TSINTACCIYAR MAGE part 55/56

1.4K 66 0
                                    

_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
  _a true love story_

_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*Page 55/56*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Katafaren gida ne nagani na fad'a wanda ya amsa sunansa na gida, k'aton gate ne a k'ofar shiga har biyu 'daya a k'ofar gaba d'aya kuma yana ta baya ne, batareda sunga wani gateman ba sukaga gate yawangare kawai danhaka driver's d'in suka danna hancin motocinsu ciki, saida sukakai tsakiyan gidan sannan suka tsaya nan Amira da Aunty maryam suka fito suka budewa MUFIDA murfin mota tafito, har izuwa yanzu kuka take takasa dainawa hakan yasa bata'iya ganin gabanta saida Amira tarika hanunta, matan mahaifin MUFIDA ne su biyu da Ammin ta Sarah da y'ay'an ta su uku ne sukazo yiwa MUFIDA rakiya da dai sauran mutanen gidan,,,,....

Ta k'ofar babban parlor sukabi sanna suka haura sama suka wuce izuwa d'akinda yake mallakinta, a gefen gadonta suka zaunar da'ita sannan suka zauna suma, kwantarda kanta tai a kan shoulder d'in Amira tana kuka Amira sai rarrashinta take saboda itama kukan ne take,,....

Nasihohi sukadinga yiwa MUFIDA akan tazauna da mijinta lafiya tai hak'uri Allah kuma yabasu zaman lafiya da zuriya tagari daganan suka tashi suka wuce,, basufi 15mnts datafiyaba Angwaye suka shigo, suna shigowafa nan suka fara barkwanci dasu nusaiba sai dariya suke, ganin lokaci narafiya yasa Rayyan yakatse wasan yatashi yafara magana "to Alhmdllh jama'a dikkannin yabo da godiya su kara tabbata ga ubangiji halitta MUJAHID da MUFIDA yaudai Allah yanunamaku wannan ranar ta farinciki ranarda kuka dad'e kuna jiran zuwanta yau kunzama ma'auratan juna abunda kawai yaragemaku shine hak'uri dakuma zaman lafiya Allah yabaku zaman lafiya yabaku zuriya mai albarka wacca duniya gaba 'daya zatai alfahari da'ita Allah yakawarda fitina a tsakaninku yakuma k'aramaku dank'on k'auna, yaudai TOM yamallaki Jerry d'insa wasa yak'are anzo k'arshen wasan jenan" yai maganar yana murmushi haka shima MUJAHID murmushin yake su Amira kuwa dariya suke, kallonsu Amira yai yace "to aminan amarya ko akwai mai magana acikinku ne"  Amirace ta mik'e tsaye tareda fadin "eh akwai" sanna tafara magana "Alhmdllh....Alhmdllh.....Alhmdllh tabbas komai yai farko to zaiyi k'arshe yaudai MUFIDA tazama ta MUJAHID mallakinsa matarsa ta sunnah to MUJAHID da MUFIDA Allah yabaku zaman lafiya yasa wannan soyayyar tad'ore har abada Allah yabaku zuriya d'ayyiba munaso nanda 9months muzo suna muna maku fatan alkhairi a rayuwar aurenku" tana gamawa ta zauna nan sauran suma suka tashi kowa dai yai nasa maganar ta fatan alkhairi daganan akayi siyan baki Rayyan yabiya k'udi sannan suka tashi zasu wuce kasancewar dare yanayi,, har sunfito k'ofar parlor sai Amira tace "kai barrister dama nayi kwanciyana anan wallahi gobe idan kunzo sannan muwuce" zaro idanuwa Rayyan yai sannan yace "ruafawa kanki asiri Amira kar MUJAHID yau yamaki kuka zakihanasa yin rawar gaban hantsi" nanfa suka kwashe da dariya MUJAHID yakaimasa dukan wasa ya kauce sunata dariya,,,....

Saida yarakasu har gun motocinsu suka shiga suka wuce gate yarufe sannan yadawo ciki,,,.....

Cikin sallama yabud'e k'ofar d'akin yashigo har yanzu tananan gunda yabarta a zaune, wani irin murmushi yai sannan yak'araso yazauna dab da'ita, cikin fara'a yace "a,a my Jerry yaukuma fuskar rowanta akeman baza'abud'eman ba naganta" shuru tamasa batace uffanba, jin tayi shuru yasa yakai hanunsa ahankali yad'aga mayafin saiga kyakkyawar fuskarta ta bayyana, tasha make-up amma saidai make-up dik yab'aci da hawaye, murmushi yai sannan yakai hanunsa d'aya yarik'o gementa yad'ago da fuskarta yaduk'o yak'uramata fararan idanuwansa yana kallonta cikin murmushi, ahankali yahuramata iska izuwa fuskarta saita kumshe idanuwanta sannan tabud'esu tad'ago tak'uramasa daran daran idanuwanta dasuka sauya launi izuwa ja saboda kukanda tai, murmushi yai sannan yakai bakinsa yazura harshensa yalashe dik kwallanda suka zubomata sannan yace "sam kwallah basu dace da wannan kyakkyawar fuskarba murmushi da dariya sune sukafi dacewa da'ita saboda haka dan Allah my only na kidaina man asarar hawayena kinji ko saboda yanzu kinshigo rayuwarda ba'azubda kwallah acikinta" murmushi yasakeyi yace "meyasa kike kuka my only na ko auren ne bakyaso kokuma nine bakyaso dai" kallonsa kawai take ko kiftawa batayi, saida yahuramata iska sannan talumshe idanuwanta tabud'e sannan tahararesa taredayin murmushi ta sadda kanta k'asa cikin yanayin kunya tace "a,a inatinawa ne da daddy na lokacinda za'akaini gidan hamma faruk irin hud'ubarda Abba taju yaman shima irinta yaman wannan yasa natina dashi nakasa hak'uri saida na zubda kwallah, ganitai yab'ata fuska saboda kawai takira sunan hamma faruk,,,"....

TSINTACCIYAR MAGEWhere stories live. Discover now