52

3.2K 367 10
                                    


                          *MACE A YAU*
                                  52

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

*Of course, you know that this page is yours the people of Maman mama novels, ina godiya sosae da goyon bayanku.....*

A'ISHA ASHIR

Bari mu leka muji yadda rayuwar Wannan bayun Allah ta kasance bayan Auren Khulthum.

Rayuwa ta mika musu, abubuwa sun sauya ciki Harda Fara makarantar Aisha wadda ta samu gurbin karatu cikin North west University wadda iyayen Ashir suka dauki nauyin karatun. Amir shima yayi nisa cikin karatun da yake ga kuma budi da Allah yayi mishi gurin kasuwancin da Khulthum ta dade tana mishi dariya, wato saida gwanjo. Sede gashi Allah ya albarkaci abin har ya fara gyara musu dan gidan da suke ciki, wannan abin ba karamin faranta ran Malam Suleiman yayi ba domin yasan tabbas Allah ya amshi adduar da ya dade yana Yi.

Ranar wadda ta kasance asabar tun sassafe A'isha ta tashi kamar yadda ta Saba, babu Wanda ta tada haka ta fito daga daki ta Debi ruwa tayi wanka sannan ta dawo daki ta gyara kanta ta shirya cikin doguwar rigar farin material me fatsi fatsin Baki. Dukda ba mai tsada bane amma yayi mata kyau, fitowa tayi ta hura wuta sannan ta Fara Sharar tsakar gida, ta hada wanke wanke tayi a lokacin Amira ta fito Tana ta murtsuka idanu, kallon A'isha tayi tace

"Kai Yaya A'isha duk ke daya kika yi wannan aikin?"

Harara A'isha ta makawa Amira tare da cigaba da aikinta sannan tace

"Waye zai biyewa lalacin ki, kamar ba mace ba ace se yanzun kike tashi a bacci"

Baki Amira ta turo tace

"Rayuwarki tayi tsauri Yaya A'isha, amma ina yiwa Yaya Ashir samun ki"

Sunan kawai da Amira ta ambata Seda wani sihirtaccen murmushi me kayatarwa ya kubce daga kyakyawar fuskar A'isha, Dama ita din ma'abociyar murmushi ce amma na Ashir na daban ne. Ita kanta ko cikin mafarki ko burika Irin nata bata taba tunanin zatayi soyayya da Ashir ba, Ashir daban yake wanda samun mutum kamarshi se an sha wuya, kullum rana se A'isha ta kara godewa Khulthum akan bar mata Ashir da tayi. Halayenshi kadai sun isa ya sace zuciyar mutum dashi. Mutum ne me takatsantsan akan dokokin Allah, hardly Kaga ya ketare abinda Allah da manzonshi sukai Hani akan, mutum ne that's very caring dukda ya kasance baya kasar amma bai taba jera hour biyar ba tareda ya ji muryar A'isha din ba, hakan yasa suka mugun sabo da kuma shakuwa da junansu.

Da farko kasa sakin jikinta tayi saboda tana ganin kamar ana amfani da ita ne wajen huce haushi Amma a hankali yadda yake tsumata da Wannan zumar tashi yasa ta bada Kai bori ya hau. Cikin nitsuwa suka dinga shimfida soyayya me Cikeda amana, karko da kuma fahimtar halayen juna, cikin kankanin lokaci sukai clearing differences dinsu hakan yasa basu sha wahala ba.

Amira dake gefe tana kallon Yayar tata da tayi zurfi cikin tunanin Ashir wanda ko bata fada ba hakance don wani Irin soyayya me rikitarwa ce tsakaninsu. Daki ta koma jiyo ringing din wayar A'ishan, murmushi tayi ganin Ashir dinne hakan yasa tayi saurin kai wa A'ishan wayar tareda fadin

"Gashi nan dan halak ya huttar dake"

Maficin dake hannunta ta wullawa Amirar wanda ta zulle Zuwa daki Tana dariyar kunyar A'isha. Se kira na biyu ta samu ta dauki wayar dan tuni wancan call din ya katse

"Yau Queen da rowar murya kika tashi? "

Dan murmushi tayi tace

"Ni na isa, tana daki wayar"

Kanshi ya jinjina tareda fadin

"Dan Allah Queen ki dinga hutawa da Wannan ayyukan da kike, ace kullum mutum tamkar inji yayi ta aiki babu Hutu Haba mana! Shiyasa dole a matso da date din aurenmu!"

Dariya ta saki a hankali wadda take nuna Irin nishadin da take ciki, shima lumshe idonsa yayi yace

"You will not answer me right? Anyways Dama zan miki zancen next week zan dawo"

Da sauri ta Mike wani Irin farin ciki Marar misaltuwa ya mamaye mata jikinta da zuciyarta tace

"I'm so happy blood, Awnnnn!"

Haka suka Bata Lokaci me tsayi suna waya har ta kammalla ayyukanta, lokacin sukai sallama shima don ganin mutanen gidan sun Fara fitowa ne. Tunda Mama ta fito take shiwa Aisha albarka, har zuciyarta take jin dadin wannan halin na A'isha ko ta so ko taki A'isha tafi Khulthum sau dubu kuma Tun ranar da Khulthum ta bar gidan taji wata nutsuwa ta saukar mata, taji tamkar an sauke mata wani babban nauyi ne daga kanta, haka bata ji wani kewar ta ba, to ta yaya zataji Bayan nemar mata magana kawai take yi, yanzun hankalin kowa ya kwanta tunda bata nan.

Bayan sun kammalla cin abincin Baba ya dubi A'isha yace

"Ya kamata kuje ku ga dakin 'Yar uwarku, ko mai ya faru ina son ku manta da hakan, Ummu_Khulthum yar uwarku ce"

Kai A'isha ta gyada tana jin komai ya wuce dama ita bata rike Khulthum ba don kuwa tasan ba'a canjawa tuwo suna Yana nan a tuwonshi! Tare suka shirya Mama kamar ta Goya su da taji inda suke haramar Zuwa, dukda Tunda Khulthum ta saka kafarta ta bar gidan babu Wanda ta taba Kira da sunan gaisuwa, se Mama dince kan kirata time to time.

Tunda aka sauke su A'isha kofar gidan Baki daya suka saki Baki da hanci suna kallon wannan tafkeken gidan, mamaki cike a zuciyar kowannensu saboda babu Wanda yazo ganin daki don ba'ayi rabuwar arziki ba Balle har su raka ta in fact lokacin bikinta ma gaba suke me tsanani. Seda A'isha ta kira Mama ta tabbatar mata gidan ne sannan suka kwankwasawa, kasancewa securities din sun saba da kawayen Khulthum masu didif didif a gidan suka Barsu suka shiga tareda nuna musu part din Khulthum din. Daidai zasu shiga Musbahu na fitowa daga part din Sanye da jallabiya brown, Fuskarshi babu digon annuri an dinke tamkar anyi masa sakon mutuwa, a tare suka gaishe shi kawai se ya samu kanshi da amsawa saboda kana kallon Amira Kaga Khulthum saboda yadda suke kama da junansu sosae,

"Ku shiga ciki mana tana nan "

Ya fada Yana basu guri tareda Kare musu kallo, kana kallonsu kasan talauci yana damunsu Amma a idanunsu zaka fahimci they're contented. Gaba daya bin parlon sukai da kallo saboda tunda suke a rayuwarsu basu taba gani Balle har su shiga makamancin gurin. Zama sukai kan kujera shi kuma ya nufi dakin don kiranta, tana kwance inda ya barta ko hannu ta Kasa dagawa, kamshin turaren shi da taji yasa ta mugun firgita don babu Abinda take tsoro yanzun a rayuwarta shi ne Musbahu, azabar da yake mata Allah kadai yasan hakan amma tasan kaddarar ta ce hakan!

"Kinyi baki"

Bai jira amsarta ba ya fito Bayan yasa a kawo musu abinci, baki daya A'isha tsoron karbar da Khulthum zatayi musiu take, da Khulthum bata da komai take rashin mutunci Balle gata da kyakyawan miji na nunawa duniya, ga kudi da katon gida. Ai se abinda yayi gaba, suna nan Zaune zaman kurame Don babu me magana cikinsu se gata ta fito, ta kintsa kanta cikin voile Red dinkin skirt da Riga, tayi kyau amma tayi Baki, idanunta sunyi ja tareda fadawa ciki, fuskarta kadai zaka kalla ka gano tsantsar damuwa da tashin hankalin da take ciki, tana ganinsu A'isha ta nufe su da sauri tareda rungume su dukkansu, sunyi mamaki canzawar ta da kuma Wannan ramar da tayi.

Tsakiyar su ta shiga tana jin kamar an jefata a Aljannah, dadi kamar me daga baya ta kwashesu Zuwa dakinta tana ta musu hira har suka saki jikinsu suka ci abinci. A'isha karshen gado ta koma ta kwanta tare da amsa kiran wayar Ashir, tunda ta Fara wayar hankalinta Baki daya ya bar dakin da mutanen dakin, Khulthum na ankare da ita Tana ta son jin da wanda A'isha ke waya hakan yasa ta tambayi Amira wadda ta bata amsa da

"Yaya Ashir ne"

It takes a huge of sacrifice typing this peace..... Dan Allah kui manage dashi.

Shatuuu ♥️

Mace a yau! Where stories live. Discover now