan's, gaskiya naji dad'in yadda kuke nuna damuwarku akaina, ina jin dad'in addu'o'in da kukemin, masu bina a pc wad'anda ban samu namaida musu reply ba kuyi hak'uri nima ba a son raina hakan take faruwaba ammah duk da haka ana tare nagode sosai da addu'anku*_
_wannan page d'in nakune my fan's nabakushi a kyauta😘_
Page 3⃣8⃣
Sapna kuka takeyi babu k'ak'autawa saida taji kanta ya fara ciwo sannan tayi shuru dakyar tatashi tasha magani sannan takoma takwanta nan da nan zazza6i yafara rufeta dakyar take tashi tana sallah,
har akayi sallar isha'i batasa haydar a idontaba dakyar tatashi tayi wanka tasaka rigar baccinta kwanciya tayi ammah takasa baccin ga yunwa ga zazza6i, ganin har k'arfe tara batasa haydar a idontaba yasa tafara kwallah tace shikenan shi yana can wajen 'yan matansa nikuma ya barni nan ni da baya k'auna, tsayuwar motarsa ce taji sai jin wani sanyi taji a ranta, haydar ko da yashigo bata kalli inda yakeba murmushi yayi yace baby ba dai har yanzun fushin ake da niba?
haushinsane taji ya k'ara kamata cikin ranta tace tunda ka je kagama soyayyarka, bata tankasaba tajanyo wayanta tafara game, ammah babu alamun fara'a atare da ita.
murmushi haydar yayi yace bari dai inje inyi wanka inyaso idan nafito sai mushirya, haydar wanka yashiga da harara tarakasa cike da jin haushinsa sannan tacigaba da game d'inta.
bayan ya fito saida yashirya sannan yad'auko ledar da yashigo da ita yadawo gefen gadon ya aje sannan yatashi yaje kitchen yad'auko plate da cups sannan yadawo gefenta yazauna yace baby kitaso muci naman nan ni yunwa nakeji kuma nasan yau yadda ake fushin nan ba abinda zaki girka min saisa nasiyo.
turo baki sapna tayi tace kaje kaci ni bana ci.
murmushi haydar yayi tare da shafa cikinta yace ammah ai kema kina jin yunwa, ture hannunsa tayi daga saman cikinta.haydar bai damuba yatallabo fuskarta yace subhanallah baby halan kuka kikayi naga fuskarki duk ta kumbura, sapna kamar jira take sai hawaye suka fara tsiyaya, haydar a rikice yace sapna meyake faruwane? kallonta yake cikin ido kishinsa yagani k'arara acikin idonta
janye fuskarta tayi daga rik'on da yayi mata, murmushi haydar yayi yace sapna ba dai akan fitar da nayi bane? harararsa tayi tace ni ina ruwana da fitar da akayi dan ka je wajen wacce kakeso ai ba laifi bane,
tunda tafara maganar haydar yakafeta da ido yace baby nifa d'azun hospital naje wata theater mukayi babu wajen wacce naje ni wace mace zata soni ahaka.
sapna kamar zatayi kuka tace kai d'inne mace ba zata so ba bayan kana da kyau da kud'i?
murmushi haydar yayi yace toh ya za'ayi tasoni bayan ke kanki baki sona ai bana tunanin akwai wadda zata soni ahaka.
