TSINTACCIYAR MAGE part 53/54

1.3K 56 0
                                    

_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
  _a true love story_

_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*Page 53/54*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Saikusan 9pm sannan tadawo gida tana dawowa kawai tawuce d'akinta tatufe, wanka tai sannan tai sallah tai shirin bacci tai kwanciyarta,,....

Washe gari ma bata fitoba sai kusan 9am sannan tai wanka tashirya tafito, d'akin hajiya taje tamata barka da safiya sannan taje d'akin Abbu a can ta tadda mai martaba da sarki nanta durk'usa takwashi gaisuwa cikin tsintsar ladabi suka amsa mata tareda sakamata albarka sannan tafito,,....

Tana fitowa saitai kicib'is da MUJAHID zaishigo, dasauri taja da baya tai tsuru tana kallonsa, murmushi yasakarmata sannan yai tsaye ya rungume hannayensa yana kallonta, murmushi itama tasakarmasa sannan ta duk'arda kanta tace masa "barka da safiya mr man" cikin murmushi yace "barka dai amaryata fatan kintashi cikin lafiya" tace "Alhmdllh" gyara tsayuwarsa yai yakalleta yace "lafiya baki fito break ba d'azu kowa yafito kekad'aice" d'an sosa kanta tai kamar mara gaskiya sannan tace "umm....um bacci ne yad'aukeni wallahi bayan nagama sallah" yai murmushi,,,.....

Ammar ne da musty suka shigo da gudu cikin uniforms d'insu, dasauri musty yarik'e hanun MUJAHID yanafadin "yeee narigaka wallahi nine number one" tsaye ammar yai yakwabe fuskarsa kamar zaiyi kuka, dasauri MUJAHID yarik'o hanunsa yana fadin "a,a my Lil bro karkayi kuka mana kai namijine kazama jarumi kaima watarana kamatsa sosai kacinyesa kazama number one kajiko" murmushi ammar yai yace "dagaskiya brother me nima zan iya cinye musty nazama number one kullum fa musty shike na 'daya a school a komaima shike na 'daya"  yai maganar cikin yanayin kuka,  MUJAHID yai murmushi yace "sosai ma kuwa zaka iya amma saika daina kuka kadinga jajircewa sannan zaka iya zama nmbr one kaima kadaina kuka akan yacinyeka kaima kayi karatu kayi kokari kai na d'aya, yanzudai meya maidaku gida ba school kukajeba" musty ne yai saurin cewa "ammar ne yamanta littafensa na homework kuma auntyn mu duka take sosai shine muka dawo ya dauka" itadai MUFIDA kallonsu kawai take tana dariya, MUJAHID yace "ok oya to kuje ku d'akko kuwuce school kuma kuyi karatu sosai" suka ce "toh" sannan suka wuce da gudu,,,....

Mayarda dubansa yai gun MUFIDA datai tsaye tana kallonsu tana murmushi, shima murmushin yai saitacemasa "wannan rigimar tasu ta tinaman abunda yafaru abaya daga cikin labarina" murmushi kawai baice komaiba saita juya tawuce abunta tana share y'an kwallanda suka zubomata,,,.....

    Kimanin kwanansu MUJAHID biyar a k'asar Nigeria sannan suka tattara suka koma k'asar BAGDAAZ yana kewar abar k'aunarsa haka itama tana kewarsa sosai,,,.....

MUFIDA tacigaba da fita aikinta saidai batajin dad'in aikin yinsa kawai take gashi yanzu ayyuka sunmata yawa kusan kullum suna kan hanyar k'asashe daban daban domin kulla alak'a da wasu companonin daban hakan yasa yanzu batada lokacin kanta bare kuma nawani wani lokacin ma dole saita kashe wayarta saboda kar adameta da kira,,,....

              *****  *****

Rayuwa tacigaba da gudana cikin farinciki da walwala tini aka raba gadon Alhj Doctor Ahmad Shitu dukiyar MUFIDA kuma aka damk'amata abarta, a ranar wuni tai kuka saboda abun yatinamata da rayuwarta ta baya yanda dady ke nuna tsintsar kulawarsa a gareta yake bata gata da jindadi tamkar yarsa tacikinsa daya haifa, tai kuka sosai kamar ranta zai fita saida tagaji tabama kanta hak'uri,,,.....

Munira tadawo itama ta kammala degree d'inta MUFIDA tashiryamata walima had'addiya sannan tabata kyauta mai tsoka ta musamman, a ranar kuwa saida sukai kuka sosai saboda tinawa da mahaifinsu, tinda munira tadawo suka koma gidansu kasancewar akwai security's kuma dik hadiman gidan sunanan donhaka suka koma acan,,,....

TSINTACCIYAR MAGEWhere stories live. Discover now