Page 2

5.4K 276 5
                                    

Zuhraa❤❤
            (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
             ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 2

Malam Abubakar jauro wadda aka fi sani da buba likita su biyu rak iyayensu suka haifa dashi da kanwarshi nana fadimatu ana ce mata gaaji wato auta da fulatanci asalinsu 'yan jihar Adamawa ne karkashin karamar hukumar fufore sunan kauyensu Gurin, gari me tarin ni'ima da albarka gari ne na asalin fulani sbd hausa yayi musu karanci suna kan border ne na nigeria da cameroon suna da yawaitar jami'an tsaro a garin nasu, buba ya gado mahaifinshi jauro ne gurin bada maganin gargajiya shiyasa ake mishi lakabi da likita ya tsani boko a rayuwar shi yayin da kanwarshi gaaji ke mutuwar son boko tana zuwa nan government school dake garinsu din yayin da buba sede yabi babansu jeji kiwo da neman magani, gaaji na jss 3 Allah yayi wa mahaifiyarsu rasuwa ba'a wani jima ba mahaifinsu ma yace ga garinku, bayan rasuwar iyayennasu ne buba yaci gaba da kula da dukiyoyinsu da kuma kanwarshi gaaji har ta kammala secondary inda ya aurar da ita anan karamar hukumar fufore, bayan auren gaaji ne shima yayi aure ya auri wata yarinya ana ce mata hanse sam hanse bata da kunya kuma irin masifaffun yarannan ne ta aureshi ne sbd kudinshi don ba lefi yana da arziki garken shanu uku da gonaki hudu mahaifinsu ya bar musu, bayan auren su shekara dai-dai har biyar bata yi ko batan wata ba a lokacin gaaji na da 'ya'ya uku Abubakar(hamma), uwani, se Amadu sossai zumuncin su yaja baya sbd makircin hanse.
Wata rana malam buba yaje kiwo yayi nisa sossai a kiwonshi ya fara jin kukan jinjiri ya kasa kunne sossai sbd ya tabbatar ai kuwa da gaske kukan baby yake ji a hankali ya ringa bin kukan har ya iso gurin ya kyakyawar yarinya jaririya sossai don wannan baza ta wuce kwana uku da haihuwa ba a cikin farin showel da riga da wando na babies me tsada da warworo a hannunta daga gani na goal ne da sauri yazo ya dauki yarinyar a take yayi fito shanukanshi suka hade kansu suka kama hanyar gd, tun daga bakin kofa ya fara kwala kiran hanse, hanse da sauri ta fito na'am malam ko fe'i(me ya faru)? Yace kinga Allah ya bamu 'ya tsab ya bata labarin inda ya samu yarinyar ai kuwa hanse tayi tsalle ta dire tace wlh baza ta rike 'yar tsuntuwa ba akan wani dalili au wato don bata haihu bane shine yake neman yi mata wulakanci da kyar malam buba ya samu ya shawo kanta akan zata rike ta kamar 'yarta ai kuwa yayi murna da sauri yaje kasuwa ya siwo wasu kayan babies din ya shiga garken shanunshi ya tatso madara ya kawo aka bata ya cire kayan daya tsince ta dashi yayi musu kyakyawar adana ya mata huduba da suna fadimatu(zuhra).
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah zuhra na da wata biyar da tsuntuwa sossai hanse ke kula da ita a hankali ibtila'i ya sauko ma malam buba duk anfanin gonanshi wuta ya kama cikin dare komai ya kone kurmus, shanukanshi suka dinga mutuwa har seda ya saura garke daya sossai yayi hkr don ya yarda da kaddara, a take mutanen gari suka fara kawowa hanse maganganu ai zuhra ce me farar kafa kafin su sameta ai suna da arziki se bunkasa yake amma daga ta shigo gida suka fara talaucewa blah blah blah surutai de Kala Kala ai kuwa hanse ta hau kai ta zauna ta fara hantarar zuhra, ta fita harkarta malam buba ne ze mata wanka in kuwa be mata ba sede ta zauna haka hanse ba ruwanta duk malam buba ya koma cinta, shanta, wankanta, kwanciya duk shine ga kiwo ga bada magani atake yayi tsufan dole sbd wahala ga talauci sossai yayi musu sallama, ana cikin haka hanse ta samu ciki murna a gurinsu kaman ba gobe har cikin ta yakai wata tara ta haifi 'yarta mace zainab suna ce mata jainabu tsakanin zuhra da jainabu shekara daya da wata biyu jainabu na da shekara uku hanse ta sake haihuwa ta haifi 'yan biyu hassan da hussaini.
Haka yaran suka taso da tsanan zuhra suka kafa mata karan zukaa ga wulakanci Kala Kala hussaini ne kawai ke mugun tausaya mata duk lokacin da aka hanata abinci shi zai dauki nashi ya bata sbd yasan za'a bashi wani, zuhra itace tallan nono, itace aikin gida, dibo ruwa, kiwon shanu duk wani aikin wahala zuhra ta iyashi baffan su ya sa su a makantar boko da islamiya zuhra na da mugun kokari sau daya aka fada mata abu ta rike shiyasa ake ji da ita a school dinsu a islamiya har tayi sauka hadda takeyi da karatun sauran littattafan musulunci, kawarta kwaya daya duk kauyensu shatu su biyu iyayensu suka haifa da ita da yayanta gidado suna ce mishi hamma gidado mahaifiyarsu sunanta husna suna ce mata chubado se mahaifinsu malam liman suna kiranshi baba.
Cigaban labari............

Zuhraa❤❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora