TSINTACCIYAR MAGE part 47/48

1.2K 62 3
                                    

_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
  _a true love story_

_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

  _*Page 47/48*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Kai tsaye hanyarda zata sadasu da fadar sarki akawuce dasu, kamar nacewa MUFIDA tawaiga tana waigawa kuwa saita zaro dara daran idanuwanta takafe wanda tagani da mayun idanuwan nata,,,.....

Tsintsar mamakine ya bayyana k'arara a fuskarta ganin Rayyan tsaye tareda wasu kyawawan y'ammata twin's larabawa shar dan ko hausardasuke ma dakaji kasan basu iyataba, kasancewar baigantaba yasa tajuya fuskarta tacigaba da tafiya,,,,"...

K'ofar shiga fadar ma tsare take da dakaru hud'u kowanne rik'e da bindiga nan Abbu yashiga gaba sukuma sunabin bayansa, cikin sallama suka shiga ciki mutanen fada suka amsa masu cikin sauri sarki yataso yazo yadurk'usa cikin fara'a yakwashi gaisuwa gun Abbu nan Abbu yad'agosa suka rungume juna sannan abbu ya sumbacesa a goshi nansuka gaisa cikin yarensu na larabci,,,.....

Bayan sungaisa da Abbu sannan yajuyo yabama Abban ammar hanu sukai musabaha sannan suka sumbaci juna a kunce, bayan sungaisa yajuyo yakalli su MUFIDA yafara masu magana cikin harshen larabci nanfa su MUFIDA akai tsuruu ana kallon juna, Abbu dariya yai sannan yafad'awa sarki ai su basajin yaren saidai hausa yai dariya sannan yamasu hausa nansuka gaidasa, tinda MUFIDA taga sarki taketa kallonsa a zuciyarta tace "wannafa mai kama da mr man d'ina kaddai ace shine mahaifinsa kuma shine mahaifina wayyo Allah Allah yasa bahaka bane dansuma twin's d'inda nagani a waje kamarsu d'aya da mr man to kodai nanne gidansu" hakadai taita sak'e sak'e a zuci,,"....

Bayan sungama gaisawa sai aka masu iso izuwa cikin gida, sashen tsohon sarki da matarsa wato d'anuwan Abbu aka wuce dasu, suna isa sarki yataso yana dariya yazo suka rungume juna shi da abbu suna gaisawa bayan sungaisa sannan su Abban ammar dasu MUFIDA suka durk'usa suka kwashi gaisuwa, bayan sungaisa saiga gimbiya matarsa hajiya zainab tafito nansuka gaisa da abbu sannan su MUFIDA suka gaidata,  suna anan sashen saiga wata kyakkyawar mata tareda kyawawan y'ammatanda MUFIDA tagani tareda Rayyan sun shigo dakaru mata guda hud'u suna bayansu,  nansuka shigo suka gaisa, y'ammatan nan sukazo sukaja hanunsu MUFIDA suna dariya suka fita itakuma momyn faruk sarauniya Sainah tawuce da'ita izuwa sashenta su abbu da abban ammar kuma aka kaisu masaukinsu,,,.....

Sai dare sannan su MUFIDA suka dawo masaukinsu nan sukai wanka sukai sallah suka sauya kaya sannan suka kwanta, around 8pm aka aiko da wasu hadimai hud'u suka kawomasu abinci, girke girke ne kala kala sai wanda kakeson ci hadda na gida Nigeria, 9pm sarki mai ci yanzu yashigo suka gaisa sannan yace sufito sashen sarki za'ayi magana nansuka shirya sannan suka fito atare,,,,".....

Kai tsaye sashen sarki tsoho suka wuce, suna isa MUFIDA tahango wani mai kama da sarki na yanzu nantake taji gabanta ya fad'i, bayan sun isa sunzauna sai Abbu yafara magana "to Alhmdllh kamardai yanda kukaji tajudeen shine mahaifin MUFIDA kuma shi kansa yasani saidai asakamon wani laifi daya aikata shiyasa bai fad'amaku yanada ita ba kuma yamanta da'ita dikda kuwa da tsawon shekarunda yakwashe bai haihuba, MUFIDA" Abbu yakira sunanta wacca kwallah sukariga sukagama wankewa fuska tad'ago ahankali takallesa yace "wannan shine mahaifinki doctor tajudeen",, taju ne yace "Abbu kana nufin kace wannan y'atace" murmushi abbu yai sannan yace "tabbas kuwa y'arkace MUFIDA wacca ka haifa da shahida kukagudu kukabarta" duk'arda kansa yai kasa nantake kwallah suka fara zubomasa, mai martaba ne yace "mufa kunsakamu acikin rud'ani kumana kyakkyawan bayani saboda mufahimta" abbu yace "yanzu kuwa zakuji" nantake yabasu labarin komai tin had'uwarsa da shahida har girman MUFIDA da irin rayuwar jin dadinda tai a hanun dady,,,"....

Labarin yamatuk'ar bama su sarki mamaki da al'ajabi dan tinda suke da taju baktab'a basu wannan labarinba, shikuwa banda zubda kwallah ba abunda yake hakama MUFIDA kuka take sosai,sarki mai martabane yafara magana "hak'ik'a tajudeen kayi abunda yamatuk'ar b'atamin rai sannan ka aikata babban kuskure wanda badan MUFIDA tasami kyakkyawar rayuwa ba da bazan tab'a yafemakaba amma yanzu zakaci darajar Ahmad" abbu ne yaisaurin karb'an zancen "yanzudai ai Alhmdllh dama abunda mukeso kusanta kusan jininkuce sannan shima yasan yanada y'a itama kuma tasansa sannan yafad'amana inda mahaifiyarta take domin akaita taganta dikda basunemetaba",,,....

TSINTACCIYAR MAGEWhere stories live. Discover now