54

3.2K 348 22
                                    

                        *MACE A YAU*
                                    54

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

*Umma dandago,Rashida muktar,Hafsat el-marzuq,maimuna el-marzuq, Ummu Lubna, Nobles cakes n more and all other well wishers, lovers behind the curtain.... Nagode sosae Allah ya bar zumunci da soyayya*

Dauraye hannunta tayi a sink din toilet din sannan ta kashe tareda kallon fuskarta jikin mirror din dake saman sink din. gashin da ya zubo mata wajen idanunta ta dauke da hannuwanta sannan ta fito baki daya daga toilet din, babu kowa cikin hadadden bedroom din Nata wanda dukkan furniture din dake kafe a ciki yake golden da Baki, sunyi kyau sosae, kujerar dake gaban dressing mirror ta jawo ta zauna tareda goge jikinta dake smooth yana ta daukar idanu yayi shar dashi Irin glow dinnan. Cikin hanzari ganin lokaci ya fara tafiya yasa tayi saurin shiryawa cikin wata Maroon exclusive wax da fari dinkin skirt da Riga me Peplum, tayi mata kyau abinka da farar mace wadda take ganiyar kuruciyarta, ga soyayya da kulawar miji duka, turarrukan ta ta fesa sannan ta fito Zuwa wani tamfatsetsen parlor me balain kyau, kujerun ciki da carpet din yan Persia ne, kalarsu kalar furnitures din bedroom dinta ne wato gold da Baki, wani corridor ta bi wanda aka Jere kananan frames na flowers, carvings da portrait innovations se hakan ya kayatar da gurin. Kofa ce ke facing gurin, ta murda a hankali ta tura kofar yana tsaye ya juya baya da dukkan alamu links Yake daurawa a hannun long sleeve coffee top din dake Sanye jikinshi, a hankali ya juyo Yana kallonta wani nishadi na kara shigarshi, yana jin nutsuwa hade da mugu mugun sonta na bin dukkan wani channel da jini ke ratsawa.

Sulaim na isa inda yake fuskarta da murmushi ta dan rankwaba tare da fadin

"Ina Kwana? "

Hannunta ya kamo cikin nashi yana kare mata kallo tareda fadin

"Kinyi kyau Dove, da duk wannan kwaliyyar Za'a tafi school din? "

Bakinta ta turo tace

"Ina kwalliyan yake ne? Powder ce kawai na shafa se kwalli da balm! "

Dariya yayi ganin yadda ta Bata rai, cikin kwantar da murya yace

"Bance wani abu ba fa, Ehen yau class din Dr. Ammar kuke dashi ko?"

Kanta ta gyada tana maida hankalinta Kan gyara mishi link din da kuma collar rigar tashi,

"He's not coming, so ina ganin ba se Kinje ba"

Wani karamin ihu ta saki tana fadin

"At least someone can rest"

Bakinshi ya tabe yana Mika mata wayarshi yace

"Lazy fellow! "

Kafadarta tayi shrugging Irin Kara fada dinnan, sannan suka fito Zuwa parlourn inda ya zauna suma su Ahmad da Muhammad an shiryasu cikin uniform. Seda ta gama shirya breakfast din kan dining mat dake ba kowanne Lokaci bane suke ci kan table ba, suna kamalla breakfast din suka Mike kowannensu na kokarin fita inda ya dace, kallonta yayi bayan ta rakasu bakin mota yace

"Dove Anjima zaki fitan? "

Kanta ta gyada tace

"Eh Inshaaa Allah Zamu fita tareda su Aimana "

Kanshi ya gyada yace

"Na bar miki sako kan gado, Allah ya kiyaye hanya"

Godiya tayi mishi yana harar ta Daga haka sukai sallama ya wuce ita kuma ta koma ciki ta Fara gyara inda ya dace da taemakon Nanny su Muhammad. Parlor ta dawo ta zauna Tana kurbar tea tareda kurawa wani frame dake kan center table din ido, hoto ne Daddynta da Mummynta, Junaid da ita, idan zata iya tunawa wannan hoton anyi shi lokacinda ta gama primary ne akai mata graduation party, tana ta dariya dukkan wushiryar ta siririya me kyau ta bayyana haka dimples dinta masu matukar daukar hankali sun lotsa, hannunta cikin na Junaid wanda yake dariya da sauran iyayensu, a hankali ta kai hannunta ta dauki hoton wasu abubuwa na tsirga mata, hakika tayi kewar wannan fuskokin da ace suna da rai ko wanne irin farin ciki zasu kasance ganin sun auri junansu. Allah kadai ya san Irin murnar da zasui, Allah dai ya jikansu ya rahmushe su yasa sun huta, Tana fatan su kasance tare a Aljannah don ko bata fada ba tana kewarsu dukda bata rasa komai ba amma iyaye daban suke.

Mace a yau! Where stories live. Discover now