_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story__*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 43/44*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Dik wani lungu da sak'o na k'asar kebbi ba'inda ba'asaka matakan tsaro ba, hanyoyin shiga da fice filayen jirgi tashoshi dakuma hanyoyi ba'inda ba'asaka tsaroba ko'ina police ne da sojoji,, bincike ake sosai ko'ina da ko'ina ba kama hanun yaro domin kamo momy da mubina,,,,"....
Zaune suke suna firan irin k'ok'arinda Rayyan yai, acikin zuciyoyinsu kuwa farinciki ne fall yanzu abu d'aya suke jira shine kotu ta wanke MUFIDA daga zarginda ake mata koma ba'akamo su momy ba tinda dai antabbatar ba'itace ta aikataba to Alhmdllh,,,....
Cikin ikon Allah ana tsaka da bincike sai aka kira D.I.G daga office d'in masu tsaro na filin jirgin Ahmadu Bello International Airport wa'enda ake nema suna daya daga cikin basinjojin jirginda zai d'aga 2pm, nantake aka k'ara tsaro acikin filin jirgin lungu da sak'onsa,,,...
Cikin nasara kuwa Allah yasa akaga momy da mubina da mustapha zaune acikin office din d'aya daga cikin ma'aikatan wajen nan akamasu sannan aka daukesu aka wuce dasu izuwa court,,"....
3pm dot aka koma kotu akacigaba da gudanarda shari'a, bayan mai Shari'a ya'iso sai aka fito da momy da mubina aka kai musty gun momyn su faruk sukuma aka gurfanardasu agaban kotu sai rabon idanu suke dakagansu kaga marasa gaskiya,,,....
Bayan mai Shari'a yagama abunda yake saiya dago yadubesu sannan yacire glass d'in idonsa yafara magana "tabbas kwararan shaidu sun tabbatarda mubina kece kika kashe faruk saidai shaidu basu tabbatar da kece kika Nashe Alhj Ahmad ba amma dole kinada masaniya akan Wanda yakashesa saboda haka kotu na sauraronki daki fad'amata waya kashesa?" dube dube tafara nantake kwallah suka fara zubomata takalli momy wacca itama kwallan take sannan tafara magana "eh ni nice nakashe faruk amma banice nakashe dady ba momy ce" tana fad'a nantake motanen kotun kowa yace "SUBHANALLAH WA'IYAZUBILLAH" nanfa surutu yafara cika kotun saida mai shari'a yai magana "order order is ok" sannafa akai tsiitt,,,.....
Y'an rubuce rubuce mai Shari'a yai sannan yasake d'agowa yace "mubina meyasa kika kashe faruk meya maki akan wane daliline yasa kika kashesa?" Tsuru tai da idanu tana sai kwallah take zubarwa, ahankali tafara magana "Mahaifina shine silar canzawar halayyata wacca natashi bada itaba sakamakon nunamana fifiko dayake a tsakaninmu da wacca ba y'ar uwarmuba, tinda muka girma muka mallaki hankalin kanmu nafara sanin bambanci tsakanin farinciki da bak'inciki dad'i da d'aci fari da bak'i tin lokacin tsintsar tsanar MUFIDA tafara Shiga acikin zuciyata sakamakon fifiko da mahaifinmu ke nunawa a tsakaninmu da ita, tin muna yara dady yafison MUFIDA akanmu komai zai siyamana sai nata yafi namu kyau da tsada tin bama magana harmuka fara amma idan munyi sai mahaifiyarmu tace ai itace babba akanmu, a makaranta ma idan MUFIDA tai ta d'aya saiyamata kyauta amma ni idan nai bayamun, lokacinda mukaje university sainasamu wani saurayi Wanda nake matuk'ar so najima sosai atare dashi, kwatsam sainagansa da MUFIDA danamasa magana saiyamun tozarci ya wulak'antani a saboda ita, nahak'ura dashi nafara son yayanmu wato hamma faruk, nayi nisa sosai cikin soyayyarsa wacca takaiga harnakasa b'oyewa nafad'awa dady da momy sai dady yace najira harmugama karatu saboda so yake yahad'ani tareda MUFIDA da munira ya aurardamu atare, jin hakan yasa nakwantarda hankalina tinda shi dady yasanda zancen,, kwatsam wani lokaci munyi Hutu muna gida sainaji wai anyiwa MUFIDA baiko da hamma faruk, nayi kuka nayi kuka kamar raina zai fita lokacin ne nafara tinanin kashe faruk zuciyata take ingizani tinda narasasa to itama bazata auresaba" share kwallanda suka zubomata tai sannan tacigaba,,,....
Lokacinda natinkari momy da zancen lokacinne take fad'aman ai MUFIDA basu suka haifetaba, naji dadin hakan ba kad'anba sai momy tahanani d'aukan matakinda nai niyar d'auka tafad'aman tsarinda tai akan dady da MUFIDA, natsorata sosai saida tak'araman kyakkyawan bayani sannan hankalina ya kwanta na'amince da tsarin nata",,,,....
