Page 39

3.3K 199 27
                                    

Zuhraa❤❤
(The flower)

By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)


Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 39

Bayan wasu kwanaki

Sauri sauri gudu gudu Aliyu ya iso get d'in gidan a kafa knocking yayi sojojin dasu ke gadi suka bud'e mishi a take suka sara mai hannu ya d'aga musu ya bud'e brief case d'inshi ya ciro tickets guda hud'u ya mika musu, "akwai taxi a waje ze kai ku airport d'in" suka had'a baki wurin cewa "yess sir".......

D'akinsu suka nufa da sauri dan had'a kayansu, da hanzari ya shiga cikin gidan a parlorn sama ya same ta kwance tana danna waya "Aisha tashi ki d'ibi abunda zaki bukata zamu bar kasan nan" zaro ido tayi kaman gaske tace "meyasa major?" Tsawa ya daka mata "get up my friend, wlh bazan iya kara 30 mins a nigeria ba.......

Da sauri ta mike tana murmushin mugunta ta nufi d'akin ta ta had'o kayan ta, tana fitowa ta samu shima ya gama had'a nashi fitowa suka yi suka nemi taxi cikin bacin rai tace "yanzu major duk motocinka ga motocina ace ta taxi zamu airport" be tanka ta ba ya bud'e baya ya shige bayan me taxi d'in ya sa musu kaya a mota......

Ba yadda ta iya tana tura baki ta shige ita ma, kallon windown motan ya ke yi yana jin wani irin kunci a zuciyar shi, me yake damunshi ne? Ya tambayi kanshi, da aka zo wuce kofar gidansu wani hawaye yaji yana cika mishi ido da kallo ya bi gidan har suka wuce, suna isa airport basu wani 'bata lokaci ba jirginsu ya d'aga zuwa kasar Holland.......

********

5 months later

Ammie ce zaune a parlor tana kuka bilhakki, maami ma hawaye take yi Abba da Abbie suna tsaye cikin tashin hankali su Aida da arfah ma kuka suke, Abbie ne cikin dauriya yace "saudah ba kuka zakiyi ba plz ku daure ku mishi adu'a duk inda yake Allah ya bayyana mana shi"......

Cikin kuka Ammie tace "baban Aliyu dole inyi kuka Aliyu fa ba lafiya ba tabbas da Aliyu na lafiya baze ta'ba share wata biyar be kira ni ba, kuma kace kaje har office d'inshi an cema ba aiki aka tura su ba, ajiye aikin yayi da kanshi ya bar garin, gidanshi wata biyar kenan a kulle da manyan padlocks innalillahi wa'innailaihi raji'un"........

Ta karasa da wani kukan zaid da salma ne suka shigo cikin tashin hankali ganin yadda mutanen gidan suke kuka ne ya sasu tsayuwa turus daga bakin kofa da sauri ammie ta tashi ta isa gurinshi tace "yauwa zaid kuna waya da Aliyu?" Zaid cikin sanyi yace "a'a Ammie wata biyar kenan kullum se na kira shi wayan shi baya shiga na kira gurin aikinsu ma suka ce min ya ajiye aiki, na zata be da lafiya ne kuka boye min, ba shiri muka taso muna isowa nigeria ko gida ba muje ba muka wuce gidanshi muka ga a kulle shine muka biyo nan muga ko lafiya".......

Hannu ammie ta d'aura a kai tare da sa wani kukan tana cewa "shikenan kuma wani abun ya faru da shi Aliyu ba lafiya ba" zaid ma cikin tashin hankali ya kara da "tabbas da Aliyu na cikin hankali da natsuwar shi da baze kai tsawon wannan lokacin ba tare da ya nemi wani daga cikin mu ba".....

Salma data kara kyau tayi fresh da ita tace cikin natsuwa "toh kun gwada kiran iyayen matar shi kunji ko suna waya da 'yar su?" Abba yace "tabbas kin kawo shawara bari mu kira TY Abdulsamad d'in" kiranshi Abba yayi suka gaisa tukun ya tambaye shi suna waya da Aisha kuwa, daddy d'inta yace "eh kullum muna waya lafiya kuwa?"......

Yace "lafiya klau dan Allah turo mana number d'in da kuke wayan" daddyn yace "ohk" tare da kashe wayan ba'a fi minti biyu ba ya turo musu da numbern jikin Abba na rawa yayi dialing tare da sawa a speaker se da yayi mata two misscall tukun ta d'auka cikin isa da gadara tace "waye ne?"......

Zuhraa❤❤Onde histórias criam vida. Descubra agora