TSINTACCIYAR MAGE part 65/66

1.4K 50 2
                                    

_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
  _a true love story_

_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*Page 65/66*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

         ______________

MUFIDA kuwa tariga data cire tsammanin MUJAHID zai sake waiwayota yanzu komai tariga data barwa Allah tamayarda hankalinta ga ibada saboda tasan shine kad'ai mafita agareta,,,...

Gidan MUJAHID acan dakaru suka cimmasa nan suka shaidamasa sakon mai martaba, sanin halin mai martaba yasa dole badan yasoba yashirya suka tafi,,,".....

A babban parlon mai martaba MUJAHID ya cimma mai martaba, tinda yashigo parlon yaga yanayin fuskar mai martaba yasan lallai mai martaba ransa ya baci sosai, cikin tsintsar ladabi yak'arasa ciki yadurk'usa yakwashi gaisuwa, dasauri mai martaba yadakatardashi da fad'in "bana buk'atar gaisuwarka Yarima"    mikewa yai tsaye sannan yazauna ya sudda kansa k'asa,,,"....

D'agowa mai martaba yai yakallesa sannan yafara magana "Amma wallahi Biryama kabani mamaki haba saikace ba musulmiba kamar ba namijiba kamar bamai ilimi ba haba ai kowanne irin laifi yarinyar nan tamaka izuwa yanzu yadace ace ka yafemata kodon halinda take ciki a yanzu, takiraka tayita neman layinka amma daga ace yana kashe saikuma kagi dagawa kokuma ka kashe wayar gaba 'daya, tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita, shekaranjiya  batada lafiya kwananta biyu a asibiti amma kak'i zuwa kuma nakira na fadamaka, haba MUJAHID bansanka da wannan halayyarba kai mutum ne mai hak'uri da juyawa  komai baya ka yafewa banza bare kuma matarka y'ar uwarka kanwarka jininka kuma wacca jininka yake a jikinta",,,,....

Yanajin abunda mai martaba yafada "wacca jininka yake a jikinta" saiya d'ago da sauri ya kallesa yace "jaddu kana nufin MUFIDA cikine da'ita?" kallonsa mai martaba yai ganin yanda fuskarsa tai sannan yace "eh shine ma silar zamanta asibiti yanzu watansa biyu da kwana  uku saboda haka inaso kayafemata dik laifinda tamaka kadauki matarka kaje kacigaba da kula da'ita dakuma abinda ke cikinta saboda karta sami matsala, kaga yanzu haka tinda muka dawo asibitinnan dikda taji sauki sosai amma har yanzu batada walwala sosai kullum tana cikin d'aki a kwance abincima sai hajiya tamatsamata sosai sannan takeci shima ba wani mai yawaba sosai, dan Allan Biryama kayi hak'uri Allah mafa yanason mai yafiya saboda shi kansa munamasa laifi kuma ya yafamana to bare mu kuma damuke ajizai masu aikata sabo, kayi hak'uri ka danne zuciyarka mace hak'uri ake da'ita saboda ita mai rauni ce kaina babba dole kadinga hak'uri",,,,....

Haka dai mai martaba yaita bama MUJAHID hak'uri yana kara jan hankalinsa da nasihohi yana kwantar masa da hankali har yaji zuciyarsa tai sanyi nantake tausayin MUFIDA yafara ratsashi musamman dayaji irin wahalarda takesha, d'agowa yai ya kalli mai marataba yace "shikenan jaddu nayafemata Allah i yafemana baki d'ai"  wani irin farinciki mai martaba yaji yai mirmushi yace "ameen yh rabbi Allah i maku albarka yak'ara kareku daga sharrin shaid'an da mak'iya" ya amsa da ameen,,,....

Can yace "jaddu ina take ne?" sai mai martaba yace "tana ciki a 'dayan d'akin" nan yatashi yashiga ciki,,"....

Kwance take a k'asa kan tiles d'in d'akin saboda yanzu komai batajin dadinsa tafison ma ta kwanta a kasan tanajin d'an sanyin tiles d'in yana shiga jikinta, ahankali yabud'e k'ofar yashigo cikin sallama, can kusa da bango yahangota kwance kamar y'ar baby, dama MUFIDA bawani jikin kirkine da'ita ba bare kuma yanzu da ciwo yazo, yanzu bayan tilin bobbs da hips bakomai ajikinta dikta rame tai fari tass,,,....

Jin zazzak'ar muryarda ko a mafarki tajita zata gane mai ida yasa dasauri tad'ago sai tai tozali da kyakkyawar fuskarsa, wasu zafafan kwallah ne suka zubomata sannan ta tashi a zaune dakyar towel d'inda take d'aure dashi ma kasa rikesa tai yasub'uce yafadi k'asa, cikin muryar kuka kwallah nabin kuncenta taharde hannayenta tace "dan Allah MUJAHID ka yafeman narok'ek'a da girman ubangijink....a" tak'arasa muryanta na rawa tana kuka,  dasauri yak'araso kusa da'ita yadurk'usa yajanyota izuwa k'irjinsa ya rungume cikin tsintsar tausayinta,,,....

TSINTACCIYAR MAGEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora