Page 10

3.4K 247 2
                                    

Zuhraa❤❤
          (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
             ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin



بسم الله الرحمن الرحيم

Page 10

Alhamdulillah jirginsu ya sauka lfy a modibbo Adama international airport a safiyar asabar su Abba ne da sauran convoy dinshi suka je dauko su, suna hanyar dawowa gida ne Aliyu ke fad'a ma Abba yadda sukayi da doctor, shiru Abba yayi yana nazarin maganan har suka karasa estate, a farfajiyar gurin suka samu 'yan gidan gabad'aya sun fito taryarsu, fito da maami akayi aka shige da ita part d'inta, Aliyu ma part dinshi ya shige bayan yayi hugging Ammie da Abbie da sisters dinshi, yana shiga ya samu zaid a kan doguwar kujera yana bacci, girgiza kai kawai yayi ya shige d'akinshi.
Bayan yayi wanka ne yasa kaya marasa nauyi ya fito parlor, har lokacin zaid na baccinshi duka ya d'aka mishi, ihu zaid yayi tare da salati ya mutsuke idonshi yana kallon Aliyu da ya 'bata rai kaman ba shi yayi dukan ba hararar shi yayi tare da cewa "A. A ribadu wani irin iskanci ne wannan daga dawowarka zaka sa mutum a gaba yanzu dan Allah me na maka ina bacci na me dad'i kazo ka katse min, ni wallahi na ma dauka aljani ne" murmushi Aliyu yayi don yana wuya ganin dariyarshi yace, "matsoraci kawai, kaman ba na muji ba? kazo ka shantake sai bacci kake har nayi wanka na huta, wai kai kazo tarya", ya karasa da kwafa, zaid zeyi magana kenan akayi sallama, zaid ne ya amsa tare da bada izinin shiga, Aida ce ta shigo da tiren abinci ta dangwarar a kasa ta juya zata tafi ba tare da ta gaidasu ba, wani gigitacciyar tsawa Aliyu ya daka mata "ke!! Wai ke wace iriyar marar kunya ce wato kin raina ni koh? Before da count of two kneel down there" a razane ta juyo ta duka kasa, harara ya daka mata da sauri ta gaidasu zaid ne kawai ya amsa, major kam harara ya kara bata, ya motsa baki kaman zeyi magana kuma se ya fasa, zaid daya lura da haka kuma yaga yana shirin mikewa da sauri yace mata "serve us" fasa mikewa Aliyu yayi tare da kwafa da sauri tayi serving dinsu ta mikawa zaid, taja center table ta daura ma Aliyu nashi, ta mike ta nufi fridge ta dauki ruwa ta zuba a set din cups da ke saman fridge din.
Ta dauko kenan tsautsayi yasa ta kwara wa Aliyu ruwan, saukan wani gigitaccen mari taji hagu da dama ihu ta saki kafin ta rufe baki ya zare belt ya fara jibgar ta, da sauri zaid ya mike yana shirin kwatan belt din turashi saman kujera Aliyu yayi, tare da fisgar hannunta suka shige d'aki ya sawa kofar key, seda yaga ta kusa suma tukun ya qyaleta ya shige toilet yana jan tsaki, mikewa Aida tayi da kyar ta bud'e kofar ta fice don tasan yasake tarar da ita wani dukan ne, a parlor tasamu zaid na cin abincinshi a ranta tace mugu kawai dan rainin sense yana ganin yaya na jibga na ko ya kwace ni, karamin tsaki taja ta fice ba tare da ta bashi second glance ba, murmushi kawai zaid yayi.
Se bayan la'asar Aliyu ya tashi daga baccin gajiyar da yayi bayan yayi wanka ya chanza kaya yayi sallan la'asar data wuce shi tukun ya fito, seda ya fito ma ya tuna d'azu yabar zaid a parlor, yasan haushi yaji yayi tafiyarshi, ga parlorn kaca kaca da abinci karamar tsaki yaja, ficewa yayi ya nufi part d'in mahaifiyar shi, ya shiga ba kowa a parlorn kasan haurawa sama yayi ya nufi d'akin Arfa yayi knocking tace "yes come in" bud'ewa yayi ya shige da sauri ta mike zaune tana shirin sauka daga kan gadon, hannu ya d'aga mata tare da cewa "na baki 10 minutes ki tabbatar kin gyara min parlor" be ko kara kallonta ba ya fice ya nufi d'akin Ammie knocking yayi daga ciki yaji ta amsa, shiga yayi ya sameta zaune bakin gado rike da waya a hannunta tana dannawa, karasawa yayi ya hau gadon ya kwanta tare da daura kanshi a cinyarta, murmushi tayi tare da shafa kanshi, yace "Ammie na ya muka same ku? Dazu bamu yi wani gaisuwan kirki ba" tace "lfy klau son ya gajiyar hanya fatan yabi jiki?" Gyad'a kai kawai yayi, ci gaba da shafa kanshi tayi, da kyar ya budi baki ya ce "Ammie am hungry" d'an hararar shi tayi tace "ba dazun Aida ta kai muku abinci ba ka dakarmin 'ya don kawai ta zubar maka da ruwa bada saninta ba, Aliyu ka rage zafin zuciyar nan taka baka san wace iriyar mata Allah ze had'a ka da ita ba" sossai ta mishi nasiha me kama da fad'a duk da ta san ba wani shiga fadan ze yi ba, don tun yana karami take wanna fad'an, har haddacewa tasan yayi zuwa yanzu kam, shiru ya mata be ce komai ba, girgiza kai tayi tace "toh mike in je in samar maka abunda zaka ci, don yanzu in na kira kitchen ma nasan ran kowa ne ze baci da fad'arka, in baka son komin maids kayi aure mna kowa ya huta ni ban ma ta'ba jin Ance ga buduruwarka ba" ta ci gaba da sababi tana ficewa daga d'akin, murmushi kawai Aliyu yayi, yana girgiza kai, shi har ya saba da sababin Ammie da maami ke shiga mishi yanzu kuma ba bakin, Allah sarki, Allah ya baki lfy maami.
Ammie ce ta shigo da sallama bayan fitanta da mintuna da plate a hannunta, tazo ta mika ma Aliyu, shagwa'be fuska yayi yace "Ammie hannuna fa na ciwo, kuma ban warware gajiyar hanya ba fa" murmushi tayi don tasan me yake nufi zama tayi a kusa da shi ta fara bashi suna hirarsu irin na d'a da uwa.

