27

3K 296 6
                                    


                           *MACE A YAU*
                                     27

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Sati daya kenan da tafiyar su Subay'a komai na gidan a hannun Sulaim yake wani sabon responsibility ya hau kanta tamkar Marar gidan haka take ji. Alarm din dake gefen bedside drawer ne ya fara ringing alamar lokacinda akai setting dinshi yayi. A hankali ta bude idonta Wanda yake Cikeda bacci tasa hannu ta kashe tareda gyara kwanciyarta don baccin bai isheta ba, sede ta kasa komawa saboda yadda ake ta kiraye kirayen sallar subhi, haka ta mike Tana mutsitsika idanta tayi zauna bayan tayi addu'a ta shiga toilet, wanka ta Fara yi sannan ta daura Alwala ta fito. Bayan ta Idar da sallah ta wuce kitchen inda ta tarar har su Atika sun Fara aiki, gaiswaw sukai sannan ta dubi Atika tace

Atika jeki ki tashe su kiyi musu wanka Bari na karasa girkin.

Tohm

Ta amsa mata sannan ta wanke hannunta ta fice don aiwatar da umarnin Sulaim, kallon kayan da Atika ta fito dasu tayi, wasu ta mayar ta dakko wasu kayan ta Fara aiki, tanayi tana Azkhar baki daya zuciyarta na rage damuwar da take jibge a ciki.

Daki ta koma lokacin Atika ta gama shirya mata su Muhammad suna zaune kowanne rikeda madara cikin glass cup, Tana shigowa ta kallesu Ahmad yace

Anty morning

Kanshi ta shafa tace

Morning Boy.

Ahmad ta dauka Wanda idanunshi suka cicciko da kwalla it's normal kullum se yayi kukan Papa da Mimi har ta Saba. Jijjiga shi tayi a ranta tana fadin

Inama ace inada wanda zan kwanta a jikinshi nima nayi kukan rashin Papan naku da nayi baku kadai kuke missing dinshi ba.

Seda yayi shiru kafin ta ajeshi ta nemi Abaya fuschia pink ta saka sannan ta daukesu suka fito dining, serving dinsu tayi sannan ta Fara cin Nata tana duba time don Kada suyi latti. Suna gamawa ta dakko lunch boxes dinsu, school bags dinsu da Nata suka fito parlour anan wayarta ta Fara ringing, Duk tunaninta ma Salim ne don rashin Ja'afar, rashin Junaid yasa ta saki jikinta sosae da Salim sukai wani Irin sabo sosae me wuyar faduwa Dan hausawa sunce a rashin uwa akanyi uwar daki. A rashin wannan gwarzon mazajen guda biyu da zuciya ta kasa kankare su tayi Abota da Salim.

Yaya ina Kwana

Ta fada Bayan tayi picking, muryarshi deep da dadin saurare yace

Yakuke gaba daya.

Lapiya lau

Ta bashi amsa Tana zura key cikin handbag dinta,

Megadi yace min baki fita da motar napep kuke Hawa me yasa?

Kanta ta girgixa tace

Babu komai.

Kyautar Batayi miki ba?

Da sauri tace

A'a Yaya dama I was planning yau mu fita da ita.

Sounds better, se munyi waya Anjima ki gaida yaran.

Kafin ta bashi amsa ya kashe, ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki gaba daya wani yanayi ya mamaye mata jikinta. A hankali ta taka zuwa wani couch dake parlon ta ciro key din motarshi da Tun ranarda zai tafi Estonia ya bata akan suna zuwa ko ina Tunda yasan ta iya driving don dawowarta Nigeria lokacin rasuwarsu daddynta Tana cikin mental breakdown Baba yasa Jawad ya ke koya mata don hakan ya dauke mata hankali da kewa amma ko kadan a lokacin umarni kawai take bi Don ba yadda xatayi amma Lokaci gani take meye sauran farin ciki Bayan rashin iyayenta babu wani abu da ya rage Amma dake Allah Allah ne se gashi ba'a shekara ba ta koma normal self dinta.

Mace a yau! Donde viven las historias. Descúbrelo ahora