Page 44

3.9K 242 24
                                    

 Zuhraa❤❤
            (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
        ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 44

  A kano tayi landing ta kara hawa wani jirgin zuwa jos da dare ta isa gidan su rukks da ta gama school har ta fara aiki amma batayi aure ba tana shiga rukks ta taso da gudu ta rungume ta "I really miss you besty" murmushin yake kawai ta mata tace "rukks na shiga uku" d'ago ta rukks tayi tace "me ya faru?".........

Ayush tace "rukks Aliyu ya sake ni saki uku" zaro ido rukks tayi "what!!! Garin yaya, ya akayi kika yi sake haka?" Ayush tace "hmm mu karasa room dinki I want to fresh up" jan hannunta rukks tayi zuwa d'akin ta, ta kira maid d'inta ta had'a mata ruwan wanka ta fad'a toilet.......

Tana fitowa ta shirya cikin wando jeans da shirt ta kama attachment d'in kanta da bun abinci aka kawo mata ta zauna taci ta koshi tukun ta fuskanci rukks da tayi tagumi tare da kafa mata ido tace "ya su zee? Bari in had'a mna conference call".....

A take idon rukks ya cika da hawaye tace "baki ji labari ba?" Ayush cikin mamaki tace "lbrn me?" Rukks tace "hmmm zee da lubsy sunyi gasan shan cocaine wadda yayi ajalinsu" "what OMG!!!" hawaye Ayush ta fara tana tuna rayuwar da sukayi ba salati ba ambaton Allah kuma a idonta ba alamun nadama......

A hankali tace "Afrey fa?" Rukks tace "tunda muka gama school bamu sake waya da ita ba se bayan 1 year tace min ta gama service d'inta, iyayenta sun gane abunda takeyi sun mata horo me tsanani da ta zata baza tayi rai ba kuma suka aurar da ita ga cousin brother d'inta kuma ba a nija zasu zauna ba" girgiza kai Ayush tayi tace "yanzu shikenan fa komai ya zama tarihi"........

"Just share ya akayi Aliyu ya sake ki?" Ayush tace "hmm wlh ban sani ba kinji... Kinji... Kinji" ta bata labarin abunda ta gani ta kara da "ina tsoro Allah yasa ba wani d'an uwan shi ya gani ba, shiyasa nake son gobe muyi sammakon zuwa gurin na kan tudu" rukks tace "toh"........

Hira suka d'an ta'ba kafin kowa ya kwanta da asussuba sukayi wanka ba wadda ya damu da sallah suka kira driver ya ja su suka wuce, tun da suka fito garin ya had'e da hadari ko a jikinsu har suka isa kungurmin dajin a dai dai dutsun ya ajiye su, sun fara hawa dutsen kenan akayi wani irin tsawa da walkiya se kan dutsen a take bukkan boka na kan tudu ya bayyana ya fara ci da wani irin mahaukacin wuta dutsen ya fara jijjiga.......

Ihun shi suka fara ji har ya fito daga bukkan jikin shi na ci da wuta ihu yake ta kurmawa har ya kone kurmus suna kallon shi cikin tsoro wani tsawan aka kuma yi da ya sasu yin wani irin tumble suka gangara kasan dutsen suna kurma ihu wani walkiyan aka sake se gasu a gaban motansu kowa ya ji jiki, rukks se ihun idonta take yi da kafanta"..........

Da sauri drivern ya karasa ganin kaman dutsen ya fara aman wuta da sauri ya sasu a mota ya figi motan da gudu suka fice daga gurin dukkansu sun sume asibiti ya nufa da su da sauri likitoci suka kar'be su se emergency mom da dad d'inta driver ya kira a take suka bayyana cikin tashin hankali.......

Kusan two hours doctors suka fito cikin sanyin jiki yace su bi shi office d'inshi bayan sun zauna yake fad'a musu "am ya sunan patients d'in namu" momy tace d'ayar sunan ta rukayya d'ayar kuma Aisha" girgiza kai doctor yayi yace "ya zanyi na banbance su?" Momy tace "rukayyah ita ce baka Aisha kuma ita ce farar".....

Gyad'a kai doctorn yayi yace "sorry to say rukayyahn ta rasa idonta kafanta d'aya kuma ya samu matsala sossai yadda baze Kara aiki ba" ihu momy tasa tana kuka sossai tare da sambatu da kyar dady yasa ta tayi shiru cikin sanyi yace "Aishan fa?" Doctor yace "ita kam kariya ce kawai a kafa" gyad'a kai dady yayi tare da godiya wa doctorn suka fice momy na ta aikin kuka........

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now