%%%%%%%%%%%%%%%%

Bayan malam ya shigar da zuhra d'aki ya fito d'iban ruwa lokacin hanse ta fito da mayafi ta fice daga gidan bin bayanta yayi ya rufo kofar gidanshi, ya koma d'aki da ruwan daya d'ibo a kofi, yana shiga ya shafa mata ruwan a fuska numfashi ta sauke tare da zabura zata fara magana baffa yace "fatima kiyi shiru yanzu dare yayi, ki je ki kwanta da safe in shaa Allahu na miki alkawarin baki labarinki". Dubanshi tayi tana share hawayen fuskanta tare da mikewa ta fice daga d'akin, girgiza kai baffa yayi yana me jin tausayin zuhra har cikin ranshi don yasan tayi kankantar shiga taskun rayuwa irin wannan, gashi zata ji asalinta be san ya abun zeyi affecting dinta ba, fita yayi ya je yayi alwala ya zo yana rokar mata sassauci a wajen mai duka.
Ta bangaren zuhra kuwa tana shiga d'aki ta kwanta da tunani kala kala a zuciyar ta, tabbas ita yarinya ce me basira sossai da hangen nesa sam bata sa wa kanta tsanar iyayenta ba, tana musu uzuri sbd bata san menene dalilin jefar da ita ba, duk da bata tabbatar ba, yanzu in ita shegiya ce fa?, ko 'yar mahaukaciya, haka ta dinga tunani har bacci 'barawo ya sace ta.



















#vote
#share
#comment


















'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now