_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
_a true love story__*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_
® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*Page 45/46*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_
Shuru yaratsa d'akin nawasu y'an dak'ik'u can Abban ammar yad'ago yafara magana "hak'ik'a yau itace ranarda yaya Ahmad yace zatazo kuma yai bak'incikin zuwanta saidai naji dad'i da Allah yasa koda tazo baya raye bare ya zubda kwallah" hankalin kowa akansa yake domin sauraron abunda zai fad'a, saida ya kalli MUFIDA cikin yanayin tausayi yace "MUFIDA dan Allah inaso ki d'auki wannan al'amarin a matsayin k'addara kibarsa a matsayin *KUNDIN K'ADDARA* ki tabbas komai yasami bawa to *MUK'ADDARI* ne daga ubangiji dolene saiya sameka" Sam bata fahimci abunda yake nufiba danhaka saiyacigaba da maganar,,,....
"Tabbas MUFIDA ba y'arsu bace basune suka haifetaba" dasauri MUFIDA ta d'ago kanta ta kalli Abban ammar nantake idanuwanta suka cicciko da kwallah, cigaba yai da magana "MUFIDA y'ar amininsace Alhj TAJUDEEN ABDUSSALAM d'an d'an'uwanka Abbu sarki Abdussalam tsohon sarkin k'asar BAGDAAZ yankin Arab's,, shekara ashirin da biyar da suka wuce a makarantar TURKEYSH INTERNATIONAL SCHOOL dake k'asar TURKEY wato makarantar yaya Ahmad yakammala karatunsa nazama cikekken likita, anan ne yahad'u da abokinsa tajudeen, cikin k'nk'anen lokaci shak'uwa tashiga tsakaninsu kasancewar abu d'aya suke karanta, sun shaku sosai dik inda kaga yaya Ahmad to zakaga tajudeen anan idan kana neman d'aya kaga d'ayan to kamar kaga d'ayan ne saboda komai nasu d'aya ne saidai inda sukeda bambamci shine tajudeen yana neman mata sab'anin Ahmad, yaya Ahmad yayi iya k'ok'arinsa dan yaga tajudeen yadaina neman mata amma yak'i gashi kuma gida anyi anyi yafitarda mata yai aure kuma yace saiya kammala karatunsa sab'anin yaya Ahmad dahar ansaka masa rana",,,,.....
Suna cikin karatu akai auren yaya Ahmad da Fatima idan baku mantaba ma har tajudeen yazo shine yamasa babban aboki a auren kuma su sarki dik sunzo, bayan angama shagalin bikin suka koma school suka cigaba da karatunsu,,,, suna gab da kammala karatun tajudeen yahad'u da wata budurwa mai suna SHAHIDA it's shuwa Arab ce amma mahaifiyarta yar turkey ce, yafara soyayya da'ita kasancewar tajudeen akwai wayou yasan dik yanda zaiyi yaja hankalin yarinya nantake yasiye zuciyar Shahida tafad'a tarkonsa saidai ita son aure takemasa sab'anin shi dayake mata son sha'awa, ahankali ahankali yafara Jan hankalinta harta amince dashi yafara kusantarta batareda sunyi aure ba, lokacinda yaya Ahmad yaji zancen nanfa yai cikinsa yanamasa masifa meyasa shi baya tinani meyasa bazaiyiwa kansa wa'aziba yadaina wannan banzar rayuwar k'azamar rayuwa idan dai har dagaske yake toya aureta mana, amma kasancewar tajudeen yariga yai nisa bayajin kira saiyai banza dashi yawatsarda zancensa",,,.....
Haka sukacigaba da wannan bak'ar rayuwa batareda sunyi aure ba, Shahida bata ankaraba kwatsam saiga ciki ya bayyana a jikinta, hankalinta yamatuk'ar tashi nantake taje tasami tajudeen tafad'amasa, shima hankalinsa yatashi sosai saboda dik y'ammatanda yake mu'amala dasu gwangwazajjin matane basa yarda su d'auki ciki amma ita wannan shine ya tirsasat dole badan halayyarta bane to yanzu yazaiyi da'ita, nantake dabara tafado masa saiyacemata kawai a zubda cikin daga baya saisuyi sure nanfa tace ita wallahi ita tinda tasab'awa Allah nafarko bazata sakeba bazata zubda cikinba saidai yasan yanda zaiyi saboda idan gidansu akasani wallahi tashiga tara mahaifinta ko kasheta zaiyi, hankalinsa yatashi sosai dan shid'inma tsoron nasa iyayen susani yake musamman dayakasance gidansu gidan mulki da sarauta ne sarki mahaifinsa sarki zai iya korarsa",,,....
Nadama iya nadama Shahida tayita ta d'ora hanu a ka tana kuka sosai saboda tasan tariga data rusa kyakkyawan ginin rayuwarta, tashi tai tafita batareda sungama yanke hukunciba saidai itakam tariga tayanke nata hukuncin,,"....
Yaya Ahmad na zaune tajudeen yazomasa da zancen nan yaya Ahmad yaketinamasa maganarda yamasa a baya amma yaki yanzu gashi tace bazata zubda cikinba kuma tabbas idan tahaihu shi zata kawowa jinjirin,, tin ranar basusake ganin shahida ba har saida suka kai saura sati d'aya suyi graduation sannan tazo da katon cikinta tafad'amasa yazama da shirin karban babynsa dan bazai tafi yabarta dashiba,,"...
